Sashe 45
Furar Danƙo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana tsaka da wannan dambarwa aka dawo da Dada gida Nigeria. Alhamdullah ta samu sauƙi sosai kamar ba itace aka fita da ita ƙasar raga-raga ba. Sai dai ta dawo ƙasarta da tagwayen al'amura biyu masu gogayya da juna zuwa uku. Na farko shine anga Lulu, sai dai tana baƙin ciki da haihuwarta da ɗan talakan nan dai, amma dai bata yarda ta furta ba gudun karta sake ƙullama kanta tsiya ga Baba Garko da tun a sibiti ƴaƴan keta faman kiransa suna bashi haƙuri ya maidata iddarta saura kwanaki ta cika amma yay biris da su. Abu na biyu shine fitowar Tajuddeen da kama Sulaiman kuma. Wannan al'amari ya sake ɗaga mata hankali. Ta kuma sake tabbatar da Baba Garko a shirye yake da kowa kenan, dan haka ta ƙara kama kanta.
Da ƙyar ta iya bari gari ya waye tasa Uncle Muneer ya kaita gidan su Lulu. Karo na biyu kenan da zata taka Jiƙamshi House a tsohon rayuwarta. Da ga lokacin rasuwar mahaifiyar Lulu sai yau saboda tsabar ƙiyayyar da takema Daddy a baya, koda yake har yanzu ma bawai ta barsa bane, kawai tana dannewa ne saboda Lulu ta nuna mata bazata ɗauki wannan ba ana zagar mata mahaifi. Duk da kasancewar gidane ginanne a tsaye, a kuma anguwar data amsa sunanta anguwa dan kosu da ke a kusa da gidan gwamna sun san a yanzu hotoro G.R.A ɗin ta basu baya. Amma haka tsohuwar nan ta dinga wani yamutse-yamutsen fuska har abin ya bama Uncle Muneer haushi da tabbatar da Dada fa bazata taɓa ta canja ba sai dai a barta da halinta kawai dan ya riga ya shiga jininta ne. Sun sami tarba tautuntawa da ga Daddy da Mommy. Duk da dai Dada na amsa musu gaisuwa sama-sama basu damu ba. Uncle Muneer ne dai ya ware abinsa sunata shan hira da Daddy cikin mutunta juna kamar yanda suka saba. A haka su Amrah dake maƙale da AA akoda yaushe yanzu, ko makaranta sai anyi jan ido suke wucewa suka fito. Yana goye ne a bayan Afrah yana barci, yayinda Amrah ke jiran time ya cika ta kunto mashi dan dole aka koma sakama kowa lokaci har su Naseer da ake korawa makaranta da ƙyar. Dan yau Suhaib harda kukansa shi sai da AA zai tafi kamar wani ƙaramin yaro. Basu ba dake ƙanana hatta Mubeen wataran faɗa ake da shi akan ɗaukar AA. Hakan na saka Lulu farin ciki da jin ƙaunar ƴan ƙannen nata matuƙa. Su twins kansu kullum sukan kirata sama da sau uku suna tambayar ina son ɗinsu. Hotunansa kam ƙa'ida akai masa wanka sai an tura musu. Ra'is da Deen kam ai sun ma dawo nan gidan saboda AA. Mommy kanta na ƙoƙarin gyara kuskuranta akan AA ɗin, dan itace a tsaye kan kula da Lulu da yaronta duk da Iya Tabawa na iya ƙoƙarinta. Dan ana cewa za'a samo tsohuwar da zata kula da Lulu ta ce ita dai a bata dama ta maida alkairi a wannan karon. Duk da dai a tsorace take saboda sanin halin Lulu ɗin. Amma dai ganin kamar ta ɗanyi sauƙi yanzu yasata cewa a bata dama. Bako a samu wata matsalaba kasancewar a yanzu ma ga Ummita kuma, sannan da gaske al'amuran Lulun sunyi sauƙi kam, duk da idan ƴan masifar na kusa takanyi abinta.........✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣
.......Alhmdllh sosai jego yayma Lulu ƙyau, ga Iya Tabawa na mata wani sirrintaccen gyara irin na mutanen da cikakke da ke zama a jikin mace duk da bada kanta ta haihu ba. Gefe kuma Aunty Saliha ta sake kawo wanda sukai mata gyaran aure na nasu suma yanzu. Mommy ma na nata ƙoƙarin. Sai ruwan addu'oi wajen Malam na Yakasai da ake amsowa Lulu na tsarin jikin da yanayin da take ciki game da Smart. Wannan ƙoƙarin Ammah ne da Abbah. Dan ita kanta Ammah kan zauna da kanta tai mata addu'oi a cikin ruwa da ma ruwan zam-zam shima AA ana bashi.
Sai Daddy da ya kawo mata malama har gida tana ɗora mata karatun addini saboda Ummita zataje ganin gida itama. Da yake Lulu tasa abun a ranta hatta Mubeen zaunarwa take ko su Amrah su ƙara mata karatun. Gefe guda kuma tana ta ciku-cikun yima ƙungiyarta rigester shima da taimakon Daddy da Uncle Khamil na Abuja da shima ya bata goyon baya. Koda wasa bata son tuna Smart, dan ko AA ta kalla babansa yazo mata a rai kanta ya dinga wani irin masifar ciwo kenan dake tayarma kowa na gidan hankali. Inda aka yankata Alhmdllh yana sake warkewa, Aunty Khadijah matar Coach ce ke zuwa dubata kullum babu fashi, idan abinda ya kama taje asibiti ne kuma sai ta shirya Mubeen ya kaita suje suga likitan su dawo. Da Ummita zata wuce shatara ta arziƙi Daddy ya haɗa mata, itama Lulun ba'a barta a baya ba, Uncle Khamil ne da yazo ya wuce da ita duk da dai jirgi sukabi zuwa Abuja tare, dan Lulu ta gargaɗeta zuwa ɓagwai saboda gudun mutanen Alh. Sulaiman kar su cutar da ita ko iyayyenta.
★A ɓangaren Ammah tsaye take wajen kaima UBANGIJI kukanta akan dai-daituwar zaman waɗan nan ma'auta. Tare da yawaita sadaka da azumi. Yaranta kaf basu zauna ba har ƴan uwanta kasancewar suna da haɗin kai. Yayinda itama Ummah ta kasa zaune ya kasa tsaye wajen sake lafto sabbin asirai kala da iri akan Ammah da Smart kai harma su Aunty Amaryar ba bari tayi ba. Dan a kwanakin nan da ƙyar suka samo kan Abba da aka nema juyarma da kai. Sai Alhmdllh al'amarin baiyi nisa ba ya sake shi, hakan ya tada hankalin Ummah kam sosai, dan ba ƙananun kuɗi ta kashe a aikin da akaima Abban ba, amma sai gashi ya tafi a banza cikin ƴan kwanaki ƙalilan....
*_UK LONDON_*
Hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk abinda UBANGIJI ya ƙaddara shi a matsayin naka babu wani mahaluki a duniya da ya isa canja wannan ƙaddarar. Dan kuwa a lokacin da Ummah ke can tana faɗi tashi akan abinda bata iya jayayya da shi ba anan ƙasar England ƙaramin labari ne ke neman canja kansa akan Aliyu Mika'il Idris Mawashi, wato Smart Mawashi zuwa babban gaske gagarumi. Dan fa manyan clubs da ke zawarcinsa ta ƙarƙashin ƙasa sun fara bayyana kansu a fili yanzu. Wannan yasa aketa faman kai kawo da dambarwa tun barowarsu Canada shi da Manager ɗinsa Uncle Yousuf. Sosai ake ta kai ruwa rana da bata kashi a tsakanin Coach's ɗin mayan clubs ɗin. Shi dai Smart ya duƙufa gayama UBANGIJI da neman zaɓinsa. Dan bashi da wani zaɓi sai nashi. Yayi alƙawarin duk inda ya tsinta kansa zaiyi aiki tuƙuru in sha ALLAHU duk da a cikin zuciyarsa yana da club ɗin da yafi so da ƙauna kuma gashi a cikin masu zawarcin nasa. Amma sai bai Zafafa ba ya bar ma UBANGIJI komai sai su Uncle Yousuf da keta kaiwa da komowa shi da Coach ɗinsu na Queen City da duk manyan masu faɗa ajin club ɗin.
Sosai mahawara ta ɗauki zafi a tsakanin manyan clubs guda uku da suka riƙe wuta fiye da sauran, dan kowa ya gagara janyema kowa. Sannan duk sun zuba manyan kuɗaɗe akan Smart ɗin masu girgiza zuciya. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta sake zama babba. Dan manyan gidan jaridu na duniya musamman a fanin ƙwallon ƙafa sunyi ƙur da idanunsu akan wannan batu domin ganin wazai ɗauki wannan lu'u-lu'un a cikin juji. An buga an turza an kai matuƙar kai ruwa rana kowa yaƙi sakarma ɗan uwansa, dole aka tafi mataki na biyu wato jin ra'ayin Smart game da wane team yafi sha'awa shi a ransa. Tun farko Smart nada ra'ayinsa dama, amma ya zaɓi barma UBANGIJI zaɓinsa. Har a yau da aka kai wannan matakin na jin ra'ayinsa bai ji zuciyarsa ta canja da ga abinda ta ke so ba tun yana da ƙuruciya. Dan haka bai wani basu wahala ba ya faɗa musu zaɓinsa wato *_ARSENAL FC_*. hankalin sauran clubs biyun da sukai gogayya da Arsenal ɗin ya ɗaga, a take suka ƙara kuɗi akan wanda suka saka a farko, amma dai Smart nakan bakansa Arsenal ɗin dai, dole suka haƙura dan aikin gama ya gama Arsenal tayi nasarar siyensa da kuɗi kimanin dala Miliyan arba'in.
Duk wani masoyin Smart a wannan rana yana a cikin matuƙar farin ciki mara misali, Ammah duk dauriyarta sai da tai hawaye lokacin da Uncle Yousuf yay kiransu yake sanar musu al'amari fa ya kai girman da aka daɗe ana fata. Sai kuma addu'ar cigaba da samun nasarori ga Smart ɗin. Amma wannan tsanin kam an haye sama ƙololuwa.
Sun ɗanyi zaman meeting meeting da ƴan cike-cike na tsarabe-tsaraben da aka san ƙwallo da shi su da Manager ɗin sa Uncle Yousuf da shi kansa Smart ɗin. Kafin dai a ƙarƙare ya saka hannu a ƙarshe. Da ga haka akaje matakin duba lafiyarsa ciki da bai. Alhamdullah nan ma normal an samesa da cikakkiyar lafiyar jiki dama ta sassan jiki. Bayan kammala waɗan nan ya ziyarci Arsenal camp domin yin hotuna da gabatar da shi ga teammate ɗinsa. Ya samu tarba fiye da yanda yay zato da tsammani ga teammate ɗinsa. Dan tunda suka shiga cikin camp ɗin bakinsa bai bar ambaton ALLAH ba. Kwarjininsa da hasken musulunci ya sake ƙawatashi a garesu da girmama mutuncinsa. Sunyi hotuna da duk abinda ya dace a wannan ranar kafin a wuce mataki na gaba. Wato gabatar da Smart Mawashi ga fans.