← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 90

Sashe 49

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Tafe yake a nutse kan ƙafafuwan sa. Da ka gansa kaga tsayayyen mutum mai cike da jatumta da lafiyar gaɓai. A komai nashi babu hayaniya babu ɗagawa duk da wasu kan fassara shiru-shirunsa da girman kai tun bai zama wani ba. A duk sanda yake da uzuri na fita ya kanfi buƙatar takawa da ƙafarsa in har wajen da yake son zuwan babu nisa. Kamar dai yau da ya fita zuwa shopping na ƴan abubuwan buƙatarsa. Ya riga da ya kai wani matsayi a yanzu da fuskarsa ta zama ba ɓoyayya ba musamman a cikin birnin London. Hakan yasa a duk sanda yake da buƙatar irin fitar nan yakan sakaya fuskarsa da abinda zai ɓadda masa kamanni. Kamar dai yau, ya saka facemask da glasses, ya kuma ɗaura p-cap duk dai cikin son kaucema idanun jama'a dan yaje ya dawo batare da kowa ya damesa ba. Alhmdllh har ko yaje ya dawo babu wanda ya ganesan, garama a cikin mall ɗin da yaje biyan kuɗi kasancewar dokace sai anga fuskarka da yaja nurse mask ɗin ƙasa mai cire kuɗin ɗin ta wani zaro ido bakinta a washe zata ambaci sunansa yay mata murmushi da mata alama zip abaki. Dole tai shiru amma murmushi da farin ciki yaƙi barin fuskarta, har da ɗan leƙensa da zai wuce, sai da ya fice gaba ɗaya take faɗama sauran ƴan uwanta da ke wajen harda masu cewa basu yarda ba. Wasu kuma suka biyo bayansa. Ya riga ya zargi za'a iya yin hakan dama sai yana fitowa ya canja hanya. Wannan yasa suka sake tabbatar mata basu yarda ba. Ba komai ya sasu jin basu yardan ba sai dan mall ɗin nasu ƙarami ne, a ganinsu Smart Mawashi yafi ƙarfin zuwa nan yin shopping. Irinsu ma sunfi son yin online shopping a manyan mall ai.
         Ɗayan hannunsa da babu kaya ya fiddo da ga cikin aljihu wandonsa ya saka security ɗin ƙofar. Sai da computer ta ambaci sunansa sannan ƙofar ta buɗe kanta a hankali. Numfashi ya ɗan furzar yana tura kansa cikin gidan bakinsa da sallama duk da yasan shi kaɗansa ne a gidan nasa. Tuni ya samu canjin wajen zama. A inda yake nan gida ne shi kaɗai a ciki madaidaici mai ƙyau da tsarin birgewa, dan yana ɗauke da abubuwan more rayuwa da ɗan adam kan buƙata koda da sha'awa ne. Ya cire takalmansa a inda yake ajiyewa yasa slippers na zaman gida, tare da hanging rigar sanyinsa sannan ya ƙarasa shiga. Ya ɗan bi falon da kallo ganin fitila a kunne ga wani baƙon ƙamshi, sai dai bai kawo komai a ransa ba ya ɗan ɗage kafaɗu da taɓe bakinsa tunda yasan dai bayan Uncle Yousuf da yasan security ɗin gidan babu wanda zai iya shigo masa, sai ko Ahmad, maybe ya manta ne da zai fita bai kashe fitilan ba. Kayan shopping ɗin nasa ya kai duk inda ya dace sannan ya nufi bedroom ɗinsa hannunsa riƙe da jacket ɗinsa da ya zare ya ɗan sagalota a kafaɗa. Tafiya yake a hankali kamar cikin kasala da gajiya yana latsa waya da alama akwai abinda yake sonyi ko kira. Cikin rashin maida hankali ya tura ƙofar ɗakin da ƙafa ya shiga tare da sake turata da ƙafa ya rufe. Dai-dai nan take fitowa daga Bathroom sanye cikin rigar wanka pink da tazo da abinta. Sosai gabanta ya faɗi da ganin mutum ya shigo mata kai tsaye a inda batai tunanin ganin wani ba, duk da tun shigarta bathroom ɗin ta shiga halin tsarguwa amma ta dake. A bedroom komai need yake babu tarkace babu abinda aka bari a waje da zaisa ka zargin akwai mai amfani da ɗakin sai a toilet ɗin ne, sai dai wani tunani da yazo mata ya sata gamsuwa tai wankanta hankali a kwance.
        “Who are you Man?!”.
     Ta faɗa cikin faɗa da son dake razanar da tayi. Shi kansa gabansa ne ya faɗi, ya ɗago da sauri dan yasan bai bar kowa a gidansa ba shi dai, amma sai ga muryar mace a tsakkiyar kansa a cikin ɗakin barcinsa bama falo ba. A karo na biyu ƙirjinsa yay wata irin jijjiga ganin wadda bai zato ko tsammani ba, wayarsa da ke neman suɓuce masa a hannu yay saurin damƙewa, sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan gannin tayo kansa da masifa hannunta ɗauke da wani deco.. da ke ajiye a bedside drawer ɗinsa. Duk da yana a cikin yanayin ruɗani sai da ta so bashi dariya amma ya dake, yo abinda ta ɗakko ɗin ko buga masa tayi mizai ji duk da glass ne. Tana gab da zuwa ina yake ya ce, “Please Relax Ladyy”.
     Cak taja ta tsaya zuciyarta na harbawa da masifar ƙarfi dan ko'a magagin barci wannan deep voice ɗin bazata layance mata ba. Cikin rawar lips da ta murya ta furta, “Aliyu!”.
         Idanu kawai ya zuba mata ta cikin glasses ɗinsa na kusan sakanni talatin, kafin a hankali ya kai hannu yay ƙasa da mask ɗin fuskarsa tare da zare glasses ɗin. Idanun ya lumshe a hankali tare da sake buɗewa yana mai kamo gefen lips ɗinsa da haƙori. Kallon nasa da yanda gaba ɗaya ya canja fiye da ganin datai masa a lokacin haihuwar AA a Canada ya sata jin kamar jiri na neman kwasarta zuwa ƙasa ne ma. Shima yana jin fiye da abinda take ji ɗin, sai dai ƴan mazan a tsaye suke banda a ƙwayar idanunsa bata iya hango komai da zata iya bama fassara. Son tabbatar da ba aljana bace ko mafarkin da ya saba harta fara masa gizo ya sashi kauda idanunsa a kanta ya fara waige-waige. A saman gadonsa ya hango abinda yake neman a kwance yana barcinsa da alama ya gaji dan yayi wani baje-baje da ƴan kafafu da hannuwa yana zuƙar iskar sabuwar ƙasar Babansa da fesarwa cikin kwanciyar hankali. Karo na farko ya saki murmushi ganin wanda ya bari a jinjiri ya fara zama mutum, dan girman jikin AA yafi watanninsa yawa kasancewar ya ɗakko har tsawo irin na gida. Duk wanda ya kallesa yasan su ɗin jini ɗaya ne dan kamaninsa sun sake bayyana kansu matuƙa a tattare da yaron. Lulu da ke jin wani yamm-yamm kamar zata zube ƙasa a hankali ta furzar da iska mai nauyi tare da jan jikinta baya a hankali ta koma bakin gado ta zauna cikin dafe kai. Wato ta fahimci Daddy da Uncle Yousuf wayo sukai mata kenan kawai. Shiyyasa taita fama da shi su fara zuwa U.S amma ya dage su fara zuwa UK yana da abinda zaiyi mai muhimmanci. Takun sawayensa ya sata kallonsa ta gefen ido, ganin kamar inda take yayo ya sata ɗagowa sosai tana masa kallo mai kama da harara. Sai kawai ya basar ya wuceta zuwa inda yaronsa yake.........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣

........A ɓangaren Ummah tana shiga ɗakinta ta sake tsagewa da kuka, a haka ta hau neman layin Hajiya Naqiba.
      “Na shiga Uku Aminiya Abban Salim ne ya mutu?”. Cewar Hajiya Naqiba a rikice jin Umma na ɓarza kuka.
    “Ba garama mutuwar ba zan haƙura dole Aminiya. Ashe malamin nan yaudarata yake shima duk irin maƙudan kuɗin dana zube masa. Gonata ta gado fa na ɗaga na sayar na bashi kuɗin aikin nan amma ace wai duk a banza nayi, yau sai ga shegen yaron nan mai taurin ran tsiya a tsakkiya Turawa kamar zasu cinyesa dan soyayya. Wai wani ƙungiya na kwallo asinal yake ko uwarmi ne ma oho musu suka sayeshi da wani uban kuɗi da har yanzu ma zuciyata da ƙwaƙwalwa ta sun kasa haɗawa dai-dai, wai zai musu ƙwallo na shekara biyar. Shike nan na mutu Aminiya, duk wahalar da nake akan yaron nan dai abanza take cigaba da tafiya”.
        “Tofa babbar magana, wai shi Hydar ɗin ne yakai wannan matakin na shiga ƙungiyar Arsenal? Shin ko shine ma ɗazun Maheer ke ban labari cikin zumuɗi wai wani matashi Smart ɗan Kano ya zama babban gwaska a duniya, yanzu hakama yana nan gidan Alhaji Sammani wai suna kallo ko ana nunashi”.
              “Matsiyaci haihuwar asara shine. ALLAH ya tsinewa uwarsa ma bashi ba. Na tsani matar nan fiye da yanda na tsani mutuwata, duk irin wahala da kai-kawon da nake a kanta da faɗi tashi kullum abbanza suke tafiya. Narasa wace irin baƙar tambaya ke ga Hafsatu”
      “Humm Aminiya kar kice haka, kin manta nasarar da kikaci ta tsahon shekaru yaron nan ko filin ball bai iya shiga, ga tsanar da Abban Salim yay masa. Sannan a yanzu haka fa akwai asirin dake jikinsa wanda ya gagara zama da matarsa waje ɗaya....”
           “Na fara ji a raina asirin nan bai kama shegen yaron nan ba, matar tasa kawai ya kama dai kamar, kuma mayen yaƙi sakinta. Malam yana ɓoye mana ne kawai”.
     “Tunda dai har ya kama matar tasa ai ya wadatar damu. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH yanzu ma bamu makara ba. Wajen Na-zuru zamu koma tunda dama shine yay masa wancan ƙullin goron na farko, irinsa zai sake mana ko ya shiga filin ya yanke jiki ya faɗi basai muga ta ƙafafa ba. Sannan kisa ranki a inuwa, wannan maƙudan kuɗi da kikaji ba nashi bane ba, haka naji Maheer nacewa da nake masa faɗan shi miyyasa bazai zo ya koya ƙwallon ba.”
        “Kai dan ALLAH wai da gaske kike? To kudin na waye?”.
    “Ni ban sani musu ba, kamar dai yace wai ko kungiyar daya bari ne ai da kuɗin, shi za'a yanka masa nasa albashinne.”
               “Kai amma har na ɗan jin sanyi, shegiyar uwarsa sai muga ta hura hanci, ashema kuɗin na wasu ne shasha ɗan ya koma bawan turawa bata farga ba”.
     Dariya suka kwashe da shi kamar suna kusa da juma....

     Niko na ce, “Hummm!”.
Chapter 49 · 0% Book details