Sashe 72
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana zaune a bakin gado yana goge jikinsa da ƙaramin towel ta fito itama sanye cikin bathrobe. Idanu ya zuba mata cike da jin ƙarin ƙaunarta da tausayi, suna haɗa ido ta ɗauke nata cikin jin nauyi. Wucesa tai niyyar yi ya riƙo mata hannu. Batare data juyo ba ta furta, “Zan shirya ne fa na haɗa maka abinci”. Murmushi yayi da jawota baya ya zaunar a saman jikinsa. Cikin kunneta ya raɗa mata maganar da ta sakata jin rikicewa dan kunya, shiko ya shiga darawa abinsa. Tashi tai zumbur a jikinsa ta gudu zuwa gaban mirror tana murmushi da faɗin, “Ni dai babu ruwana wlhy”.
“Daga baya kenan yarinya”. Ya bata amsa yana tasowa zuwa gaban mirror ɗin shima. Da jikin mirror ɗin ya jingina, hakan ya basu damar facing juna. “Miya sakaki kuka?” ya jeho mata tambaya dai-dai tana ƙoƙarin warware gashinta data naɗe a cikin ƙaramin towel. Numfashi ta ɗan firzar a hankali idanun nata na sake cikowa da hawaye, murya a raunane ta ce, “Nadiya ce”.
“Nadiya kuma? Who is she?”.
“Ƙawata ce, sai dai bama tare yanzun”.
“Ya akai banji sunanta a labarinki ba?”.
“A Nigeria na santa ai, kaima kuma ka santa ma. Dan ka taɓa kai ni shagonta saloon”.
Cikin ɗan yin jimm na alamar tunani ya ce, “Okay na gane, ba itace kikace zata taimakemu ba?”.
“Yes ita”.
“Uhmum miya faru da ita?”.
Wayarta ta ɗauka ta miƙa masa. Amsa yay ya duba. Recording ne na video call da sukayi ita da Nadiya. Shi kansa da farko bai ganeta ba. Al'amarin ya girgiza shi da bashi tsoro. Jiki a sanyaye ya miƙa mata wayar batare da ya iya furta komai ba. A bazata Lulu data sake fashewa da kuka ta ce, “Aliyu nagode da ƙoƙarin ka a kaina, bani da abinda zan iya biyanka da shi a duniyar nan face na dawwama ina maka addu'a har ƙarshen numfashi na kai da Uncle Yousuf. Yanzu nima da ALLAH bai taimakeni, kun tallafi rayuwata kun cireni da ga wannan mummunar ƙazamar rayuwar ba da hakance zata kasance da ni. Abinda nake sha ko rabinsa Nadiya bata iya sha fa. Amma kaga yanda rayuwarta ta koma, bata da maraba da mahaukatan kan layi masu wucewa yara na musu atire. Iyayenta sun korota a makaranta data lalace take kwana tsakkiyar kazaman ƴan shaye-shaye. Na shiga uku Hydar wace irin rayuwa ce muke jefa kammu ne haka?....”
Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yanda take kuka na fitar hayyaci. Ɗagota yay ya rungumeta a jikinsa, tare da fara jera mata kalaman lallashi da nasiha. Sun jima a wajen tsaye ya karasa busar mata da kan nata ya ɗaure mata shi. Cikin son kauda mata yanayin ɓacin ran nata ya ce, “Ina auntyn taki wai, naga da Iya Tabawa kawai muka gaisa tana goye da AA”.
Murmushi ta ɗan saki kaɗan, sai kuma ta kallesa tana ɗan lullumshe ido cike da salon dake narkar da mutumin nata tace, “Tana asibiti ai, tun randa suka zo”.
Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce, “Asibiti kuma Madam”.
Sai da ta ɗan hararesa saboda kiranta Madam sannan ta bashi amsa. “Eh ai abinda ya kamata ayi kenan, mizai sa na riƙeta a gida har sai ka dawo kuma. Yanzu kam kaga har sun bamu ranar da zasu mata aikin ma. Sai ka ƙarasa shiryawa muje ka ganta dama Doctor ɗin ta buƙaci ganin mijinta, sai dai nace mata baya kusa sai ƙaninta dai.”
Rasama mizaice mata yayi shi kam, sai kawai ya zuba mata idanu yana kallonta, yana jin tamkar ya haɗiyeta ya huta ma kawai. “Kallon fa?”. Ta faɗa tana wani tura masa baki da kashe masa ido ɗaya. Hannu ya kai zai cafkota ta zille tana dariya. Shima sai ya murmusa yana dimtse gefen lip ɗinsa da haƙori. Kayanta ta maida dan bata son Iya Tabawa ta zargi komai tunda ta ganta da su. Ta dawo gaban mirror ɗin ta maida ɗaurin ɗan kwalinta kamar yanda yake ɗazun da yin ƴar kwalliya.
Shima sai ya nufi closed ɗinsa ya saka kaya. Tsaff suka fito suna zuba ƙamshi da annuri, ita sai yanzu ma ta san ashe tare yake da Ahmad. Amma yake komansa hankali kwance a ciki kamar bai bar kowa na jiransa ba, shiyyasa da zata fito ya sakata sanya abaya ashe. Sun gaisa da Ahmad yana faman tsokanarta kamar yanda ya saba. Ita dai nata murmushi ne musamman daya kasance boss ɗin nata ya watso mata kallon gargaɗi. Abincin da suka sha wahalar yi ita da Iya Tabawa ta gabatar musu. Sosai Smart yaji daɗin ganin tuwo, dan zai iya cewa tunda ya baro Nigeria bai sake ci ba. Kasa haƙuri yayi ya tambayi inda suka samo garin tuwo haka. Lulu ta bashi amsa da cewar su Aunty Bilkisu ne sukazo musu da shi. Bayan sunci sun ƙoshi kaɗan suka huta Lulu ta takura musu dole suka fice zuwa asibiti duba aunty Bilkisu, zuwa lokacin AA ya tashi yana hannun Babansa da yay kewa.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣3️⃣
.......“Banda abinka Sulaiman Garko idan kaji makaho yace ai wasan jifa ai ya taka dutse ne. Toni a wannan gaɓar dutsina na taka bama dutse ɗaya ba. Sorry fa, inata son zuwa na maka jajen abubuwan dake ta faruwa amma nayi busy da yawa. Sai kuma naji yau ma wata yarinya ta ɓaro muku babban aiki, dan kaima banace bakayi ba. Wanda zai iya yima ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya fyaɗe ai abune mai sauƙi yayma sauran ƴaƴan jama'a ciki harda wanda ya haifa ma.....”
“Da hannunka kenan a ciki? Dama an tabbatar min da yarinyar ƙawar ƴarka ce ai. Isma'il karka manta ni zaki ne. Nakanyi farauta a duk dajin da yay min na kuma ci kowacce irin dabba na zauna lafiya batare da ko jin ɗar ba tattare da ni....”
“Banda Giwa, dan koda ka kadata namanta bai ciyuwa gareka sai da taron dangi Sulaiman Garko. Tabbas Nadiya ƙawar Mawaddat ce bakayi ƙarya ba, idan kuma kace zaka nuna wani giggiwa a wannan kadamin karan bana ne zai yi maganin zomon bana. Dan ka tabbatar da Mawaddat ce ta haifi Mawaddat, kasan kuwa tunanin zai iya zama duk iri ɗaya, hakama jarumtar. Ballema a yanzu da take a jingine a jikin matashin *_ZAKI_* na haƙiƙa ba arar suna ba irin ka. Gefenta ga *_DAMISA_* ƙi sabo. Sannan ga addu'ata biye gareta a dukkan motsinta. Ai nasha faɗa maka ni da ƴata da zuri'arta gaba ɗaya *_FURAR DANƘO_* muke, *_A SHEKARA ANA DAMU BAMU FARAU-FARAU_*. Idan kai acan ka wuni, ni kwana nayi. Maza ka sake shiri *_MAZAN_* ƙwarai da *_MACE_* mai kamar maza ne tafe bisa kanka ƙaramin biri......”
“Isma'illll!!!!!!”
Alh Sulaiman ya kira sunan Daddy cikin wata irin Mummunar tsawa mai razani. Kafin Daddy ya ce komai ya ɗora da faɗin, “Amma dai kasan zan iya karar da duk jama'ar asalin ƙauyen da ka fito bama kai kawai ba ko??!!!”.
Dariya Daddy ya ƙyalƙyale da shi tare da faɗin, “Ai ga fili ga mai doki nan Sulaiman Garko, zaka iya gwadawa idan har zaka iya, dan wlhy ba jama'ar garin jiƙamshi ba, koda ƙasar jiƙamshi ka taka da manufa saina karya ƙafafunka ta yanda bazasu ƙara ɗaukar gangar jikinka ba har gaban abada. Amma kafin ka tafi jiƙamshin ƙarar dadu ka tabbatar ka fara duba saƙo ga shi nan zai zo a hannun matarka shashasha ƙaramin biri abin wasan yara a tsakkiyar kasuwa”. Ya yanke wayarsa.
Haukacewa ne kawai Alh. Sulaiman baiyi ba da kalaman Daddy masu ƙona zuciya. A wani irin birkice ya ɗaga wayar ya naka a ƙasan tiles. Dai-dai nan amaryarsa ta shigo hannunta ɗauke da leda. A ɗan tsorace da ganin yanayin nashi ta ajiye ledar tana faɗin, “Saƙone aka kawo a baka, yanzu maigadi ya kaw....”
Yanda ya juyi a fusace ya hanata ƙarasawa. Har ya juya shima da nufin baida lokacinta sai kuma ya juyo tare da wani irin fisgar ledar. Zazzageta ya shigayi cikin tsumar jiki. Babu komai a ciki face Flash drive. Cikin rawar jiki data ruhi ya kai zaune daɓar yana mai janyo laptop ɗinsa ya saka flash ɗin jiki. Gaba ɗaya ya manta da kasancewar matarsa a wajen yay playing video ɗin da ke cikin Flash ɗin. Ba komai bane face fuskar mahaifiyar Lulu tana kuka da faɗin wannan shine kundin manyan laifuka na shi a ciki. Tana roƙon ko bayan babu ranta iyayensu su sani shine yayma Sultana fyaɗe....”
Ai bai ma kai ƙarshen video ɗin ba ya buga wata irin kuwwa da hankaɗa Laptop ɗin ƙasa itama ta kifu. Amaryasa data gama jin komai cikin firgita ta buga ihu itama tana neman hanyar fita a guje. Cikin tashin hankali yay tsalle ɗaya ya taɗota ta zube ƙasa. Idanunsa a rufe ya kai mata wata irin wariyar shaƙa. Tuni idanunta suka juye ta fara ƙaƙarin mutuwa.
“Mi kika ji?!! Na ce, “Mikika ji!!? Dan uban uwarki”.
Kanta take jujjuyawa alamar bataji komai ba. Wawan mari ya ɗauke fuskarta da shi ta bayan hannu da sake maƙureta. “Idan ma kinji ko kin gani wlhy wlhy wlhy ki zama kurma. Idan ba haka ba da hannuna zan kashe ki, na gina rami a tsakkiyar falon nan na bizneki. Kuma har abada babu mai sake jin labarinki ko tambayata ina kike. Baƙar mayya mai leƙe-leƙen masifaa!!”. Ya ƙare maganar da yarfar da ita ƙasa. Ya wuce bedroom ɗinsa a birkice. Babu jimawa sai gashi ya fito. Har lokacin tana kwance a wajen yabi takanta ya fice abinsa. Umarni ya bama maigadi akan kada wanda ya fita a gidan. Daga haka ya birka motarsa da kansa yau ya fice a bala'in guje....
*_★UK★_*