Sashe 15
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wani irin rikicewa da daburcewa Dr Olivia tai lokacin data juyo sukai ido huɗu da Lulu da bata san tana bayanta ba. A yanda taga Lulun kuma ya tabbatar mata taji wayar da tai da Dada. Cikin harshen turanci take ma Lulu magana harshenta na sarƙewa. Hannu Lulu ta ɗaga mata kawai alamar bata son jin komai, daga haka ta bar wajen cikin tangaɗin hajijiyar da take ji na kwasarta. Amma koda ta fito sai ta sauya yanayinta saboda bodyguard ɗin da Alh. Sulaiman yasa suke biye da su. Magana taima Ummita akan tazo ta rakata restroom. Ganin ɗaya daga cikin b.g ɗin na ƙoƙarin biyosu ta kallesa sheƙeƙe da faɗin “Can ɗin ma sai ka bimu. Ko an faɗa maka ma na gama abinda nake a asibitin!”. Tsayawa yay kansa a ƙasa dan ya fahimci masifar Lulu tafi tashi.
Tsaki taja da sake ɓalla masa harara sannan taja hannun Ummita. Ba restroom ɗin suka shiga ba, da ga can gefensa suka tsaya, karo na farko a rayuwar Lulu da taji ya cancanta ta sanarma wani damuwarta, dan zurfin ciki babbar ɗabi'arta ce shiyyasa abubuwa da yawa sukai mata nauyi a zuciya.
“Ummita so nake na gudu”.
“Sosai Ummita ta waro idanu waje, sai kuma ta kalla inda Bodyguard ɗin nan da Lulu bata lura ya dai biyosun ba a laɓe, ƙasa Ummita takai kamar mai son gyarama Lulu takalmi, dan Ummita wayayyar mace ce da taga jiya taga yau, hasalima tashin ƙauye ce ita, daga baya ta dawo wajen yayarta a cikin Kano, sai dai matsalar data fuskanta ya sata komawa Abuja a yanzu.. “Aunty karki ruɗar da kanki dan munafukin nan ya biyo mu. Muyi tamkar takalmin nake gyara miki”. Lulu ta fahimceta dan haka hankalinta ya sake tashi. Amma sai Ummita ta ce, “Karki tada hankalinki zamu samu mafita. Aunty tsakanina da ALLAH nake jin ƙaunarki a cikin raina, saboda kin min abinda bazan taɓa yarda a cutar dake ba. Nima halin da kike a cikin gidan nan na tada min hankali. Na kasa tunkararki da batunne saboda ina jin tsoron karki kasa fahimta ta. Sannan ke kanki kin kasa gane tamkar anyi kidnapping ɗinki ne anzo an ajiye anan. Dan gaskiya akwai manufa a al'amarin kawun nan naki a yanda nake lure da shi, na fahimci hakanne tun sanda aka zubar miki da ciki da ɗauke passport ɗin mu da yayi”.
Lulu dake jin hawaye da wata matsananciyar tsanar Alh. Sulaiman ta cika mata zuciya ta ce, “Nima na fara jin haka a raina Ummita, sai dai gani nake mizaisa Dada a matsayinta na grandma ɗina ta aikata hakan, shiyyasa kawai nake hora zuciyata da ƙin yarda. Amma a yau zuciyata ta kasa karɓar al'amarin, cikin da suka zubar ashe bai fita ba”.
Da sauri Ummita ta ɗago tana kallonta. Lulu ta gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, “Yana nan Ummita, kuma wlhy naji ina matuƙar son sa. Idan har kakata nada manufa a kaina itada Uncles ɗina dama family ɗina duka ashe bani da babban abinda ya kamata na runguma sama da wannan cikin, yafi kowa kusanci dani a yanzu, banda uwa, banda ƙani, banda yaya. Daddy na da Uncle Yousuf sun fifita soyayyar wani a sama da tawa. Wlhy a yanzu-yanzu Ummita naji ƙauna da soyayyar abinda ke cikina harda zumuɗi da fatan zuwansa duniya lafiya, a wannan karon bazan bari su taɓamin shi ba, ina son na rayu da shi, bana son na rasashi ko shi ya rasani kamar yanda na rasa mahaifiyata”. Sosai Ummita taji itama hawaye na cika mata ido. Miƙewa tai tana murmushin yaƙe dan har yanzu munafukin na laɓe, sai dai bazai iya jin abinda suke faɗa ba. Hanya ta nunama Lulu alamar su koma tana ɗan murmushin yaƙe. “Muje restroom ɗin karsu fahimci wani abu, ina son ki kwantar da hankalinki ko'a fuska kada ki nuna musu kina son cikin balle yunƙurin guduwa. Na miki alƙawarin kozan rasa raina zan taimakeki. Dan nima kin min abinda bazan taɓa mantawaba, wanda shine dalilin amsar wannan aikin da nayi a lokacin da na ganki cewar kece wadda zan zauna da ita anan”. Sosai Lulu kema Ummita kallon mamaki, amma sai Ummitan tai mata murmushi kawai. Restroom ɗin suka shiga, Lulu ma sai tai fitsari sannan suka fito. Ganin sun nufo hanyar dawowa bodyguard ɗin nan yay saurin yin baya yana sanarma Alh. Sulaiman cewar gasu nan zasu dawo da gaske restroom ɗin suka shiga. Sarai Ummita taga waya a kunnesa, hakan ya sata sake gaskata zarginta. Sun koma wajen Dr Olivia wadda suka sameta tana waya da Dada. Dan haka Lulu ta laɓe tana saurarenta. Dr Olivia da bata lura da Lulun ba ita cikin harshen turanci ta cigaba da faɗin, “Idan akace sai an fidda cikin nan a wannan gaɓar akwai babbar matsala, dan za'a iya taɓa lafiyar ta ɓangarori da dama, koma a rasata baki ɗaya. Kawai Mrs Garko kuyi haƙuri ta haifi abinta. Amma dai har na mutu bazan daina mamaki da al'ajab ɗin wannan al'amarin ba, harma na sakashi a cikin manyan record namu na ban mamaki da suka faru a asibitin nan. Sannan zanyi bincike mai ƙarfi akai dan tabbatar da daga ina aka samu matsalar”.
Shiru alamar tana sauraren Dada itama, sai kuma ta nisa da cewa, “Shike nan sai kin shigo ɗin”. Daga haka ta yanke wayar. Haɗiyar zuciya Lulu ta dingayi cikin wani yanayi, kafin ta saita kanta da ƙyar ta nufi cikin office ɗin. Murmushin da Dr Olivia ta gani a fuskar Lulu ya ɗan sata jin relief, ta rubuta mata magunguna da abubuwan da ya kamata taci dan inganta lafiyarta data abinda ke cikinta. Lulu tai mata godiya ta fito akan zata cigaba da zuwa awo. Koda suka fito a asibitin sai da suka tsaya sukai ɗan shopping sannan suka wuce gida. Sun samu Tajuddeen yazo, amma kamar yanda Lulun ta saba kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta tare da wucewarta ɗaki tana amsa masa gaisuwar da yake mata a taƙaice. Tajuddeen da yake jin kamar ya fasa kuka ya sauke numfashi mai nauyi tare da dafe saitin zuciyarsa dake harbawa da sauri-sauri, da gasken gaske yake ƙaunar Lulu, soyayya yake mata mai zafi wadda shi kansa wani lokaci yana jin abun na neman fin ƙarfinsa. Bai taɓa jin koda ɗigon sonta ya ragu masa a rai ba duk da cin kashin da take masa. Hasali ma duk abinda tayi sai ya zama shi birgeshi take yi tare da ƙara jin sonta a ransa. Burinsa ya mallaketa matsayin matar aure, ta zama uwar ƴaƴansa, randa yaji ta ɗauki cikin wani ba nasa ba har hawaye yayi, dan ƙarshe ma sai da ya ga likitansa.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣2️⃣
.........*_LONDON_*