← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 90

Sashe 17

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yau wayar Smart da Abbah ita ta haskakama matan gidan mi ake ciki, dan Umma na tare da shi ne a sanda Smart ɗin ya kira sa kasancewar itace da girki yau ɗin. Ƙagara tai Abba ya gama wayar jikinta har karkarwa yake ganin numbar da aka kira Abban kuma taji ya ambaci Aliyu ta fara da +44.. yana gamawa cikin rawar harshe ta ce, “Alhaji wai wane Aliyu kuma ka samu da lambar wajen ƙasar nan haka?”.
Kai tsaye cikin rashin damuwa Abba ya bata amsa da cewar, “Aliyu na ma. Ai yana can ƙasar turawa buga ƙwallo. Yanzu haka ma ya kirani ne yana faɗa min sunci wasan da tun kusan kwana biyar kenan yake faɗin mu tayasu da addu'a akai dan wasan nada ƙalibale sosai. To Alhamdullah sunci kuma shine ya saka kwallon har sau biyu bayan har sun fidda rai ga hakan”.
“Tofa sabon zance, shi Hydar ɗin ne ya tafi ƙasar Turai ƙwallo amma mu da muke a gidan bamu da labarin hakan? To Alhaji wani sabon makirci ne yazo ake ɓoye mana hakan kamar wasu masu baƙin ciki ko mugun hali ko yaya ne!!?”. A hasale Umma ke magar har idanunta da suka kaɗa jajur na tara ƙwalla.
Abbah da sai yanzu ma shi ya tuna cewar babu fa wanda yasan ina Aliyun yake bayan shi da Ammah da Bilkisu ya tsurama Ummah idanu da mamakin ganin yanda take kumfar baki. Sai dai maimakon ya mata masifa kamar yanda ta hayayyaƙo masan sai yay yinƙurin son fahimtar da ita dalilin ɓoyewar tasu cikin hikima. Amma abin mamaki Ummah ta birkice masa cikin ɗaga muryar data jawo hankalin jama'ar gidan gaba ɗaya zuwa sashen Abbah. Tun Umma na jidali da Abba a ɗakinsa har fa ta fito tsakar gida ta maida abin kan Ammah. Nanfa Mama itama ta ara ta yafa jin ba'asi, yayinda samarin gidan da sauran yaransu suma dai maganar tai mugun dukansu. Ammah dake da ga falonta zaune shiru kawai tai tana sauraren jidalin da Umma da Mama keyi, sai aunty Amarya dake basu haƙuri da faɗin ita bataga abin tada jijiyar wuyaba anan, kamata yay a kwantar da hankali aji dalilin su Abban nayin haka dan bazasu ɓoye ba ai da gangan dole suna da dalilinsu. Neman dawowa faɗan yay akan aunty Amarya, suna cewa itama ai munafukar ce, tunda tana naniƙe a jikin Ammah dan ƙwaɗayin ganin ƴaƴanta na auren masu kuɗi dole tace haka. Maybe ma tasan da tafiyar Aliyun amma taja bakinta tai shiru saboda makircinta da munafurci. Aunty Amarya kusan halinsu ɗaya da Ammah, itama bata da faɗa sai in an kaita maƙura, dan haka tai musu shiru da ga farko, sai da taga suna neman keta mata mutunci a gaban yaransu itama ta fara zazzaga musu nata masifan. Nan fa gida ya sake harmutsewa har sai da Abbah ya fito da ga ɗakinsa a fusace.......✍️

_🥱Shin Hajiya Yahanasu babu rami miya kawo rami ne?._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣

........Cikin rufewar ido da nuna ɓacin rai Abba ya tsawatar musu. Ganin Umma na gunguni ya ce, “Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ta bar min gida a wannan daren. Kuna son maidani wani shasha ne? Kuje an ɓoye muku tafiyar Aliyun kuyi duk abinda kuke jin zaku iya yi dan ALLAH marasa mutunci kawai”. Da ga haka ya koma ciki fuuu ya barsu da harare-harare. Duk abinda akeyi Ammah na jiyosu amma ko leƙowa batai ba, ta kuma hana har su Asma'u leƙowa wajen. A haka aka kwana cikin ɓacin rai wannan dare. Tun kuma a daren su Umma suka bazama sauran ƴaƴansu bayani ta waya cikin nuna hassada. Haka ma ƴan anguwa da rikicin ya ɗan shiga kunnuwansu musamman maƙwafta aka fara riƙe bakin mamakin jin Aliyu ashe baya Nigeria, duk ƙaryar da su Umma keta bazawa matan anguwa cewar ya gudu Lagos saboda dangin matarsa sun ce sai ya saketa ashe ƙarya ce. A wannan dare Umma bata koma ta kwana ɗakin Abba ba, washe gari sai ga yaran gidan na ma'auri nata zuwa musamman mazan tunda safe a cikin tashin hankali. Salim babban ɗan Umma da take ji dashi da fariyyar yafi kowa kuɗi a gidan shine tsageran tunkarar Abbah da maganganun rashin kunya wai yana nuna musu banbanci akan Aliyu. Sai da Abba ya gama saurarensa tsaf sannan ya zageshi ciki da bai da faɗi masa ashe sai yau ne suka san matsayin Aliyu da mahaifiyarsa a wajensa. To bari ya ƙara tabbatar musu da cewar Ammah ta daban ce a zuciyarsa, dan itace first love ɗin sa. Ta auresa a sanda baida komai, yayinda mahaifinta ya tallafi rayuwarsa batare da ƙyama ba a matsayinsa na almajiri, da ya nuna yana son ƴarsa ko sau ɗaya bai nuna ta fisa ba ya aura masa. Tun suna zama a gidan haya ɗaki ɗaya har ALLAH ya horo masa gidan kansa. Ammah tasha rufama rayuwarsa asiri da danginsa da abunta bata taɓa nuna masa isgili da hakan ba koda a cikin wasa. Tayi haƙuri da shi ita da iyayenta akan rashin haihuwa, har sai da uwarsa ta shigo da ƙarfin tuwo ta haifesa shi da ƙaninsa Sadiq kafin ALLAH ya bata cikin Bilkisu. Amma bata taɓa nuna baƙin cikinta ko hassada akan wata tazo a bayanta ta haihu ba. Uwar tasu da suke gani matsayin ƴar uwarsa shi bai taɓa jin sonta ba, da biye-biyen dangi ta kama ƙafa aka tilastashi aurenta... Wannan magana ta Abba taima Umma zafi matuƙa, har ta kaita da fashewa da kukan wai Abba naci mata mutunci a gaban kishiyoyi. Duk da Mama da ita aka fara fitinar sai gashi ta koma yima Umma dariyar ƙeta. Dan ba ƙaramin wankin babban bargo Abba yay mata ba a ranar. Har sai da ta kaita da kuka da hawaye. Da ga ƙarshe ta shige ɗaki ita da ɗiyanta suna zagin Ammah da jawa Smart mugayen addu'oin rashin nasara badan ya musu laifin komai ba sai hassada da uwarsu ta cusa musu kawai a ransu matsayinsa da ɗan uba garesu. Ɓacin rai ya saka Ammah tattara kowa a gidan ta watsar, inda cikin hikima ta nusar da aunty Amarya akan kada ta sake biyema su Ummar dan ALLAH. Tako ji maganarta dan itama ta kame kanta dana ƴaƴanta waje guda kamar yanda Ammah tayi.

         Tun a ranar Umma tai kiran Hajiya Naqiba ta sanar mata komai cikin ɓacin rai. Ran aminiyar cin mushen nata ya ɓaci itama. Inda ta balbale Umma da faɗan miyasa ta kasa riƙe kanta ne ta fito tai magana haka har miji na mata tonon silili a tsakiyar ƴaƴa da kishiyoyi maƙwafta na saurare. Cikin damuwa da hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Rainane ya ɓaci wlhy Hajiya Naqiba. Kiga wahala da kashe kuɗin da nai akan yaron nan amma sai da ya tafi wannan shegiyar tamaular da na dutse ya tabbatar min itace silar arziƙinsa da bama gidanmu ba hatta ƴan anguwa nan sai ya riƙe da dukiyarsa. Wane irin koma baya ne ya sameni da har haka zata kasance. Wai yaushe ma ƙullin malam Na-zuru ya kwance akan yaron nan?. Haka fa zancen aurensa sai ji kawai mukayi, yanzu dan cin amana da makircin wannan shegiyar matar dake wani sim-sim kamar ta ALLAH za'ace wai yana Turai......”
     Ƙaramar dariyar data katse Umma Hajiya Naqiba tayi, sai kuma tai saurin faɗin, “Yi haƙuri wlhy kece kika ban dariya da kikace sim-sim. Bayan kinsan Hafsatu ba sim-sim bace ba kawai dai tana kwasar ƙurarku ne ta watsar. Amma matar da in ta tashi muku wankin babban bargo sai kun kasa sukuni kike jinginawa da sim-sim, kawai dai shegen girman kai ne da ita kamar yanda ɗan nata ya gado saboda taga ta fiku komai. Ubanta mai arziƙi, tanada ƙyau, gata da ilimi kamar zai kasheta duk da ma bata son nunawa.....”
       “To wai ni ban gane ba, yabonta kike ko minene?”.
    “A'a rufamin asiri, wane yabo zanma kishiya nikuwa. Kinga mubar zancen tunda kin gagara fahimtata. Yanzu dai bamuga ta zamaba kenan. Dan na fahimci makircin da muka ƙullo a gidan Garko ba dukane yay tasiri ba ko kuwa yaya miya faru?”.
             “Dan tasiri fa yayi tasiri, tunda gashi har sun ƙwace ɗiyarsu daga hannunsa. Abinda dai zamuyi shine shima fa makircin sai an haɗa mishi da ƙulli....”
       “Ƙulli wane iri? bayan wanda mukayi”. Ummah ta katseta da sauri. Ɗan jimmm Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai kuma fa haka ne, to kodai tsohuwar nan bata bama yarinyar nan rubutun nan ba ne? To aiko da sakel, dan dolene kiyi duk yanda zakiyi a satin nan mu shiga wajen Malam Na-zuru. Dan ba'a bori da sanyin jiki, dolene mu sake tashi tsaye akan wannan ɗan iskan yaron kuwa.”
      “A yanzu kam da ya hau sama bana jin zai bar wata fita a gidan, sai dai ki taimaka min kije zan kirashi ta waya mu fara magana kafin kije”.
      “Shike nan hakan ma yayi kuma dabara ce. Dan ko wani abu ya biyo baya ma baza'a zargeki ba kamar wancan sai dai suyita tunani cikin abokan tamaular tashi ne”.
      Haka suka cigaba da tattauna mugayen ƙudirinsu akan Smart da Ammah iri-iri kamar basa tuna mutuwa mai gaggawa da kan iya ziyartar bawa a kowane lokaci a kowane irin yanayi mala'ikan mutuwa shi mai cika umarnin UBANGIJI ne.......

     (ALLAH ka gafarta mana ka tsarkake mana zukatanmu, ka hanamu damar saɓa maka balle ta kaimu ga shirka ko cutar da wani mun akan abinda bazamu taɓa iya sakawa ko hanawa ba.😭🙏)  

          *_CANADA_*
Chapter 17 · 0% Book details