Sashe 73
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tashin hankali Lulu ke kallon Smart. Dan duk abinda ke faruwa tsakanin Alh. Sulaiman da matarsa akan idonsu ne kasancewar sun saka direct camara a jikin Alh. Sulaiman batare daya taɓa farga ba. Sun yi wannan aikinne kuma a lokacin da ya tafi jiyya bayan jami'an tsaro sun sake sa akan kidnapping ɗin Lulu da yayi. Sun haɗa baki da likitansa aka saka masa camara a gefen kunne ta wajen wuyansa a zuwan wani tabon theatre da akai masa ne a wajen wai na'urar na rike jijiyar kunnensa. Wannan aikin Uncle Yousuf ne, sun zaɓi saka masan ta yanda bazasu gansa ba sai dai suga abinda yake aikatawa saboda yanayi na yau da kullum irin na ɗan adam. Wanka da makamantan hakan. A kuma duk lokacin da zai shiga ɗaki da matansa ko aikata wata Masha'arsa da karuwansa sukan tsaida gani daga wajensu domin kiyaye dokar ALLAH. Ta wannan direct camara suke sanin duk wani motsin Alh. Sukaima batare da shi ya farga da hakan ba dan yana kallon abinda aka saka masan ne a yanda aka faɗa masa cewar tana riƙe jijiyar kunnesa da ta samu matsala.
“Wannan mahaukacin fa zai iya kashe matar nan. Ya kamata muyi wani abu”. Lulu ta faɗa cikin tashin hankali itama ganin yanda Kawun nata ya fita a hayyacinsa. Murmushi kawai Smart yayi yana ɗan lumshe idanu da zamewa ya kwanta. Kamar bazaice komai ba sai kuma zuwa can ya firzar da iska yana bata amsa da, “Babu abinda zai maita, wannan hargagin da kikaga yanayi na rashin mafitane kawai da ruɗanin da yake a ciki. Amma ba itace a gabansa ba yanzu Daddy ne da ke sai kuma mu da yake son sanin su wanene. Ina mai tabbatar miki yanzu haka gidan Daddy zai je”.
Da sauri Lulu ta ce, “What! Gidanmu fa kenan?” sai kuma ta fisgo computer ɗin gabanta ta sake buɗewa batare da jiran amsar Smart ɗin ba. Ilai kuwa sai ga Alh. Sulaiman na kwaɗa gudu a saman titi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a anguwarsu, a ma ƙofar gidansu. Sai dai ya gagara ƙarasawa saboda jami'an tsaro da ke zagaye da street ɗin ma gaba ɗaya musamman jikin gate ɗin gidan nasu. Wani irin duka ya kaima steering ɗin kamar zai fasa ihu. A haukace yay reverse ya koma ganin jami'an tsaron sun yo kansa.... Bata ma san lokacin data kwashe da dariyar data saka Smart buɗe idanu yana kallonta ba...
___________________★
Abubuwa tako ina suna cigaba da kwaɓema Alhaji Sulaiman Garko. Domin kuwa da zaman meeting na maganin matsala da yayi musu. Dan kullum a cikin yinsa suke. Kowace hanya sunbi domin ganin sun cutar da Daddy ko zuri'arsa al'amarin ya gagara. Yanda Daddyn ke zagaye da jami'an tsaro lamari ba'a cewa komai. Sun kai hari gidan su Smart shima dai, sai dai anyi rashin sa'ar samun gidan a baje sai masu aikin gini. Iya bincike kuma kowa a anguwar sai yace bai san inda suke ba a yanzun. Fahimtar kamar raina masa wayo sukeyi ya sakashi komawa gida rai a ɓace neman mafita. Kowa bai nema ba a matansa ya nufi sashensa kamar zai tashi sama. Wani irin kallon ɓacin rai yabi falon da shi, ganin yanda ya barsa a harmutsensa haka ya dawo ya tadda abinsa. Abinka da mai zuciya a kusa, tuni ransa ya sake ɓaci. A dai-dai nan Hajiya Turai ke shigowa sashen nasa. Ganin ko'ina a harmutse ga shi yanata faman huci ya sata zuba masa ido. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Alhaji lafiya kuwa kake miya sameka haka?”.
“A'a a cikin turnuƙun yaƙi nake? Ke ban san iskanci fa da rainin wayo”.
“Ikon ALLAH, ALLAH ya baka haƙuri da ga tambaya”.
Bai sake tanka mata ba, itama saita fara ƙoƙarin tattara falon. Taɓa Laptop ɗin sa da tayi ya sashi tunawa da Flash ɗin dake jiki. Cikin tsawa ya ce, “K bani ita nan!”. Bata musa ba ta miƙa masa zuciyarta na sake shiga mamakinsa. A fisge ya amsa. Sai dai me babu Flash ɗin a jiki. “Ina Flash ɗin jiki yake?”.
“Flash kuma? Ni banga wani Flash ba, a gabanka fa na ɗaga ta”. Wani irin kallon zan kashe ki na binne anan ya shiga binta da shi. Hannu ya miƙa mata alamar bani. Sai duk ta sake dabircewa. “Wai Alhaji kana lafiya kuwa. Wlhy ban ɗaukar maka wani Flash ba. A gabanka fa na ɗaga Lap-top ɗin nan ba wani waje naje da ita ba balle kace.”
Babu zato babu tsammani taji saukar mari har biyu. Kafin ta gama dawowa a hayyacinta ya sake miƙa mata hannu da tsananin tsawa yace, “Turai!! Bani”.
“Wlhy tallahi Alhaji ban ɗaukar maka komai ba. Wai yau ka fara zama dani ne? Koka taɓa ajiye abinka ka nema ka rasa da har zaka ɗaga hannu ka maran!”.
“An mareki ko zaki rama ne?”.
“Bazan rama ba, amma zan barka da ALLAH”. Ta faɗa tana ficewa fuuu. Mutumin naku tuni zuciyarsa neman fitowa take ta baki, amaryarsa da ya bari a falon nasa ta kuma ji komai ce tazo masa a rai. A harzuƙe ya nufi sashenta, babu ko sallama ya banka ƙofar ya shiga. Baiko kalli ƙanwarta dake gaishesa a falo ba ya wuce bedroom ɗinta kamar zai tashi sama.
“Wlhy aunty ba ƙazafi bane ba naga komai fa da idona, kuma na faɗa miki ƙanwar nan tasu data rasuce ma fa a video ɗin, ɗayar kuma ƙanwar tasu ce ta ɗauka mahaifiyar yarinyar nan da ake cema Lulu....”
Waɗan nan kalamai da suka nema fasa zuciyar Alh. Sulaiman ne ke fitowa da ga bakin amaryarsa. Abinda kuma yaji na tabbatar masa taga komai da komai kuma ta faɗa ma wadda suke wayar. Ta buɗe baki zata sake magana idonta ya sauka a kansa. Zabura tayi, kafin ya iso gareta ta kwasa da gudu ta shige toilet ta banko ƙofar. Yana dannawa tana dannowa har dai ALLAH ya bata sa'a ta murza key. Wasu manya-manyan ashariya ya fara mulmula mata yana jijjiga ƙofar tamkar zai cireta. Itako duk da a tsorace take faɗi take, “Wlhy ko zaka kasheni bazan bada ba”.
Ashariya ya cigaba da ingiza mata da tabbatar mata wlhy sai ya kasheta.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣
......Sosai Smart ya tsinta kansa cikin farin cikin ganin ƴar uwarsa, duk da tana kwance a gadon asibiti hakan bai hanasu yin hira ba. Anan ne take basu labarin halin da Ummah ke ciki a yanzu. Babu ɗigon tausayinta a zukatansu sai Smart kawai, duk da yana jin ɗacin rabashi da matarsa da tayi hakan bai hanashi jin tausayinta ba. Dan ko babu komai tunda ya taso kallon uwa yake mata, sannan jininsa ce ita tunda ƴar uwar Abba ce. Sun jima a asibitin, dan Smart ya gana da doctor sun tattauna, daya buƙaci yanda biyan kuɗi zai kasance sai ya samu Lulu ta biya komai har kuɗin aiki dana gaba ɗaya zaman da zatayi ma a asibitin. Kasa cewa komai yayi har suka dawo gida. Sai dai sun sauke Ahmad a masauki. A falo suka sake zubewa aka ɗaura hira, Iya Tabawa na basu labari suna kwasar dariya. Sun jima a wajen kiran wayar Smart da akayi ne ya sashi miƙewa ya shige bedroom, hakan ya bama Lulu damar bin bayansa bayan wani lokaci. Ta samesa har lokacin yana waya da Usman da ke bashi labarin irin halin ruɗanin da Alh. Sulaiman da abokan cin mushensa suke a ciki. Sai saƙon daya bada aka aika masa ɗin nan. Sosai Smart ke kwasar dariya har yana jin inama yana Nigeria yaga wannan ruɗani a fuskar Alh. Sulaiman. Sai dai babu komai yasan zai gani ta cikin direct camara ɗin da suka sanyama Alh. Sulaiman batare daya sani ba. Bayan sun gama wayar ne yake bama Lulu labari, itama dai dariyar tasha da jin inama tana 9ja ake wannan irin cakwakiya haka.
AA ya tambayeta ta ce ai ya koma kwana wajen Iya Tabawa. Da mamaki yace, “Abincinsa fa?”.
“Wane abinci kuma bayan wanda yake ci ya ƙoshi. Ai ni na yayesa”.
“Yaye a wata goma sha ɗaya? Wane irin rashin tausayine haka Baby luv”.
“Haba kai kam miye abin rashin tausayi anan. Nifa wlhy dama so nake ya taka kawai, yaron da dama ba wani ya damu da shan nonon bane ba.”
“Kin dai so yayesa saboda kina buƙatar wani babyn”.
“Kamar ya?”.
“Kamar yanda kika ji mana”.
Ganin kamar cikin ɗan zafi yay mata maganar ya sata jan bakinta tai shiru. Ita matsalarta da shi kenan saurin fushi. Abu kaɗan bazai fahimcesa ba sai ya hau kamar fulawar burodi, sai idan shi yaso shanyewa ya nuna kamar bai gani ba. Bata yarda ta sake magana ba. Shima sabgar gabansa ya cigaba da yi batare da ya kulata ba. Ganin abin nasa babbane ta fita ta bar masa ɗakin dan bata buƙatar wani ɓacin rai kuma a yanzu....