← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 90

Sashe 5

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al'amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za'ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.
      Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma'anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba'a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba'a gadon asibiti ba”.
        “Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.
            “Ka shirya ganinta yanzu kenan?”.
        Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma'il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana ɗaukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana ɗiyar ƙanwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai ALLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani ɗin, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma'il ina maka gargaɗi na ƙarshe, ka bani camara ɗin nan, ka kuma saka a ranka baka taɓa sanina ba har abada, in ba hakaba, a wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family ɗinka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka zaɓi ya rage naka....”
       Murmushi Daddy yay mai ma'anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman ɗin ya faɗa zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma'il ɗin wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta ɗauka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka ɗauki yarinyar ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta ɗauka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na ɗan ɗana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta ɗanɗana min a tsahon shekara ɗaya dana rayu da ita.....”
        “Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya faɗa a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Isma'il kenan a tunaninka kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon waɗan nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka ɗauke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwarta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma'il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”.
        Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe.........✍️

Tofa fagen na manya ne yau🚴🚴🚴

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣

........Kwanan Dada goma sha ɗaya ta fara shirin komawa wajen mijinta. Lulu ko ta maƙale tace ƙafarta ƙafarta dan bazata sake zama ita kaɗai anan Canada ba ciwo ya halakata. Cikin lallashi Dada ta nuna mata bazai yiwu ba, ta kwantar da hankalinta ai Tajuddeen na dawowa nan ɗin duk da ba'a gidan zai zauna ba. Tsaf ta tubure cewar ai ita ko ƙasa ɗaya ma bazata zauna da shi ba. Tunfa Dada na lallashinta harta birkice mata da masifa cikin ɓacin rai. Amma hakan baisa Lulu ta yarda zata cigaba da zama a Canada ba. Sai ma cewa tai ita gida Nigeria zata koma to. Tofa babbar magana, hankalin Dada ya tashi, dan tasan taurin kai irin na Lulu sarai. Alh. Sulaiman tai kira ta sanar masa. Washe gari sai gashi ya sake dawowa Canadan. Shima balbale Lulu yay da bala'i tare da zageta tas ita da Daddy sannan ya saka Dada tattaro masa passport ɗin Lulun da komai da zai iya taimaka mata fita a ƙasar ya wuce da su harda na Ummita ma. Wannan abu ya tada hankalin Lulu, hakama Dada sai al'amarin ɗan nata ya fara bata mamaki kuma. Dan sai take ganin ya zafafa da yawa, miye na ɗauke passport kamar wasu masu son kidnapping yarinya?. Amma ta kasa iya masa magana dan harga ALLAH tana shakkar ɗan nata kasancewarsa ba kanwar lasa bane ba.

      *_NIGERIA_*

    Alh. Sulaiman ya koma Nigeria bisa matsawar Tajuddeen dole yakai kotu akan alƙali ya saki Lulu, amma sai ya bashi amsa da cewar sai ma'aurata duka sun gurfana a gabansa zai iya aikata hakan. Zancen ya matuƙar bashi haushi ya yayyaɓama alƙalin magana duk da kuwa suna mutunci. Shiko yay biris da shi dan yace bazai aikata abinda ya saɓaba, taya zai kama kashe aure ma babu masu alaƙa da auren kamar a garin da babu shari'a, to yace yamawa hukunci kenan. Kusan alƙalai biyu ya sake tunkara bayan na farko amma amsar duk iri ɗaya ce suma since sai ma'auratan sunzo, dan koda aka aika sammaci gidan su Smart sai akace ma nai kai takardar ai Smart bama ya ƙasar, bakuma asan randa zai dawo ba ma. Alƙalin ƙarshe ne ya bukaci ganin iyayen Smart. Koda Abba yaje sai ya nunama Alh. Sulaiman yafisa sanin takan duniya, dan cayayma alƙali ai yaron da matarsa suna tare acan turai, shi Alh. Sulaiman shirmensa kawai yake yi, yasa a kira masa Smart a waya, akayi kuwa sa'ar samunsa, sun tattauna sosai da alƙalin akayi sa'a kuma shima Smart ɗin yace yana tare da matarsa Alh. Sulaiman yana shirmensa ne kawai saboda yana son raba auren dan taƙi ɗansa. Alƙali kuwa ya samu Alh. Sulaiman yay masa tas tare da gagaɗin yabar wannan shirmen da zubda mutunci yara su rayu da juna tunda sunce suna tare, ɗanshi kuma yaje ya nema wata. Wannan makirci ya matuƙar ƙona masa zuciya, dan haka ya ƙullaci Abba a ransa da fara shiri na musamman....
Chapter 5 · 0% Book details