← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_Alhamdullah barkanmu da sake dawowa a book 2. Yanda muka fara a Sa'a ALLAH yasa mu kammala da nasarori. Ina godiya da jirana da kukayi tare da fatan alkairi 😘😘👏._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣

........Iyayensa ya kalla cikin nutsuwar data ratsashi a yanzu najin tabbacin ina matar tasa yake, cike da girmamawa ya ce, “Abba ku tashi muje gida kawai”. Abba da tausayin ɗan nasa ya ƙara mamaye masa zuciya ya ce, “Aliy ba tafiya gida ne masalaha ba, ka bari dai a sasanta muji miye dalilin aikata hakan”. “Abba bata da wani dalili face na son zuciya. Ina son cigaba da ganin girmanta a matsayinta na uwa kamar yanda kuka tarbiyantar dani girmama kowace irin furfura, tun farko ma ita ya kamata na zarga, amma banyi hakan ba saboda shi zargi bashi da amfani. Sai dai amsa ɗaya zan bada a yanzu har gaban Abada *_BAZAN SAKI MAWADDAT BA_*. Sai dai ayi ɗayan biyu. Ko na MUTU tamun TAKABA, ko ni na mata wanka na sallaceta zuwa kabarinta. Wannan dalilan guda biyu ne kawai zasu iya raba wannan auren da izinin ALLAH!!”. Ba su Dada ba hatta Abbah da Ammah sai da Smart ya girgizasu, dan magana yake a dake, a fusace, a kuma kausashe, hatta da Ahmad dake a matsayin aboki zai iya rantsewa bai taɓa sanin Smart ɗin yanada irin wannan zafin ba. Harara Dada ta watsa masa da faɗin, “Oh burinka kenan dama ta mutu kaci gadon dukiya. Sheɗani to ALLAH ya fika, sakin Mawaddat kuwa idan bakai ta arziƙi ba zakayi ta wuya dan bazamu taɓa haɗa zuria da jinin tsiya jinin talauci ba. dama koda ka aureta ai asiri kai ma iyayen nata matsiyaci”. Murmushi Smart ya saki da taɓe bakinsa cikin halin ko'in kula da zancen Dada. Sai ma ƙoƙarin barin falon da yake yi batare da ya bata amsa ba . Alh. Sulaiman da ya kai maƙura a kan Smart ɗinne ya miƙe a fusace yana nunashi da yatsa. Sai dai kafin ma yace wani abu Smart ya nunashi shima cikin gargaɗi, “Kai! Karka kuskura shiga ramin da zai bizne rayuwarka ta har abada ya barka da gangar jiki kawai da idanun kallo. Sunanka ƙanin uwa ne ba uba ko ƙanin uba ba. Ni da kake gani na nan Sulaiman na fika fiye da abinda ka iya wlhy. Idan kace zaka saka ƙafar wasa da ni sai na gigita rayuwarka ta yanda kai a karan kanka bazaka taɓa morarta ba balle waninka. Magana ake ta mutane ba irinku riɓɓaɓu ba okay...” da ga haka Smart ya sa kai yay ficewarsa kafin ma Alh. Sulaiman da jikinsa ke rawar ɓacin rai dana firgita ya iya furta komai, da gaskiyar Lulu idanun Smart sun cancanci kowane irin suna, musamman a yau da ransa ke a ɓace dan Alh Sulaiman idanun Smart na ɗaya da ga cikin abinda ya razana shi. Fitar Smart ɗin ta saka falon zama tsit, yayinda Alh. Sulaiman ke nuna ƙofa cikin rawar baki data hannu. Daddy ya sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya a karo na farko, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, dan tunda Smart ya fara magana yake kallonsa harya fice. Uncle Yousuf ne ya tashi yabi bayan Smart, haka ma Ammah da Abbah. A gate suka sami Smart yana waya da Coach, dan a gobe ya kamata ya wuce dama, sai dai da yayi aniyar haƙura dan bazai iya tafiya wata ƙasa batare da anga Lulu ba. Amma a yanzu ya gama yanke shawarar wucewa babu fashi. Uncle Yousuf da ke kallonsa da murmushi yay masa nuni ya shiga mota inda Abba da Ammah suke, bai musa ba ya shiga. Har gida Uncle Yousuf ya kaisu, inda ya samu zama na musamman da Abba da Ammah. Shi ya lallashesu akan su kwantar da hankalinsu dan ALLAH a zubama su Dada ido aga gudun ruwansu, dan ya tabbatar sun aikata haka ne dan Alhaji Garko baya nan. Sosai Abbah ya gamsu da bayanin Uncle Yousuf ɗari bisa ɗari tare da ganin shawarar itace dai-dai. Bayan wucewar Uncle Yousuf Abba da Ammah suka sake zaunar da Smart sukai masa nasihar ya cigaba da shirinsa na tafiya kawai kamar yanda Uncle Yousuf ya faɗa da masa faɗan abinda yay ma Alh. Sulaiman da Dada. Haƙuri ya basu da alƙawarin bazai sake ba. Wannan shine sanadin tattara al'amarin Lulu ya haɗa kayansa a washe gari shi da Uncle Yousuf da Coach suka nufo ƙasar UK a London. Inda yay signing da wani ƙaramin team Queen City. Su Uncle Yousuf sun sake masa nasiha akan ya kwantar da hankalinsa kan al'amarin da kanta zata bijirema su Dada. Shi dai cikin dauriya da dakiya yake amsa musu da to kawai. Amma a cikin ransa shi kaɗai yasan irin ƙunar da yake ji da matuƙar kewar matarsa. Sai dai ƴan mazan sun ɗauki aniyar da jarumtar a wannan karon na sai ya tabbatar ma family ɗin Lulu gaba ɗaya da ita kanta shi ɗan halak ne, sannan talauci ba hauka bane ba. Duk da dai yanayin yaso taɓa shi da son maidashi sanyi-sanyi a watanni ukun daya samu kansa, sannan sam yanzu baka ganin fara'a a fuskar Smart, ya sake zama shiru-shiru a yanzu ma harda miskilanci zamu iya cewa ya ƙaro. Dan bai shiga sabgar kowa, abinda ya kawosa kawai yake yi sai bautar ALLAH. Baya zuwa ko ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al'amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta....)

Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England.

Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci....

     Wannan kenan.

____________________★

       *_CANADA_*
Chapter 2 · 0% Book details