← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 90

Sashe 31

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

........“ALLAHU akbar, ALLAH mai rahama mai jin kai, Sarki gagara misalin masu misalai. Isashe mai iko da koman da ke iya kallon kansa a iko. Dama anga ɗiyar tawa?”.
         Kai Uncle Yousuf ya jinjina mata, da ga ita har Abbah da farin ciki ya sashi jin yama kasa motsawa, sai sunayen ALLAH yake ambata a jajjere. Cikin nutsuwa Uncle Yousuf ya zayyane musu komai ta yanda zasu fahimta. Wato gano inda Lulu take dama abinda ya faru akan cikin har zuwa haihuwarsa a yanzu. Sai dai suna roƙonsu da su ɓoye wannan sirrin dan basa son asan inda Lulu take a yanzu har sai abubuwa sun dai-daita domin koyama Alh. Sulaiman da Dada hankali bisa kuskurensu. Da ga ƙarshe suka sanar musu sunan yaro Aliyu kamar yanda Lulun ta saka aka masa huɗuba da shi. Sosai su Ammah sun gamsu da wannan dabara, tare da mamakin wannan baƙin hali na su Dada. Ga kuma Umma a gefe itama tana nata yaƙin, duk da dai Ammah ce kaɗai tasan da wannan. Yaro yasha addu'oi shi da mahaifiyarsa Lulu na fatan samun lafiya a gareta. Da ga ƙarshe Daddy yace musu su shirya domin sama musu visa dan yana son suje su gano Jariri. Da farko Abbah yaso ƙi, acewarsa bazasu sakasu wahala ba. Duk randa suka dawo Nigeria ai zasu ganshi. Amma sai Daddy da Uncle Yousuf sukaita roƙonshi. Da ƙyar dai ya yarda ya amince. Inda tun a ranar suka fita da su domin yin passport. Abinka da harkar kuɗi, an gama musu duk abinda ya dace cikin ƙanƙanin lokaci saura jiran result kawai.
     Kowa ya kalla Abba da Ammah a wannan yinin yasan suna cikin farin ciki mai tsanani, sai dai ba'a san kona minene ba. Dan hatta su aunty Bilkisu Ammah bata sanarmawa ba sai Gwaggo Sa'adah kawai saboda ita ɗin sirrinta ce, ai ko sai ga Gwaggo Sa'adah itama da hawayen farin ciki, da yammacin nan bata iya haƙuri ba sai da tazo gidan taga hoton jariri. Ita Umma dama bata gidan, tana can wajan biɗar baƙar tambayarta. Bata dawo gidan ba sai yamma lis. Sannan su Abba har sun dawo da ga fitar da sukai. Amma sai Mama ta sameta har ɗaki da gulmar wai yau surukan Smart sunzo gidan, kuma sun fita da su Ammah tana ganinfa akwai matsala. Sai dai kuma su Ammah tunda suka dawo sai faman washe haƙora sukeyi da ga ita har Abba. Dan Ammah harda su sadaka tayima yaran anguwa da maraicen nan. Sosai wannan magana ta tsayama Umma a rai, dan sabon malaminta da sukaje wajensa a yau ɗin nan dama ya sanar musu akwai wani babban al'amarin farin ciki da ya samu Smart ɗin, sai dai ya gagara gane ko minene anata nuna masa haske kawai babu komai. Amma taje gida duk abinda taji gobe ta dawo. Sai kuma gashi da ga dawowar tata taji sabon zance a wajen Mama macijin sari kanoƙe. Cikin matsanancin tashin hankali tai kiran Hajiya Naqiba suka tattauna, sai dai duk iya hasashensu sun kasa canko komai ilai tunanin ko Lulu zata dawo ne. Amma dai sun tsaida matsaya Umma taje ta zunguri Abbah akan batun. Wannan shawarar ta rika, dan haka a daren dan ta kasa nutsuwa ta nufi ɗakin Abba da nufin su gaisa tunda yau bata yini a gida ba. Lokacin Ammah ta baro ɗakin da kwanikan da yaci abincin dare. Zaman dirshen Umma tai suna hira da Abba bayan sun gama gaisawa, inda cikin salon makirci ta fara zungurarsa da batun Smart duk da bata fito fili ta ambaci sunansa ba. Dai-dai nan ALLAH ya kawo Ammah, tsaf ta fahimci manufar Umman, dan haka ta zauna a falon dan tasan halin maza wani lokacin sai addu'a musamman idan suka haɗu da makirar bace. Zuwan Ammah baima Ummah daɗi ba sam, dan tasan halin Ammah da shegen tsartar tsiya. Dan haka ta tashi ta fice cikin jin takaici tana ƙwafa. Da kallo kawai Ammah ta bita tana girgiza kai, inda bayan sunbar falon zuwa makwanci cikin hikima ta sake nusar da Abba muhimmancin ɓoye al'amarin haihuwar nan kamar yanda su Daddy suka roƙa, Abba ya fahimceta sosai, sannan bai zargi tayi hakane saboda Umma ba dan Ammah mace ce mai hikima da dattako. Kawai dai dan ba fitinanniya bace da lallai su Ummah sun kaɗe a gidan nan.....

         *_UK LONDON_*

   Sosai yake cikin farin ciki mara misali, yaso yay amfani da ɗan hutun da suka samu yazo gida Nigeria sai dai hakan na neman gagara saboda kara kainar da manyan clubs keyi akan al'amarin sa. Duk da dai abin bai fito fili duniya ta fahimta ba Coach ɗin sa shi da komai ke a garesa da Manager ɗin sa Uncle Yousuf suka ce ya dakata dai aga inda wasan zai tsaya. Wannan shine dalilinsa na haƙura da zuwa gida Nigeria ya cigaba da bama kansa hutu a gidansa. Sai motsa jiki da yakan fita da ɗan yawata gari idan yaso a wasu lokutan.
Chapter 31 · 0% Book details