← Book details Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 90

Sashe 7

Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

........Basuyi mata allurar zubda cikin ba kamar yanda Alh. Sulaiman da Dada suka bada umarni har Lulu ta farka, an gama dai duk wani shirye-shirye har Dada ta saka hannu. A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi sosai tana bin ɗakin da kallo, sai da hankalinta ya gama dawowa jikinta sannan ta fahimci a asibiti take. Yunƙurawa tai da niyyar tashi sai hakan yay dai-dai da shigowar Dada ɗakin. “Sunahanallahi Mawaddat kin tashi?” cewar Dada tana nufota. Ita ta taimaka mata ta ƙarasa tashi, tare da kaiwa zaune a kusa da ita. Hakan ya bama Lulu damar kwantar da kanta a jikin Dadan tana hawaye. “Yaushe kika zo?”. Ta tambaya cikin raunin murya irin ta mara lafiya. Cike da kulawa Dada ta sake rungumeta a jikinta da faɗin, “Tun ɗazun dear. Ya kike jin jikin naki yanzu haka?”.
      “Dada ko ina namun ciwo, ga yunwa ina ji sosai”.
     “Ba dole kiji yunwa ba kina ɗauke da jinin yunwa. Shegen yaro da bai wuce saiti abu yi guda ya ɗiraka miki ƙunshi ya barki da jidali”.
    Da mamaki Lulu ta ɗago ta dubi Dada saboda rasa gane ina zantukanta suka nufa. Dada ta ƙyaɓe baki cikin hasala tana yin ƙwafa. “Dada wai mi kike faɗi ne?”.
           “Mtsoww ba komai tashi muje na kaiki ki wanke baki kizo kici abincin”. Duk da Lulu na son jin fassaran zantukan na Dada sai batai musu ba ta tashi a jikin nata, da taimakonta ta wanko bakinta da fuskarta suka dawo. Apple da tace tana so ta bata ta sha, takai kusan rabi ta ajiye ta ce ta bata yugut. Shi tasha sosai dan kaɗan ta rage a babbar robar da yake ciki. Sosai Dada ta saki baki tana kallon Lulun kamar wadda ke'a cikin yunwa. Ɗan gumin da ya tsatstsafo mata na ƙoshi ta kai hannu ta share tare da komawa jikin Dada ta lafe. Shigowar Dr Olivia ya sakata miƙewa zaune. Sannu Dr Olivia ke mata cikin fara'a da jin daɗin ganin ta tashi da daɗin rai, bayan ta ɗan tsokanarta ta ciro allurar da zatai mata. Lulu bata wani damu ba, dan ta ɗauka normal allura ce, dan haka babu musu ta yarda akai mata doctor na cigaba da tsokanarta.
          Minti talatin dai-dai dayin allurar nan wani irin ciwon mara na azaba ya tasoma Lulu. A take jikinta ya fara vibration, tai wani irin dunƙulewa waje guda tana kiran “Wayyo ALLAH na Dada marata”. Yanda ta saki siririyar ƙararar sai da zuciyar Dada ta harba, hankali tashe tai amfani da wayar landline dake a ɗakin tai kiran doctor Olivia. Tamkar dama a kusa take babu jimawa sai gata ta faɗo, zuwa sannan jini ya ɓalena Lulu abin babu daɗin gani....

      Iya wahala da azaba Lulu ta Shashi, inda da ƙyar aka samu jinin ya tsaya, akai mata allurar barci tare da gyarata, barcin wahala ne ya ɗauketa sai wata irin tagwayen ajiyar zuciya take saukewa a cikin barcin. Dada da duk ta shiga damuwa ta shiga tambayar doctor yanda ake ciki, Doctor ta tabbatar mata da aiki yayi ƙyau, dan yanzu haka dai ciki ya fita sai kuma ɗan jiyyar jiki da Lulun zatai na kwana biyu. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyin gaske Dada ta sauke, a take tai kiran Alh. Sulaiman, a lokacin yana tare da su Hon. Misau suna tattauna batun Daddy. Kamar yaƙi ɗauka sai kuma dai ya ɗaga yana kaiwa kunne. A ɗan daƙile ya ce, “Dada nafa sanar miki inada uziri, mi kuma ya faru yanzun?”.
         A ɗan ɗokance da ture maganarsa ta farko Dada ta ce, “Ai an kammala aiki yanzu haka ciki yabi gottern turawa kuma”. Ajiyar zuciya Alh. Sulaiman yayi da faɗin, “To maddala, na san zasu sallameku yau ku koma gida, zuwa anjima idan na samu nutsuwa zan kiraki”. Daga haka ya yanke wayar batare da ya jira tace wani abu ba. Hakan ya bama Dada haushi dan bata gama maganarta ba, amma sai batace komai ba bayan jan tsoki. Kamar yanda ya faɗa zuwa dare da Lulu ta sake farkawa aka sallamesu. Duk da Lulu najin jikinta cikin rashin ƙarfi kwata-kwata ga jiri na ɗinarta bata kawo komai a ranta ba. An basu magunguna suka hau cab zuwa gida. Sun samu Ummita ta gama gyara ko'ina sai tashin fresheners masu ƙamshi da gidan keyi, cikin ƙarfin hali Lulu ta ce ma Dada tana son tai wanka first, amma ta taimaka mata. Dada da kanta ta cuccuɗa Lulu tare da taimaka mata suka fito, kaya ma da taimakonta ta saka, tana gama sawa tasha tea ɗin da mai aikinta Ummita ta haɗa mata bisa umarnin Dada. Sosai ta sha shayin har ma abin yaso bama Dada mamaki, ita dai cikin sauke numfashi ta koma ta kwanta dan barci takeji har yanzun.

       *_BAYAN KWANA UKU_*
Chapter 7 · 0% Book details