Sashe 3
Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Faruq ne ya kallesa da kyau yace"buddy bai kamata ba wallahi ka tsaya kayi think karkazo ka yanke hukunci cikin fishi, indai fansa ce nima ina bayanka ka dauka bani da wata matsala, dan haka kai tinani.
*FATEEMAH ZAHRA*
Written by
A'ishatu Bint Muhammad
Matar uncle /Queen Waleedah
Zinariyar Nazari Writers Association
NAZARI WRITERS ASSOCIATION
_Kyawawan Nazari kafin rubutu na
amfare da bin
a'idojin rubutu._
_Cikakken Nazari kafin rubutu kan
ayata duniyar Adabin hausa._
Alkalami yafi takobi
Dedicated to
Fateemah Y Zakariyyah (Oum Ameerah)
Marubuciyar Ahalin Mu Daya
And Idan So Cuta Ne
Episodes 7&8
Daidai lokacin da ta saka kafarta anna taji wani sassanyan kamshi mai matukar kwantar da zucoya, daga idanunta ne yasata saukesu akan tangamemen hoton dake office din na wani garden mai matukar flowers.
Matar ce tace"madam ki zauna anan, yanzu zai karaso, murmushi fateema tayi tace"tohm nagode sosai daga nan ita kuma ta juya ta koma.
Yana daga privacy office dinsa ya kalleta a jikin cameras din dake dayan office din, a hankali ya furta, wow wannan ita ce wadda nake nema tabbas ita ce, domin kuwa ga tsantsar kama irin na, bai krasa ba naga ya dauki wayarsa yana karawa a kunne.
Ganin shirun yayi yawa ne yasata fara tinanin al'ameen, shin ina al'ameen ya tafi kuma bai fada mata ba, sannan kuma bai gaya min ba, sai wata takarda daya bar min, tinawa rati da takardar tana gida bare ta karanta da zaman banza da takeyi.
Bata ankara ba taji wani sanyayyen kamshi ya shigo hancinta, a hankali ta furta alhamdulillah tare da dago kanta tana kallon mamallakin wannan kamshin, dagowarta idanunta ne suka sarkafe dana MD, tsawon lokaci yana kallonta cike da kyakkyawan yanayi.
Saurin janye idanunsa yayi ya nemi waje ya zauna, cikin cool voice yace"tin yaushe kikazo, a ranta tace"ji wata shegiyar tambaya, to naga dai kasan lokacin da nazo ko, a fili ta furta "yanzu na karaso.
Telephone din kusa dashi ya danna yayin da idanunsa suke kan azzahrah, gaba daya kallonta yake, azzahra tasan me yake dan haka dik ta takure, a hankali yace" Please shigo mn, daga haka ya ajiye wayan.
Ko seconds 30 ba a dauka ba, wani mutum y shigo, MD ne ya kallesa yace"ka kaita office din manager ya bata form ta cike, da toh y amsa, MD ne yace"azzahra tashi ki bisu, daga nan suka fice yana kallonta.
Office manager suka shiga a zaune ya ke, a hankali ta gaishesa sannan mutumin yayi mata bayani tare da bata form, dauka tayi ta fara cikewa, kamar yadda tayi tinanin kuwa cleaning ne aikinta, Daga nan aka tafi da ita aka nuna mata bangarorin aikinta.
______---------_______
Faroq ne ya dafa sa yace"zuwa yanzu ya kamata mu nemi mafita, karka manta ba kyalemu zaiyi ba indai yasan da hannunmu a ciki, buddy ne ya cije lebe kana bani haushi wallahi, kai kana da matsala da mataala, ana ga gabas kana da yamma.
Faruq ina fada maka, ni nasan dabarar da zanyi, amma tabbas nasan akwai risk amma dik wani risk ajiyesa a gefe, dan kasan allah sai na dauki fansar abinda yayi min, kuma ba tare da kowa ya sani ba.
Faruq zuwa gobe zamu shiga makaranta saboda kwana 2 ban shiga ba nayi missing dinta, fitowa yayi daga office din, sannan ya hau motarsa ya bar gidan.
NASSARAWA GRA
Kano State.
A wani katafaren gida ya tsaya, tsayawarsa ne yasa wata mota kirar jeep ita ma ta tsaya,cikin kankanin lokaci gate man ya bude kofa, a guje na gaban ya shige ya bar na bayan, cike da bacin ran ganin ya bulesa yasa shima shiga da gudu.
Gate man ne yace"kai wannan gidan allah ubangiji yayi mana sassauci ace gaba daya gida ba hadin kai sai fada, wannan rayuwa wannan rayuwa allah ya daidaita mana ku.
Fitowa yayi shima na gaban ya fito, ido na ne yakai kan buddy da kuma MD a hankali buddy ya hararesa.
Cikin hassala yace"how dare you da zakana hararata, MD ne ya kallesa ya fice daga wajen dayake, cikin bacin ran ganin bai kulasa ba yasa shi janyo masa riga dai dai lokacin da ya saka kafarsa a falon.
Cikin zafin rai MD ya jiyo ya sharara masa mari, take ya cikuikuyo masa riga.
Wata yar tsohowace ta fito ta fara hayaniya, to iyayen bakin hali, kai dai DAREIB abin nan naka kullun gaba yakeyi maimakon yayi kasa sai dai kullun abu yayi ta sama, Buddy ne ya kalli tsohuwar yace"to ai dama hajiya na fada miki DAREIB baya so na, kuma bai karasa ba, MD ya haye upstairs din da zata sadaka da dakinsa.
Hajiya ce tace"kai ni DAREIB bansan ranar da zakayi hankali ba, aikin banza aikin wofi, kuma wallahi bari alhajin ya dawo, dan naga har yanzu abin naka yawa yakeyi, yana jinsu kawai ya fada daki tare da doko kofar dakin.
Hajiya ce taja tsaki tace"kai dai HAFEEZ ka kyaleni dashi wallahi dole ya daina maka abinda yake maka, kai kaine ba a so, dan me zai mareka, aikin banza kawai.
Buddy ne ya shige dakinsa yana hade haden rai, a hankali ya furta wallahi dole nai maganinka DAREIB dole ne ma wannan.
Bed din dakin ya fada yana hada rai yana muzurai kamar Tsohon jaki, wayarsa ya janyo ya lalubo number faruq.
Kui hakuri da wannan update din dan allah ina da uzuri ne, kuma ina godia sosai ubangiji ya ska muku masoya na yan albarka..
*FATEEMAH ZAHRA*
Written by
A'ishatu Bint Muhammad
Matar uncle /Queen Waleedah
Dedicated to
Fateemah Y Zakariyyah (Oum Ameerah)
Marubuciyar Ahalin Mu Daya
And Idan So Cuta Ne
Episodes 9&10
Sallama tayi jin gidan shiru yasata kutsawa ta shiga dakin ta, a zuciyar ta ta furta "to inaga innah bata nan, da tana nan, bata rufe bakinta ba naji tana kwala kiran fati fati, gaban ta ne ya fadi jin kiran da take mata, da sauri tace" na'aaam inna gani nan yanzu zan fito.
Dage labulen tayi tace"to
uwar kinibibi kinaji ina kiranki shi ne baki amsa ba ko saboda ni ba uwarki bace, azzahra ce tace"aa inna ba haka bane, kayana nake cirewa, tsaki inna taja tace"bani kudin da kika samo, zaro ido tayi tana fadin inna kudi kuma, tsaki innar taja tace"wallahi fatsima zanci uwarki ni zaki tsaya kina musu dani, da kyar fai ta lallaba inna akan cewa bata samu kudi ba yau, da kyar dai ta yadda ta kyaleta, sai kuma tace"idan kin gama kizo dazu ubanki yazo, a fili ta firta"inalillahi wa inna ilaihi raji'un, inna me yace miki, harara ta galla mata.
Bta gama kimtsawa ba ta fito tana mata magana, inna ce tace"fati ki kyaleni naji da abinda yake damuna, azzahra ce tace"inna dan allah me yace miki kifada mini kinji.
Tsaki inna taja tace"kai yau naga bakar jaraba, to shikenan ba wani abu yace mini ba illah ki tattara ki koma gidan sa domin nima nagaji da zaman nan da nakeyi a gidan nan tare zamu koma.
Bata san lokacin data zauna ba tafara jero addua, inna ce tace"ke dai wannan anyi yarinyar banza, wallahi komawa gidan habibu kamar anyi angama, domin nima nagaji nafiso na koma gidan sa komai ma ayi a gabana, amma zaman gidan nan baya min ddi.
Hawaye fati ta share tana yi tana magana"yanzu inna gidan zamu koma, wai.
Inna mai yasa kika yadda da zancensa ne, ni banason komawa gidan abbaah domin gidan kamar, tsawa ta daka mata tace"ki tattara yana ki.
Yanaki jibin nan zai turo da mota mu tafi domin ni nagaji da zaman gidan nan daga nan ta wuce ta barta a zaune.
Haka ta hakura ta mike ta dakko abincinta ta shige daki, ci takeyi sai da tagama tai sallar isha'i,sannan ta janyo wasikar da al'ameen ya bada a bata, kallon takardar take cike da fargaba ta fara kokarin budewa.
______******_______
A katafaren falon kusan mutum 8 ne ke cin abinci, hajiya ce ta dubi alhaji tace"idan ka gama.
Inaso ne zamui magana dakai, kallonta yayi yace"wai ke hajiya me yake damunki ganin da yara a wajen yasa ya fasa mata maganar da yayi niyya.
Saida kowa ya watse sannan suka zauna a parlor, hajiya ce tace"dama.
Ba wani abu bane inaso ka shiga tsakanin DAREIB da hafeez domin naga kamar dareib nason ya raina hafeez.
Cike da mamakin maganarta daddy yace"to wannan kuma.
Wace magana ce haka, yo dama ba dole ya raina shi ba tinda a kalla zai basa shekara 4,ni wallahi hajiya na rasa me ke damun kwakwalwarki, ke kullun kina girma kina cin kasa haba dan allah,dan karamin tsaki taja tace"ea mana alhaji ai dolr ka fadi hakan dik da matar nan ta fadi ta mutu amma baka daina sonta ba, kai ni wai wace irin jaraba ce wannan, cike da mamaki yace"dole bazan daina sonta ba, domin ita batayi min abinda ke kikeyi min, kuma indai so ne yanzu na fara kuma banga ranar dainawa ba, na dauka arzikinta muke ci ko kuwa tsabar butulci sai na yada yaranta, ke hajiya komai fa ina sane da dik abinda ke faruwa a cikin gidan nan karkiga kamar banason su DAREIB ina son abuna ehee, domin ni rayuwar su dareib ta fiye min rayuwar su hafeez, dan haka indai akan wannan maganar ne karki kuskura ki kara tada maganar, tashi yayi ya gyara zaman jallabiyarsa sannan ya mike ya wuce ya barta anan cike da mamakin lafazinsa.