← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 90

Sashe 77

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

     Ƴaƴansa ne gaba ɗaya. Alh. Sulaiman da wanda suka rasu biyu mahaifiyar Lulu da Sultana ne kawai babu. Sunyi kusan zaman mintuna huɗu kafin ya fito. Bayan yakai zaune suka sake gaishe da mahaifin nasu. Da kai ya amsa musu yana gyara zama dan zuciyarsa sam babu daɗi. Sai da ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya kafin yay gyaran muryar da ta sakasu sake maida hankalinsu garesa.
       “Na taraku anan ne a dalilin abinda yay sanadin kwanciyar mahaifiyarku asibiti duk da ni har yanzu ban san minene ba shiyyasa na buƙaci ganinku mu gani tare dan zata iya yiwuwa nima na tsinta kaina a yanayin da yafi nata ma...” cikin tashin hankali da ruɗani duk suke kallonsa. Bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan wasunku sun san rikicin dake tsakanin ɗan uwanku da matansa wasu basu sani ba. A watannin da suka gabata rikicin da bamu san tushensa ba ya ɓarke a tsakanin Sulaiman da matansa su dukansu har suka wuce gida. Sai daga baya uwar ƴaƴansa ta dawo amaryar da al'amarin yafi tsamari a kanta taƙi ta koma. Na barsu ne naga iya inda abin nasu zai kai sai kuma gashi jiya ta samemu anan gida. Flash drive ta kawo mana ta tace shine sanadin rikicin nasu. Da ga haka batai mana wani ƙarin bayani ba ta tafi. Bayan wucewartan ne mahaifiyarku tazo ta ɗauki Flash ɗin ta wuce da shi sai mai aikinta ta isarmin da saƙon gata can ta faɗi babu rai. Duk abinda zai saka mahaifiyarku a wannan mummunan yanayin bazai kasance mai sauƙi ba. Shiyyasa tun jiya na kasa dubawa ni kaɗai na zaɓi mu duba tare da ku”. Ya ƙare maganar yana jawo tab ɗin Dada da har yanzu flash ɗin ke a jiki. kusa da shi duk yay musu nunin su dawo. Haka suka zauna wasu kusa da shi a ƙasa wasu a kujera. Babu wanda zuciyarsa bata kaɗa ba a lokacin da fuskar marigayiya Mawaddat ta bayyana. Kafin sukai karshen videon babu wanda jikinsa baya rawa a cikinsu, ga hawaye duk ya cika musu idanu. Auta da yafi kowa shaƙuwa da Sultana a gidan baima san sanda ya fashe da kuka ba tamkar ƙaramin yaro. Kasa jurewa Baba Garko yayi ya miƙe jikinsa na karkarwa. Sai dai dole sukai saurin riƙosa saboda hajijiya dake neman zubar da shi a ƙasa, shima sai kawai ya fashe da kuka. Kukan mahaifin nasu ya sake tayar musu da hankali. Suma duk suka fara sharar hawaye..........✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO
Billyn Abdul

-ZAFIN KAI
Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo

Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400

Pay at👇

1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇

09032345899

Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣
Chapter 77 · 0% Book details