← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi ce ta kalki Azzahra tace"yaya dareib ne yayi accident yanzu aka kirani ana sanar dani, kuma bata karasa ba gaba daya suka saka kuka, ummi ce tace"ni bansan ina suka kaisa ba, amma bara na kira daddy na fada masa, domin nasan bai sabi ba, ba tare da wata shawara ba ta fara dialing numbern daddy.

Cikin kasurgumin daji suka kutsa, sun danyi tafiya ba mai nisa ba, suka hangi wani katon rami, nana ce ta karaso ta fara shigowa, da mamaki sahura tace"wai nana kina nufun cikin wannan ramin zamu shiga, da sauri tai mata alama da yatsa akan tai shiry.

Tafiya suka yi bada yawa ba, sannan suka shiga wata murya ce ta fara magana"LALE DA ZUWANKU YA KE NANA DA KE DA KAWARKI SAHURA, LALLE KUNZO INDA BUQATAR KU ZATA BIYA, sai kuma wata dariya ta biyo bayan maganar.

Wani hayaki ne ya bayyana take suka gansu a gaban wani shirgegen mutum, gaba daya kuma ba riga a jikinsa, jikinsa dik gashi, fuskarsa ce kadai ba gashi.

Nan ya fara karanto musu wasu damasumai, sai kuma ya dago yace"kunzo ne domin ke sahura kinaso a kori yarinya kuma kinaso dareib da danuwansa su tozarta,karki damu kinzo inda buqatarki zata biya, domin tin kafin ma ki karaso na fara aijata miki aikin da kike nufun ai miki.

Cikin tsawa yace"leki nan da sauri kuwa ta leka saboda muryar yadda ta karade wajen, dareib ne kwance cikin jini mutane sun kewaye sa,motar ambulance ce ta karaso aka saka shi sai asibiti.

Dariya sahura tayi tace"wannan abu yayi mini matuka, sannan sai batun yarinyar, shafa kasa yayi sannan ya dago yace"aikinki zai yiwu amma fa akwai matsala, sahura ce tace"ni bana tsoron dik wata matsala kawai aiki ya biya.

Bokan ne yace"me kikeso ai mata sahura, sahura ce ta kalli nana tace"kawata ki bani shawara, nana ce ta kalli bokan tace"boka a mantar da ita wacece ita, sannan kuma ai mata kurciya ta bar garin nan kwata kwata karta kara dawowa har abada.

Sahura ce tace"shi kuma alhaji a cire masa kaunar yaransa guda 2,sannan kuma ya daina kulawa dasu dukiyar hannunsu a kwace a bawa yarana, domin suci gaba da kulawa da su, kuma a batar min dasu, nan fa jikin boka ya fara tsuma, cikin wata shakakkiyar murya yace"bazan iya aikata komai akan wadandanan yaran ba, domin kuwa suna da tsari a jikinsu, zan miki dai aikin fateemah da haka ki ajiye kudi ki tashi ki bani waje, ajiye sukai sannan suka fito da sauri.

Nana ce tace"ke sahura tinda haka ne kawai ke kiyi maganinsu da kanki, zan baki shawara da zata miki aiki shikuma yanzu tinda wancan rai a hannun allah ba dole ya dawo gida ba, kinga nan ma kin samu kafar da zaki yi musu wani tuggun Motar su suka hau duka dakko hanyar gida.

Fitowa sukayi azzahra na zaune tana jiran ummi ta fito daga dakin domin taje dakko hijabi, jin kirjinta yayi nauyi, idanunta sun dauki rawa, kwakwalwar ta kamar ta tarwatse, tashi tayi ta fara ta tafiya,har tazo bakin gate ganin ba kowa a wajen yasata saka kafa ta bar gidan, titin gidan ta hau ta fara tafiya.

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
The Stars
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
23&24
Da sauri daddy ya fito daga wani katafaren gida, gaba daya hankalinsa yana kan driver, cikin daga murya yace"Yi sauri muje Zooon private hospital, basu waninbata lokaci ba suka fice daga gidan.

Tafiya suke daga waya yayi yace"gani nan ina zuwa, kuyi komai ya dace, tafiya suke basu dade ba suka iso bakin hospital din, gaba daya ba kowa daga ummi sai baba daddy ne ya tsaya yana kallon su yace"ina doctorn, a hankali ummi tana share hawaye tace"daddy suna ciki tin dazu basu fito ba.

Baffa ne 'Hashimu karka zama kamar ita mana, tin da ta shigo asibitin nan take faman kuka, na kasa samun hanyar ma da zan tambayeta ina ta baro abokiyar zaman nata, wato sajida sai a lokacin taa tina da wata azzahra, daddy ne ya bar zancen, domin.

Haka kawai bayaso a tado masa da zancen wannan yarinyar.

Sahura gida tayi anan ta fara tarar da sabra, tsayawa tayi ganin ta kire kida sai rawa takeyi, da mamaki sahura tace to dik ina mutanen gidan,safina ce ta fito cikin shiri, da mamaki sahura tace"ke safina ina zaki dik in amutanen gidan naji gidan shiru.

Karar kidan ta tsayar tace"mama yaya dareib ne yanzu yayi accident to gaba daya gidan kowa yana asibitin, shi ne ita kuma sabra ta Kure kida wai party take, dan kar ma ya tas...

Maganar ce ta makalar da ita sakamakon tozalin da idanunta sukayi dana wani hadadden gaye wanda ya gaji da haduwa.

Sanye yake da riga da wando black ne dika, sunyi matukar amsar jikinsa, sai takalmi black, sumar kansa tasha gyara, kallo daya na masa naga kamarsu da dareib, sahira ce ta katse shirun da fadin "naji kuma kinyi shiru idan ya mutu ubanwa yayi asara, ke sabra cigaba da partynki domin insha allah ma bazai tashi ba.

Gani nai ya taho cikin wani irin salo na tafiya jin kamshin Turaren sa yasaka kowa juywa, safina ce zata ruga cikin wata daddadar murya cikin harshen turanci yace"karki kuskura ki motsa ko nan da can idan ba haka ba, ya nuna ta da yatsa.

Damkar gashin kan sabra yayi ba ita ba hatta sahura surender tayi domin tasan tinda ya shigo gidan nan dole sai ta kara mikewa tsaye, janta ya farayi ganin haka yasa sahura tsayar dashi tace"kai...

Makalewa maganar tayi sakamakon kallon daya wurga mata, cikin kunar rai yace"karki kuskura ki karasa, daki ya wullata bansan me ke faruwa ba, amma tin tana kuka da karafi har ya dawo bakyajin kukanta.

Cikin tsawa yace"sai kije kici gaba da party shashashar yarinya kawai, fitowa yayi yana kallon safina yace"wane hospital aka kai dareib, cikin inda
tace"Zooon private hospital, bai jira karasawarta ba ya huce, sai kuma ya jiyo yace"ku dauke ta ku kaita asibiti, kuma kar wanda ya sake ya kawo ta zooon tinda naga ba gadonku a cikin hospital din ko.

Zo kaga takaici wajen sahura domin ji tayi kamar ta fasa ihu, dakin da sabra ta ke ta shiga anan ta ganta ba kyan gani, haka kuwa sukai hanzarin daukarta zuwa asibitin.

Tafiya suke yayin da sahura ta dauki aniyar sai ta lalata shirin wannan yarin har shi zai dakar mata 'ya shidin waye to, lalle kuwa ya tafka babban kuskure, domin bazan taba rabuwa da shi ba, sai na halaka sa kamar yadda na halaka uwarsa.

A can kuwa wajen su dareib asibitin ya shiga, ummi ce sai baba sai kuma daddy, kakkonsa suke cikin mamaki, domin sudai basu fada masa ba, tsayawarsa likitan ya fito cikin sanyin jiki ya dubesu yace"dan allah ku biyoni zuwa office.

Zama sukai sannan ya kai dubansa zuwa ga dsddy yace"alhaji am sorry amma rayuwar sa tana cikin hadari, accident yayi mai muni, a yanzu haka ya samu karaya 4 gashi kuma ua fada doguwar suma, nidai a yanda zan baku shawara ku dauke ku fitar dashi zuwa kasashen waje, domin anan kadai zasu iya yi masa abinda ya dace.

Daddy ne yayi shiru yana tinanin mafita, baba ne yayi karfin halin cewa to shikenan bakomai sai mu fitar dashi zuwa kasa mai tsarki ko allah zaiyi ikonsa akan wannan bawa nasa, shidai baice komai ba, domin bashi da hurumin yin magana a yanzu,baffa ne ya kallesa yace"babana to yanzu sai ka wuce muje ka huta ko, girgiza kai yayi yace"daddy baba kuje gida ku huta idan nagama komai zan dawo banaso a haura kwana 2 ba'a fita dashi ba, kema ummi jeki gidan kawai kinji.

Wani private hospital suka kaita nan fa aka karbeta aka fara bata taimakon gaggawa, doctor ne ya fito yace"she out of danger, dan haka ku shiga ku ganta, inalillahi kuzo kuga fitsara, fitsara batayi rana ba wallahi,sabra mai futsara yau gashi ta kare a bed na hospital.

Kui hakuri da wannan dan allah kadan ne
Much love
FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
Follow on Arewabooks@MatarUncle
Follow on Wattpad@mataruncle
08067574868
25&26
*TUDUN YOLA*
Tin bayan da inna tabar unguwar sai bayan sati 2 sannan ta dawo, gidan maman anas ta shiga da sallama a bakinta.

Maman anas na kitchen taji sallama kamar ta inna, hakan ne yasakata saurin fitowa tana fadin lale maraba, tabarmar da inna ta gani anan ta zauna, bayan an gama gaishe gaishe inna ta dubi maman anas tace"nikam yarinyar wannan azzahra ta dawo, da mamakin tambayar inna tace"to dama.

Har yanzu baku daidai ta bane.

Inna ce tace"bayan narabu da ita, inalillahi abinda ya fito daga bakin maman anas kenan, to yanzu ina Azzahra take, tabe baki inna tayi sannan ta guntili goronta tace"ohoo mata ma waya sani, nikam zuwa nayi ki bani wannan ajiyar dana baki kan cewa idan azzahra tazo ki bata.

Maman anas ce tai damm sai kuma tace"inna sai dai kiyi hakuri amma bayan kwana 4 da tafiyarku wani saurayi yazo yace na basa kayan, saboda wai suna tare da fateema ni kuma na dauka na basa, kasancewar yace ya santa.

Gaban inna ne ya yanke ya fadi, cikin ranta ta ce"yanzu ina fatin amma a fili taxe"ai shikenan dama na biyone na karba amma tinda ta karba shikenan ni zan tafi, maman anas ce tace"aa inna kya tafi ko ruwa baki sha ba, a kufule inna tace"aa ki barshi kawai na tafi sai anjima.

Fitowarta ne wata mota kalar ash ta tsaya, tsayawa tayi tana jiran wanda zai fito domin a tinaninta saurayin azzahra ne, ganin 'yammata biyu sun fito ne, durkusawa sukai suna gaisheta, kallonsu tayi a fili tace"to ku kuma fa ina fatan lafiya, dayar ce tai murmushi tace "lafiyar kenan inna inaya ce sai munaya kawayen azzahra, daman kwana 2 bata zuwa makaranta ne shisa muka biyo muji ko lafiya.
Chapter 9 · 0% Book details