← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 90

Sashe 79

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Ranar yini yay barci, dan sai azhar ya tashi. Babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai. Yay wanka ya shirya cikin ƙananan kaya marasa nauyi. Suna falo zaune Iya Tabawa na basu labarin sanda suna ƴammata Lulu na kwasar dariya kamar ba ita tasha kuka jiya ba ya fito, sam ita bata da riƙe abu, shiyyasa idan aka riƙeta take jin zafi. Da gudu AA dake wasa ya nufosa. Cak ya ɗaga yaron sama yana mai sumbatarsa cike da jin ƙaunarsa. A haka ya kai zaune cikin kujera suna dariya shi da AA ɗin da yakema cakulkule. Iya Tabawa ya fara gaisarwa sai aunty Bilkisu. Ya tambayeta yaya jikin tace Alhmdllh sai fatan komawa gida lafiya. Murmushi yay da faɗin, “Ai keda Nigeria sai nan da shekara ɗaya”.
      Idanu ta waro sosai da faɗin, “Shi kuma mijin nawa kuyi yaya da shi?”.
    Cikin kauda kai da taɓe baki ya ce, “Uhm su miji”.
Kafin aunty Bilkisu ta sake cewa wani abu a fisge Lulu tace masa “Good Afternoon”. Kallonta yayi shima a karo na biyu cikin ɗauke kai yace, “Afternoon” a taƙaice. Daga haka babu wanda ya sake kula ɗan uwansa. Abinci ma sai da aunty Bilkisu ta zungureta ta tashi ta kawo masa. Batai zaton zaici ba, amma sai taga yaci sosai yana bama AA. Bata san yayi matuƙar kewar girkin nata ba ne. Basarwar da yake ɗin ma ta dole ce. Haka ya ƙarasa yinin nan a gida yau ko waje bai leƙa ba har washe gari. Washe garin ma sai zuwa yamma ya fita training center ɗinsu........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣

.......Kwana uku ya ɗan fara hucewa a dalilin murar zazzaɓi da Lulu ke fama da shi. Duk da dai tana nuna ita ƙalau take. Sai da murar tai mata tsanani ne ta haƙura takai zaune. Mata da miji sai ALLAH sai gashi yana tattalinta da matsa mata tasha magani. Harda haɗa mata shayin kayan ƙamshi da kansa. Idan yaga AA zai takura mata ya ɗaukesa ya kaima Iya Tabawa. Ya bata kulawa sosai harta samu sauƙi. Da ga haka aka shirya kamar basu ba aka koma nunama juna soyayya da tattali. Sai aikinsu da suka saka a gaba. Ita aunty Bilkisu ma sai abin ya koma bata dariya. Shiyyasa dai akace duk wanda ya shiga tsakanin mata da miji ya matse. Dan zasu shirya ne su barsa a ciki. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa mura na damun Lulu akai-akai. Ita abin har mamaki yake bata dan bata cika yawan mura ba a da. Sai dai ta danganta yanayin da sanyi da ake yi sosai harda dusar ƙanƙara.
     Wasan su Smart na tafiya cike da nasarori da kalubale. Yayinda sunansa keta ƙara cigaba da amsa kuwa saboda yanda yake zura ƙwallaye a raga babu ko ɗar. In dai za'a kirayi sunan wani yaro mai tashe a wannan ƙarnin a harkar ball idan sunansa baizo na ɗaya ba dolene yazo ana biyu. Ballema ALLAH ya bashi farin jinin da akan ambacesan a farko. Sam baya wasa da addininsa. Sannan tsaye yake akan Lulu itama dan har yanzu shine mai ɗora mata karatu datai matuƙar maida hankalinta a kai. Wani lokacin kuma aunty Bilkisu ke ɗora matan.. A gefe kuwa sun matuƙar saka rayuwar Alh. Sulaiman a gaba, dan a yanzu haka ana tsaka da dambarwa ne tsakaninsa da amaryarsa akan Flash. Anyi-anyi ta bada taƙi. Yayi haukan yayi hargagin yayi kurarin duk da tana a gidan nasu tayi kememe. Hajiya Turai dai ce ƴaƴanta suka dawo da ita. Acewarsu sai da Mahaifin nasu ya bar mata gidan badai ita ta bar masa ba. Dan babu kunya suka dinga yaɓa masa magana musamman ma Tajuddeen, Alh. Sulaiman ranar harda hawayen baƙin ciki. Bai taɓa tunanin soyayyar da yakema Tajuddeen zai iya kallon tsabar idonsa ya masa rashin kunya haka ba, al'amarin ya girgiza zuciyarsa kam..

(Abinda kayi dole ai maka ai dama🚴🚴🚴😂).

           *_NIGERIA_*

   Watanni kusan huɗu kenan abubuwa na'a rincaɓe musamman a ɓangaren Alh. Sulaiman Garko. Dan anata musu tsinci ɗai-ɗai na masifa ta yanda gaba ɗaya kasuwar tasu ma ta tsaya cak. Ga manyan kayansu da ke gaf da zuwa Najeriya ɗin. Duk yay wani iri da shi duk da har yanzu ma shi bako a fara taɓashi ba. Dan ko'a cikin yaransa kaf babu wanda aka taɓa. Sai aminansa da Hon. Nakowa kawai ya rage sauran duk suna hannun hukuma anyi ram da su. Kullum cikin kiran Daddy yake yana masa barazana. Shiko Daddy na maida shi mahaukaci da naɗe komai a waya tare da kunnashi. A gefe ɗaya ga al'amarin amaryarsa da yaƙi ci yaƙi cinyewa. Burinsa kawai ya amshi Flash ɗin hannunta koda zai kasheta ne shi babu ruwansa. Tayi-tayi ya saketa kuma yaƙi. A randa yaje har gida ya cima mahaifinta mutunci ta tabbatar masa anzo gaɓar da take jira, dan haka a ranar ta aike ma su Baba Garko da video. Da kanta ta shirya taje har gidan ta danƙama Baba Flash. Har wulaƙanci Dada taimata saboda taje ta gaida amarya da duba yaranta. Ita dai bata tanka mata ba har Dadan tayi ta gama san ranta. Bayan wucewarta ne Dada ta nufi wajen Baba Garko. Ta sameshi da ƴan biyunsa da sukai kuɓul-kuɓul gwanin sha'awa. Takaici kamar zai tsayar mata da numfashi amma ta danne da ƙyar. Dama bata taɓa ɗaukar yaran ba tunda aka haifesa, dan haka yanzun ma kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta. Ko'a ƙwallar rigar Baba Garko, dan ya jima da fahimtar bakin ciki take da yaran. Sama-sama ya amsa mata gaisuwa ya cigaba dama yaransa wasa kamar ma ya manta da ita. Hakan ya sake Zafafa mata zuciya taji ta tsani yaran fiye da ko yaushe. A cikin tunzura ta ce, “Amma dai Alhaji bai kamata ka fifita rayuwar ƴar wasu akan naka ba. Yanzu yarinyar nan ta gama fetse mana yaro da iskance-iskanceta ta dawo tana mana barikanci. Ni na rasa mi Sulaiman yayi maka haka da zafi ne. Kabi ka tsangwamesa babu laifin tsaye babu na zaune. Idan ma maganar Mawaddat da Tajuddeen ce ya kamata ace ta wuce tunda dai tana gidan mijin da kuke son ganin nata da shi yanzu ai ko”.
        Idan ɗakin ya tanka Baba Garko ya motsa, hakan ya sake harzuƙa Dada. Miƙewa tayi a fusace zuwa gabansa ta ɗauke Flash ɗin dake ajiye kusa da shi. Nan ɗin ma bai tanka mata ba harta fice, bai kuma nuna damuwa da ya bita akan flash ɗin ba ya cigaba da yima yaransa wasa. Hajiya Dada kam da masifa ta nufi sashenta. Harta ɗauki waya da nufin kiran Alh. Sulaiman akan yazo ya amsa sai kuma ta ajiye tana faɗin, “Bara dai naga wai ubanmi akema wannan tashin hankalin ne a ciki.” Ta ƙwalama mai aikinta kira. Jiki na rawa ta iso, a gabanta ta zube cike da girmamawa. Umarnin ɗauka mata tab.. a ɗaki ta bata. Babu jimawa ta dawo ɗauke da tab.. ɗin. Ita ta saka mata flash ɗin. Cike da gadara da ƙasaitar mulkin masu akwai Dada ta amsa ana wani gyara zama da busa iska tace mai aikin ta kawo mata lemo. Ita dai mai aiki umarni take bi.
        Fuskar data fara bayyana ta saka ƙirjin Dada bugawa, jikinta ya fara tsumar kewa. Mawaddat ɗinta ce, yarinya mai hankali, mai sonta da ƙaunarta, sai dai ita kullum tana a cikin hantararta ne saboda tana ce mata kaza ba daidai bane kaza ne daidai. Kalaman Mawaddat suka cigaba da jan hankalinta kafin kace mi ta jiƙe sharkaf da zufa. Maimakon hasken ɗakin ta koma ganin duhu. Tun tana iya jin sauti da motsi har komai ya tsaya mata cak sai razanannen ihunta daya karaɗe kunnuwan duk wanda ke a kusa da sashen nata. Rige-rigen shiga masu aikin nata suka shiga yi inda take, sun sameta wanwar a ƙasa kofin lemon da aka ajiye mata ya kife da alama ma a kansa ta faɗa. Duk da hankalinsu ya tashi da ganin a yanda take sai da suka ɗauki tab.. ɗin suka kalla abinda ya razanatan. Yayinda mai tausayin cikinsu ta fita a guje kiran Baba Garko. Ai suma sai suka ƙare da ƙwalla ƙara a dai-dai shigowar Baba Garko da amaryarsa, dan tana tare dashi sanda mai aiki taje kiransa....
Chapter 79 · 0% Book details