Sashe 68
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana kwana na biyar da kama Alhaji Sadi Dikko Aunty Bilkisu da Iya tabawa suka iso Unitet Kingdom tare da Ahmad. A ranar Smart baya gida sunje buga wasa. Sai Lulu ce taje tarbarsu duk da Ahmad yasan gidan. Sosai aunty Bilkisu da duk take a tsorace ta samu nutsuwa da ganin Lulu, cikin farin ciki suka rungume juna. Hakama Iya Tabawa yau Lulu harda rungumeta, yayinda Ahmad ya caɓe yaronsa a hannu shima. Cab suka shiga har gida, dan Lulu bata driving anan kasancewar bata da lasisi. Sai Smart kawai. Daga Aunty Bilkisu har Iya Tabawa gidan ya birgesu sosai. Sunata santi da jera addu'a ga Smart. Abincin da Lulu ta shirya musu sukaci, bayan sunyi nak Ahmad yace zai wuce can ya samu Smart. Zuwa gobe sa dawo tare ɗan ba'a ranar Smart ɗin zai dawo ba. Tafiyar Ahamd ta sake basu damar ɓararrejewa, dan ma Aunty Bilkisu ba daɗin jikinta take ji ba sai ƙarfin hali kawai. Sun ɗan taɓa hira kafin Lulu ta kwashesu zuwa asibiti dan a yau take son aunty Bilkisu ma ta fara ganin likita. Kuma ko Smart baisan da hakan ba, dan shi nashi shirin kawai sai ya dawo ya kaita da kansa.
Kasancewar Usman da Dr Lameer ne suka haɗasu da likitan basu wani sha wahala ba na ganinta. A take aka bama aunty Bilkisu gado. Abinka da inda aka san darajar ɗan adam babu ɓata lokaci suka fara mata gwaje-gwaje da duk abinda ya dace. Koda Smart yay kiran Lulu bayan sun tashi a wasan bata sanar masa suna asibiti ba. Sun dai gaisa tai masa congratulations dan ganin sunci wasan suka ɗanyi hirarsu ta soyayya sukai sallama. Da yace ta haɗashi da su yay musu barka da zuwa Iya Tabawa kawai taba tace aunty Bilkisu na barci. Bai kawo komai a ransa ba ya yarda. Sallama sukai fan yana tare da Ahamd daya sameshi a can. Da ga haka itama ta cigaba da kai kawonta tare da Dr Lameer dake taimaka mata. Kasancewar mai jiyya ba zama yake a asibitin bayan ayi mata abubuwan da duk suka dace na wannan lokacin suka dawo gida, sai bayan wasu awoyi zasu koma dubata kuma......
*_★9ja★_*
A gidan Baba Garko suna akaci na kece raini da nunawa tsara. Dan ƴan biyu kam sunyi goshi matuƙa sannan sunzo da farin jini a wajen dangi. Kai da kaga taron nan kasan da gayya akayisa. Kasancewar su kansu dangin Baba Garkon ba daɗin Dada sukeji ba yasa a wannan gaɓar suke maida murtanin bashin gaba. Dan raƙashewa akai iya raƙashewa. Ga matan ƴaƴansa da jikoki cike taf da gida. Su kansu ƴaƴan dole sukazo kowa kuma da tsarabar suna. In ba haka ba kaci ubanka hannun mai gayya mai aiki. Alh. Sulaiman ne kawai babu, amma iyalinsa duk sun zo a sace batare da ya sani ba. Dan sukam dai basu yarda sun saka kansu a cikin faɗan iyaye da ɗansu ba. Hajiya Turai kuma tsaye take akan ƴaƴanta bata basu fuskar da zasu guji kakanin nasu ba. Tace babu ruwanta suma babu ruwansu. Ko Tajuddeen dake a cikin case ɗin tsundum cikin hikima ta dawo dashi ga kakaninsa tsundum. Dan tasan abinda take yi.
A yanda Dada ta koma laƙwas sai ta baka dariya ma da tausayi. Ba komai ya jawo hakan ba kuma sai kufcewar duk wata power nata. Gaba ɗaya ta fahimci komai fa ya gudu. Dan hatta matan ƴaƴan nata da take bama gwale-gwale yanzu kar suke kallonta. Bama sa shakkar dubar tsakkiyar idonta su yaɓa mata habaici a kaikaice. Karo na farko a rayuwarta datai kuka mai yawan gaske a dalilin tuna mahaifiyar Lulu. Tasha gaya mata gaskiya akan ta rage tsananin da takema matan ƴaƴan nata, in ba hakaba watarana sai sun nuna mata sun fita iyawa. Hakama dangin babansu ta daina musu wulaƙanci musamman marasa shi ɗin nan, kada wataran a auro wata a gidan ta riƙesu su rama duk cin kashin da take musu. Amma akoda yaushe saita hantareta harma da zagi saboda takaici da baƙin cikin ta kira mata kishiya, takance badan tana kama da Baba Garko ba itako da tace an mata misayarta a asibiti ne. Iya ƙoƙari Mawaddat tayi a kanta wajen gaya mata gaskiya akan abubuwa da yawa, yau gashi bata kusa da ita balle taji mata ciwon abinda ke faruwa. Dan ta kula ƴaƴa mazan nan fa ƴaƴansu da matansu kawai suka sani, tunda gashi kowa gani yake ta tsananta da kishin amaryar ubansu, ko kunyar faɗa mata hakan basa ji. Ko yau da safe Uncle Khamil da yazo sunan shi da nasa iyalin takanas da ga Abuja sai da yay mata irin wannan ƙorafin. Hakama autanta daya aiko da shatara ta arziƙi tun daga Saudiya. Gaba ɗaya saita fahimci goyon bayan mahaifinsu suke sam bata sonta ita yanzu. Babu abinda yafi ƙona mata rai da zuciya sama da saƙon Lulu, ita sai yanzu ma take sanin wai Lulu bata Nigeria tabi mijinta, bama wannan ba, shi kansa Smart ɗin bata san ya zama wani abu ba sai yanzu.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣8️⃣
.......“In dai muna son kama mutumin nan ya zama mai ƙarfin da bashi da mafita dolene sai mun haɗa hannu da Baba Garko, inba hakaba ko yazo hannu zai zama a banza ne, kai koda an kaisa kotu ne zai iya kuɓuta ma fa, idan ma an tsallake nan alƙali ya yanke masa hukunci to abokan huɗɗarsa zasu iya cireshi saboda yana huɗɗa ne da manya-manyan shegu na duniya bawai na Nigeria kawai ba. Duk da dai abu ɗaya dana sani ga manyan dilas na waɗan nan kayan a duk sanda sukaga zata kwaɓe musu ko zaka ci amanarsu zasu iya kashe juna. Ma'ana kamar yanda sukeyi akan duk wanda ya so bijire musu, shima ya koyo wannan ɗabi'ar ne a hannun turawan nan. Dan haka dolene zamuyi amfani da matakai uku na salon yaƙin kuma duk masu kamanceceniya da juna. Matakin farko shine Baba Garko, sai kuma kama duk wanda suke zagaye da Sulaiman ɗaya bayan ɗaya, hakan zaisa mu ruɗa masa hanjin ciki da jigata masa rayuwa mu sabautashi a tsaye. Hikimar saka Baba Garko anan itace yanada ƙarfi, sannan a fannin safarar miyagun kwayoyi shi maƙiyinsu ne, zai iya yin komai akan duk wanda hukuma ta cafke ta yanda bazasu taɓa kuɓuta ba. Mataki na biyu zamu ƙullama Sulaiman talala tsakaninsa da abokan huɗɗarsa musamman turawan nan na ƙasar Mexico. Kunsan duk wani shege akan harkar waɗan nan kayan yana ƙasar Mexico, saboda wannan matsalar na zagaye da rayuwarsu fiye da kowa a duniya, kuma nanne Sulaiman yafi safarar kayansa. Na uku dolene mu ɓoye kammu mu duka ta yanda idan muka kunnamasa wuta Daddy zai fara hara har zuwa wani mataki, saboda shi kaɗai yasan yana da camara ɗin nan, mu kuma zamuyi amfani da wannan fusatar tashi ne muyita fidda laifinsa waje ta yanda wasan zai zame masa gaba kura baya sayaki...”
Su duka babu wanda murmushi bai bayyana a kan fuskarsa ba, domin gamsuwa da shawaranta ɗari bisa ɗari. Albarka Daddy ya dinga saka mata, yayinda Uncle Yousuf ke tayashi. Smart dai na murmushi da binta da kallo ƙasa-ƙasa. Dan ya sake tabbatar da lallai matar tasa ƙwaruwace a lauyanci ashe tasan mutakeyi. Daddy ne yace, “Ni yanzu gaskiya bawani sanin kowa da kowa na cikin kasuwancin nayi ba, inma komai zai mana wahala sai dai wannan”.
“Shima bazai mana wahala ba Daddy, karka manta lungu da saƙo na sani, nasan manya da yara masu wannan business ɗin, kuma duk da haka zan nemo Nadiya itama, duk da bana jin zata bamu haɗin kai ta ciki sauƙi saboda abinda nai maita a last rabuwarmu, amma zan ƙoƙarta naga na ta dawo gareni saboda nasanta zata iya komai akan kuɗi, dan wannan ita ido ce a garemu tamkar google. A yanzu haka zan iya bada list na wanda wasan zai fara a kansu”.
Anan ma duk sun gamsu da zancenta, a take kuma ta zana musu sunaye da adireshin wajajen da take sayen kayayyakin, tun daga hannun ƙananan ƙwari har zuwa manya-manyan dila data sani a dalilin abokan huɗɗar nata. Ba kuma wai a wajen Kano kawai suke ba, a faɗin Nigeria gaba ɗaya harma da kasashen ƙetare dake maƙwaftaka da Najeriyar. Sosai Daddy yasha mamakin ganin waɗanda ta zano ɗin, har ma da Uncle Yousuf. Shi dai Smart ba kowa ya sani ba sai ɗaidaiku irin su Hon Nakowa suma dan sun kasance sanannun ƴan siyasa ne. Sai dai ganin sunan MM Atik Kumo ya sashi kallonta. Ta fahimci mi yake nufi, dan haka ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Shima Dila ne ai, ko'a ranar daka ɗakkoni a gidan nan tare da tsoffin nan gidansa ne, sannan shine ya sayar mana da kayan”.
“Shi wannan ɗin da nake gani simi-simi?”.
Lulu ta ce, “Humm bakaga komaiba ma, wasu ma dan ban san yanda zan misaltasu bane ku gane saboda sunan banza na sansu da shi, wasu kuma haɗuwar club ne kawai”.
Babu wanda ya sake iya magana dan sun san a zancen Lulun kam babu tantama...