Sashe 61
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
★ Zaune suke a wajen cin abinci yana cin abincin da tai masan idanunsa a lumshe alamar dai yana jin daɗin sa, itako sai murmushin farin ciki takeyi. Dan a yanzu babu abinda ke sakata a farin ciki sama data gansa cikin farin ciki. Batai zaton zaici abincin haka da yawa ba, sai gashi ko yaci sosai har yana faɗin jikinsa yay masa nauyi. Bayan ya kammala ta gyara wajen suka koma falo. Zama yay yana wasa da AA ita kuma ta kwashe kayan da ya shigo da su zuwa ciki, na kitchen kuma takai kitchen. Sosai taji farin cikin ganin kayan sakawa ne ya siya mata, sai turarruka na mata masu daɗin ƙamshi duk da tazo da su khumra da turarrukanta abinta. Sai kayan kwalliya da batazo da su ba, shima AA an saya masa nasa. Tana cikin kwashe kayan taci karo da camara. Tsai tai tana kallo da jujjuyata a hannu, sai kuma ta ajiye cikin taɓe baki ta cigaba da gyara kayan. Sai da ta kammala tsaff ta ɗauka camara ɗin ta koma falo da ita. Kwance yake a ƙasan carpet yana waya da Ahmad, AA na gefensa yana wasa da kayan wasansa, yanda ya nutsu sosai ya tabbatar mata da magana suke mai muhimmanci, dan haka ta kai zaune Camara ɗin a hannunta tana kallonsa shi da AA ɗin cike da jin farin cikin su ɗin duk nata ne fa. Abinda ya ɗan fara jan hankalinta ga wayar tasa shine kalmar daya ambata cikin yanayin ɗan ƙaraji har yana tashi zaune. Sosai ta zuba masa idanu, yayinda shi kuma ya cigaba da faɗin, “Kaga Ahmad relax please. Karka ruɗar da kanka, ni dama nasan dolene wannan binciken ya tono mutane da yawa a ciki, aiba abin mamaki bane ba hakan karma ka tada hankalinka a banza. Yanzu abinda zamuyi shine dole mu tafi mataki na biyu, wato plan B.”
Cikin matsanancin ruɗani da ga can Ahmad ya ce, “Dole ne hankalina ya tashi Aliyu. Mahaifin aunty Khadijah fa! Kasan kuwa yanda nake ganin mutunci da kimar mutumin nan, amma ace har da shi a cikin mutanen nan. Kasan kuwa irin muggan miyagun kwayoyin da yaron nan ya sanar min ana saidawa a pharmacy ɗin nan! Ban taɓa sanin haka ƙasar nan tamu ta lalace da rashin doka da bin ƙa'ida ba sai yau. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”.
“Humm Ahmad kenan kana wasa da mutanenmu. Abinda yasa kake ganin irin waɗan nan abubuwan abin mamaki saboda rayuwar daka tashi ne. Amma mu da aka haifa a getto eria muka rayu a ciki munsan irin waɗan nan abubuwan fiye da yanda kake zato, kawai dai mutum dan baida ƙarfin ɗaukar matakine shiyyasa. Ni dai abinda nake so da kai yanzu dolene fa ka sake ƙara ɓoye kanka, dan ko Yaya Hameed da Uncle Yousuf ban san susan da hannunka a ciki, shiyyasa ma kaga nace Uncle Yousuf ɗin yabar komai a hannuna shima saboda suma suna huɗɗa da mafi yawan manyan ƙasar, zamu iya zuwa gaɓar da al'amarin wani zai girgizasu su buɗe mana aiki”.
“Hakane Smart na fahimceka yanzu, kuma in sha ALLAHU zamu basu mamaki, tabbas mune matasa ya dace muyi hanƙoran gyara ƙasar nan tamu akan wannan mummunar safarar dake cigaba da yaɗuwar gurɓatamu tamkar wutar jeji a kasarmu, in ba haka ba sai anzo lokacin da babu wani matashi da zai iya amfanar kansa balle wani ko ƙasar, zasu cigaba da mana illa ta hanyar dafe madafin iko su barmu da raɗaɗin shan miyagun ƙwayoyin da suke mana safara mu kuma muna sha da tunanin rage raɗaɗi, wlhy Smart naji na tsanesu, natsanesu, su azzalumai ne.....” Kukan da ya tahoma Ahmad ya hanashi ƙarasawa, shiru kawai Smart yay yana saurarensa shima zuciyarsa na ƙuna. Tuni idanunsa sun gashe zuwa jajur. Yana jin raɗaɗi fiye da wanda Ahmad yake ji, tun yana yaronsa ya tsani shaye-shaye, baya son yaga anayi, yana jin ciwo matuƙa idan yaga matashi ya lalata rayuwarsa da shaye-shaye, shiyyasa cikin ƙanƙanin lokaci al'amarin Lulu yay tasiri a zuciyarsa. Da ƙyar ya iya furta, “It's okay Ahmad. Kuka bashi ne magani ba, aiki tuƙuru domin ganin mun karya su. Sannan inaga dolene zamuyi amfani da ƙungiyar Mawaddat a wannan gaɓar domin tattarro hankalin matasa dan wannan aikin yana son taron dangi ne. In ba hakaba zaƙulosu da muka ɗauka ɗammarar yi bazai magance mana matsalar ba tunda zasu iya sayen hukumomi da kuɗi kasancewar wasu a cikinsu suma ruɓaɓɓune”.
“Tabbas haka ne nima nayi wannan tunani, kuma na yarda da shawarar nan naka. Sai dai yanzu ban san yaya zamuyi ba tunda kaga ita tana nan”.
Cikin ɗan ɓata fuska da kallon Lulu ta gefen ido ya ce,,......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣