← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 90

Sashe 58

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

........Kuka take sosai a gaban mijin nata da ayanzu al'amuransa ke bata tsoro matuƙa. Gaba ɗaya ya sauya mata, sauyawa irin wadda bata taɓa zato ko tsammani ba. Kai koda a mafarki ko lissafin rayuwa bata taɓa tunanin itada Sufiyanun nata zasu kasance a irin wannan ajin ba. Amma a yau sai gashi wai harda mata kishiya sa'ar jikokinta da wannan shekarun nata tsofai-tsofai. Kuma ko kunyarta baya ji yake soyayyarsa kamar wani ƙaramin yaro.
        Baba Garko da tunda ta shigo ta zauna bai ko ɗaga kai ya dubeta ba sai ma wayoyinsa da yake hankali kwance. Daya gama wannan zakaga wata ta shigo. Cikin jin gundura da kukan da take rera masa ya ce, “Amma dai kin san kina damuna ko? Please bana son damuwa idan kukanki zakiyi zaki iya bani waje”.
    Sake ɓarkewa tai da sabon kuka kamar wata ƙaramar yarinya. A dai-dai nan akai knocking ƙofar falon, ɗan jimmm yay yana kallon ƙofar kafin ya ce, “Ko waye ya shigo”. Mai aikin amaryarsa ce ta shigo a rikice, amma hakan bai hanata kaiwa tsugunne da ga bakin ƙofa ba ta gaisheshi cikin girmamawa sannan ta ɗora da faɗin, “Alhaji aunty amarya ce bata da lafiya, tun ɗazun kuma ta hana azo a sanar mak...” ai mai aikin ma bata ƙarasa rufe baki ba ya miƙe zaram ko nauyin tsufarsa baya ji. Ƙofar ya nufa a hanzarce, Dada da kanta ya nema tarwatsewa ta bisa da kallo galala, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki na sake turniƙe mata zuciya. Ba'a ko rufa minti huɗu ba sai gashi ya shigo a rikice, ko kallon inda take baiyi ba ya shige bedroom ɗinsa. Cikin ƴan sakanni ya sake fitowa ya fice hannunsa riƙe da key ɗin mota ya canja zuwa jallabiya. Kasa motsawa tayi a wajen har sai da taji ƴar hayaniya na tashi ta miƙe jikinta na rawar ɓacin rai ta leƙa ta window. Akan Baba garko da ke rungume da amaryarsa ita kuma tana faman yarfe hannu tana kuka idanunta suka fara sauka. A take zuciyarta ta ayyana mata haihuwa. Sake dugunzuma zuciyarta tayi har tana jin jiri na neman kwasarta, batama san sanda ta sulale a wajen ba ta zube saman kujera jaɓar wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, sai kuma ta ɓarke da kuka. Tunda take a rayuwarta, bata taɓa shiga matsanancin baƙin ciki da tashin hankali irin na wannan gaɓar ba. A tsahon rayuwar ƙuruciyarta ko firar kishiya bata so, kai ko ƙawa ko cikin ƴan uwa akaima wata kishiya daina zuwa gidan mutum take saboda yanda ta tsani kishiya. Amma a yau sai gata da ita a wannan shekarun nata, harma da ciki na haihuwa.....

       (🤣🤣🤣🤣🤣 Kar kuce dariyar mugunta nakema Dadaras😜)

         ____________★

     Tun Ummah na ɗaukar al'amarin ta ƙarami harta fahimci ya wuce da saninta. Kuka ma da hawaye yanzu ta kasa yinsa. Ƴan gidansu sunzo sai dai me suma ƙarewa sukai da fita da gudu harda masu faɗuwa. Wajen Abba suka koma kowa na maida numfashi, yayanta cikin damuwa ya ce, “Anya ba aljanune suka shigi Yahanasu ba Yaya Mika'il”.
    Cikin ɗan taɓe baki Abba yace, “Idan ma sune wajen biɗar baƙar tambayarta ta kwaso su. Ballema bana jin hakanne. Nafi ƙyautata zaton ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Ni yanzu jibirin ban san yanda zanyi da wannan matar ba. Gaba ɗaya ta firgitamin iyali sun kasa sakewa kowa sai zaman ɗaki”.
      Cikin damuwa Jibirin yace, “Amma yaya bai kamata kace haka ba. Ƙilama cikin matanka wata taimata haka kasan dai mata akan kishi”.
    “Wane matan nawa? A'a ƙarya haramun. Ai duk cikin iyalina babu fanɗararre irin Yaha. Nasan halin kowacce a cikinsu da abinda zata iya. Na jima ina zarginta dama da shigen-shigen nan kawai dai ban taɓa gani da idona bane shiyyasa ban kafa hujja ba. Amma a yanzu na gama fahimtar komai. Ko wannan halin da kaga tana cikin sihirin da taima Aliyu da matarsa ne ya dawo mata...”
           “Aliyu kuma Yaya? Aliyu Aliyu dai namu na nan?”.
       “Shi ɗin fa”.
   “Ikon ALLAH! To shi Aliyu dake matsayin ɗanta kuma zatama asiri. Miye ribarta kenan?”.
             “Oho mata, ita ta sani”.
        Sosai al'amarin ya girmi kan kowa. Cikin ƙarfin hali Zaidu ya bada shawaran to ko za'a samo malamai suyi addu'a ne. Dan wannan yanayin nata abin tashin hankali ne ga kowa tunda gashi hankalin kowa a tashe, shi wlhy yanzu haka baya jin yau ɗin nan zai iya barci lafiya saboda ganin wannan mummunar halitta da Ummah ta koma. Abba dai yace shi babu ko sisinsa a nema mata lafiya. Hasalima ya kirasu ne su wuce da ita dan bazai iya ba. Hankalinsu ya tashi matuƙa, dan sukam bazasu jajibi wannan halittar ba sukai cikin iyalinsu suna zaune ƙalau. Dan haka suka dage bashi haƙuri da roƙo da magiyar ya barta a ɗakinta cikin ƴaƴanta harta samu lafiya sai aji dalilinta na wannan mummunan al'amari, idan ma matakin sai ɗauka sai ya ɗauka. Anfi ƙarfin Abba ne kawai, dan haka yay shiru. Su suka fita suka zo da malamai, da ga tsakar gida suka tsaya aka kwala mata kira ta fito. Su kansu malaman sai da suka zabura da ganin mummunar halittar dake tunkarasu, ganin tana yo kansu gadan-gadan sukaji fa dauriya ba tasu bace. Ai tuni suka dafe kawuna kowa ya ara cikin ta kare yana jan kula'uzai. Bayan su an sake kawo wasu malaman amma fa kowa yazo yana tozali da Umma sai dai a tsincesa waje ya dafe ƙeya. Al'amari kamar wasa sai ƙara faɗi yake. Dan takai ƴan jarida daga gidajen rediyo har sun fara zuwa neman labari. Sai dai suma fa suna shigowa sukai ido huɗu da Umma labarin bai ɗaukuwa garesu sai ƴar reren gudu...
      Tsabar tashin hankali da hawan jini Umma ta koma ko gani batayi da ƙyau. Barci kuwa ya ƙauracema idanunta gaba ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai wata irin muguwar rama mai ban tsoro. Babu abinda ke ɗaga mata hankali sai ganin ƴaƴanta suma gudunta suke da mijinta da ta ɓata tsahon shekarun rayuwarta tana faɗa da faɗi tashi a kansa. tana son jin halin da Hajiya Naqiba take amma babu hali. Rayuwa ta mata duhu, duhu irin wanda ko tafin hannunka baka iya gani, duhu irin wanda zuciya kanta bata iya tuna komai sai ƙunci da ciwo mai raɗaɗi. Hatta salla yinta kawai take amma bata ma sanin mitake yi a cikinta. wanka kam bama'a maganarsa dan tashin hankali. abinci dama yanzu ƙofar ɗaki Abba ke zuwa ya ajiye mata saboda kowa tsoro yake ji, shi kansa dai tausayin rai ne ke sakashi yin ƙarfin halin ajiyewar kawai dan an hanata fitowa.....

        *_★UK★_*
Chapter 58 · 0% Book details