Sashe 56
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣
.......Al'amarin Umma kamar wasa ƙaramar magana ta fara zama babba. Dan ita kanta tun tana ɗaukar abun matsayin ba komai ba sai gata ta fara hawaye cikin tashin hankali. Dan kuwa dai ƙawarta Hajiya Naqiba tazo, amma tana shiga ɗakin nata itama da gudu ta dawo tana ihu mai firgitarwa da yafi na jama'ar gidan. Hankali tashe Umma ta biyota tana faɗin, “Na shiga Uku ni Yaha, Aminiya kema ɗin abinda suke min zaki min? Wai mina muku ne haka kuke irin wannan firgita da ni? Dan ALLAH ki faɗamin Aminiya kar ki min yanda suke min kema”.
Ina Hajiya Naqiba ba sauraren Umma take ba. Ihu kawai take kwarawa da iya ƙarfinta har maƙwafta da mutanen waje na iya ji, daga ƙarshe ma ta yanke jiki ta faɗi a sume dan Ummah taƙi daina binta. Cikin tashin hankali Umma ta isa gareta ta na jijjigata, a dai-dai nan mutane suka fara shigowa gidan da ga waje hankali a tashe. Ai sai ga maza na dafe huluna suna juyawa a guje. Duk wanda ya shigo yana tozali da Umma rungume da Hajiya Naqiba sai ya afa da gudu ya juya. Ba matan ba ba mazan ba ba yaran ba. Cikin ƙanƙanin lokaci zance ya zagaye anguwa. Masu ƙarfin hali na cigaba da shigowa domin tabbatar wa. Sai dai fa babu fashi duk wanda ya shigo zai juya a gujensa yana ihu da faɗin “Wayyo Dodo!! Wayyo dodo!!.”
Umma da ke zubama hajiya Naqiba ruwa tana kuka dan ganin abin da bana lafiya bane ta zabura jin aminiyar tata ta sake fasa gigitacciyar ƙara. Dan tana farfaɗowa taci karo da ita a kanta. Yin ƙurin da zatai domin ceton ranta ƙafa ta gurɗe jikake ɓass kamar an ɓalla katako ba ƙashi ba. Sai ta sake zubewa a ƙasa cikin wata irin wahalalliyar ƙarar azaba ta sake sumeya. Duk da abinda ke faruwa kaf ƴan gidan na maƙale ta windows suna kallo har ƴaƴanta da suka rarrabu. Wasu a ɗakin Ammah wasu na Mama. Ita dama aunty amarya da yaranta ɗakin Ammah suka afka suma. Ammah da al'amarin ya jijjiga ma zuciya na zaune a kujera tana cuɗawa da kwancewa. Dan in har lissafinta yayi dai-dai ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya fa a wannan karon. Tukunyar da suka gani tarwatse a tsakar ɗakin Ummah itace asirin da taima su Aliyu matarsa ke ganinsa da mummunan siffa irin wadda suke ganin Umma da ita a yanzun. Abba ne yay hikimar kiran yaranta na ma'auri da su Salim yace suzo babu lafiya. Dan shikam yama rasa ina zai kama a wannan lamari. A yau dai ya sake tabbatarwa Umma na bin bokayen tsubbu, kuma tabbas akwai ƙamshin gaskiya mai kamanceceniya da juna akan al'amarin Aliyu da matarsa da wanda Umma ke'a ciki yanzu. Yau matar Aliyu ta koma wajen mijinta, hakan na nufin komai ya daidaita tsakaninsu asirin ya dawo inda aka aikashi. Dama ai sharri ɗan aike ne, idan ya isar da saƙonka sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Har zai kira Smart sai kuma ya fasa cikin girgiza kai dan a yanzu ya tabbatar dare ne a UK.
Yaran nata ma koda suka iso duk wanda yay tozali da Umma sai gudun ceton rai. Umma ta fashe da kuka da tun ɗazun take irinsa har muryarta ta dishe. Ga aminiyarta kwance ƙafa sai kumbura take kowa ya kasa zuwa a taimaka mata saboda Umma da ke a wajen. Al'amarin dai sam babu daɗi, Umma na cikin tashin hankali fiye da wanda al'umma ke ciki akan ganinta a mummunar halittar da kowa ke ganinta. Ita kuma lafiya Lau take kallon kanta, dan har ɗaki ta nufa ganin kanta a madubi babu wata damuwa ko tawaya tattare da halittar ta sai fuskarta datai kace-kace da hawaye har idanunta sun kumbura. Kafin ta fito ne aka samu aka ɗauke Hajiya Naqiba dake kwance bata da banbanci da gawa. Dole asibiti aka wuce da ita a gaggauce dan ƙafar tayi masifar kumbura damm abin zattashin hankali......
*_UK_*