← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 26

Sashe 6

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dareib ne ya Mike yace"toh shikenan ni zan tafi sai goben, zanyi payment moneyn a reception, mikewa doctor yayi ya miko masa hannu sukai musabaha sannan ya wuce, zuciyar sa fall da rashin tsoron allah da inna tayi, da ita tasan ba san ahalinta ba amma shi ne tin da can batai kokarin fada mata ba, dan karamin tsaki yaja, ya shiga mota sannan ya kalli drivern yace "muje kai.

A harabar gidan yaga wasu motoci, dan karamin tsaki yayi, drivern ne yayi saurin parking domin yaga ran ogannasa a 6ace yake, ko kallonsa baiyi ya huce zuwa babban falon gidan, shigarsa nan kowa ya zuba masa ido, kallon mutanen falon yakeyi a zuciyarsa ya furta"ya ilahii su kuma wadannan har sun gama hutun, hucewa zaiyi daddy ne yace"DAREIB cakk ya tsaya.

Jiyowa yayi ya karaso yana fadin"na'am daddy, karasawa yayi kusa dashi ya zauna yana kallon mutanen falon, a zuciyarsa ya furta'"ciwon kaina ya dawo.

Daddy ne yace" baka ga baba ba, dan murmushi yayi yace"daddy amm dama dama, baba ne ya katse sa da fadin ya ganni ai bazai ganni ba, na fuskancin yaron nan dareib dik rashin aure ne yake damunsa, kuma zanyi maganin ku, wato kai Hashimu bazaka matsa musu suyi aure ba ko.

Yara sun zama manya manya, amma kaki takura musu tinda haka ne kuwa ni nasan matakin da zan dauka akanku ku duka, kuma shima wancan yaron dayaje kasar arna ya tare ka fada masa ya dawo gida.

Tashi yayi ya tafi yana ta fada, dareib ne ya dafe kansa yana furta "shikenan tinda baba ya dawo kowa sai yasani, kallon sauran yaran gidan yayi mata ne 3 sai sauran maza 5,daddg ya kalla yace" daddy nizan wuce, daddy ya mike yace"dareib ka biyoni inaso zamuyi magana ne, daga haka ya wuce.

Hajiya sahura ce ta zabga musu wata harara, faruq ne yace"ni wallahi ba wanda zai min aure yanzu haka kawai ban gama cin kuruciya ta ba kawai za a wani daura min aure.

Cikin matan nan guda 3 daya tace"aikin banza wai bai gama cin kuruciya ba, yaron da ake kamasa da mata ai wadda ta aure ka tabbas tayi jihadi, domin indai a haka za'a tafi zaka iya goga mata HIV ina kuwa lamari yayi dadi.

A fusace yayo kanta, da gudu ta mike tawuce daki hadi da saka mukulli,wani duka yakewa kyauren amma ina, dawowa yayi yace wallahi mama dik ranar dana kama Sabrah sai na mata hauka, sahura kallinsa kawai tayi ta mike tace"ku tashi ku tafi ku kwanta dare yayi.

Mikewa sukai kowa yana fadin albarkacin bakinsa, domin sun sani tinda baba ya fadi hakan to ba wanda ya isa ya musa masa.

A falon daddy kuwa kallonsa daddy yayi yace"dareib me yake damunka ne, dan uwanka ya kirani yace ya kiraka baka daga ba, dareib kasani tin bayan tafiyarsa haka kuke koda yaushe kuna kiran juna.

Dareib ne yace"naga kiran nasa daddy lokacin ina asibiti ne, da mamaki daddy ya kallesa yace"dareib me ya kaika asibiti, hular kansa ya cire yace"daddy mutane basu da imani, wata yarinya ce bata fi sa'ar Safeena ba amma wai daddy hawan jini gareta, kuma yayi matukar hawa sosai, nan dai ya kwashe labarin ya fada masa.

Daddy yace"yanzu ina ita innar data barta, dan dage gira yayi yace"nima yanzu bansan inda ta tafi ba, acewarta wai ta koma gidan danta, daddy yace"batayi wani kwakkwaran bayani ba, girgiza kai yayi yace"daddy batayi ba.

Daddy ne yace"shikenan tashi kaje goben sai muje ka kaini na ganta, dareib ne yace"amma daddy dan allah alfarma daya ka taimaka ta zauna a gidan nan, domin yarinyar...

Katsesa daddy yayi yace"ba komai dareib tashi kaje ka kwanta kaga 12 har tayi, yana mikewa sahura tana shigowa, shi kuma ya fice daga dakin.

Dakinsa ya shiga, gaba daya komai ya jagule masa ya rasa ta ina zai fara ga baba ya dawo, ga lamarin azzahra, gashi bai san tayaya zai fadawa dan uwansa ba, tsaki yaja ya cire kayansa tare da daura towel ya shige toilet.

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
The Stars
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
15:16
Sai da ya gabatar da sallah sannan ya nemi waje ya zauna, gaba daya ya fada duniyar tinani ya rasa ya zaiyi, jin karar waya tana ruri ne yasa shi kallon screen din, ganin an rubuta broh yasa shi hanzarin dagawa.

Karawarsa kenan a kunne yace"bro am so sorry aiki ne yayai min yawa shiyasa ban kiraka ba, banji me yace ba sai murmushi kawai yayi yace
"naji broz yanzu dai zan kwanta ne sai da safe zan kiraka, daga nan sukai sallama ya kwanta.

Washe gari bai fito ba sai wajen 10 yana fitowa ya tarar da al'ummar gidan a dining suna breakfast, zama yayi sannan ya fara gaishesu, amsawa sukai cikin sakin fuska, sahura ce taja karamin tsaki da ba wanda yaji sa, baba ne yace"muhammadu naji uzurinka sannan ba komai allah ya taimaka, allah yasa a samu iyalin nata.

DAREIB ne yace"ameen baba, kallon sabrah yayi yace"dan allah sabra hadamin basket zan kai mata abinci, kowa kallonsa yayi, sabra ce taja tsaki ta mike tace"shikenan shi mutum bazai huta va.

Baba ne yace"ke sabira uwarki, wai ku wane irin yarane marasa tarbiyya, dik cikin yaran nan banga daya na kirki ba sai mai sunan mariganyi ta, daga ita sai affaaan amma dik cikinku ba mutunci gareku ba.

Ummy ce tace"yaya kyaleta bara na zuba maka, zata hadu da gamonta, tinda ita allan da yayi ta bata ji, sabra ce ta bigeta tace"and so what ummy kawai dan kin ganni ina da kyau, dik cikinku nafi kowa kyau da....

Daddy ne ya fito, da sauri ta zauna, tsayawa yayi ya kalli sahura yace"ki shirya wadan nan yaran anjima zasuyi baki amma ke ummi banda ke kasantuwar yanzu zaki fara University.

DAREIB ne ya mike yace"baba ni zan wuce kasan menene baba, nan da wani week din zaka tafi umarah daga nan kuma sai...

Bai bari ya karasa ba baba yace"eyeeeh kace umarar bana da ni za'ayi, kace na fara shirye shiryen kayana.

Fita yayi ummy ce ta biyo bayansa tana fadin yaya na hada kayan, kallon ta yayi hadi da murmushi tace"shikenan tohm muje ko, mota ya hau ya bar gidan sun atafe suna hira.

A bakin hospital din suka tsaya, bai wani sha wahala ba ya shiga dakin da aka kwantar da ita, tana zaune tana kuka.

Ganin mutane ne yasa ta saurin gige hawayen tana sunkuyar da kanta, da mamaki ummy take kallonta, domin yarinyar nan allah ya zuba mata kyau da baiwa, maganar DAREIB ne yasata saurin yin murmushi, zama yayi a daya da kujerun dakin.

Kallon ta yaganta sukuku, a hankali yace"ya jikin naki cikin sanyin muryar da tasha kuka tace"alhamdulillah sir da sauki,tashi yayi yace"ummy ku zauna ki bata abinci kinji zanje nadawo, nasan kafin lokacin ma doctor zai iya sallamarta.

Cikin ladabi tace"tohmm yaya sai ka dawo.

Yana fita ta matso kusa da ita, da fara'ah tace"sister ya sunanki, a hankali tace"azzahra, da dan murmushi tace"laaa irin sunana, ashe takwarata ce.

Murmushi ta sakar mata, tana kara yaba kyau irin na ummy, sakkowa tayi ta bude basket din, plate ta dakko ta zuba mata soyayyen irish da soyayyen kwai, sai ta hada mata ruwan tea.

Maimakon ta mika mata sai ta fara kokarin bata a baki, da murmushi tace"ummi ki barshi mana zan iya ci da kaina, kinga ai jikin yayi sauki, mika mata tayi ta fara ci ita kam sai zuba mata surutu take, kafin wani lokaci azzqhra ta sake jikinta da ummi sai hira suke.

A haka doctor ya shigo ya kara dubata sannan ya bata takardar sallama, hadi da cewa idan dareib yazo su tafi jikinta nata yayi sauki.

Da murna ummi ta rungumeta tace"yawwa sisy kinji sauki shikenan ba ke ba kara komawa cikin wata cutar kuma insha allahu rabbi ko.

Azzahra ce a fili murmushi tayi, a zuciyar ta ce"yanzu kuwa nake a matsala ummi, domin bani da kowa a duniyar nan sai allah, bansan inda zan zauna ba, bansan a ina zan samu abinci ba, tabbas inna ta cuceni samm zama da ita bai min rana ba, a take kuka yaci karfinta da mamaki ummi ta mike tana lallashinta.

A can kuwa bayan kowa ya watse, sabra ce tace"mama nifa kawai a daura auren nan saboda da alama mutumin nan akwai shi da kudi, gaskia daddy ya birgeni da ya yadda da zabi na.

Safuna ce ta kalleta tace"nima ai bazaki fada masa kudi ba ko kyau domin gaba dayansu kyawawa ne matuka, ajin karshe, mama ce tai murmushi tace"ai ni nan farincikinku shi ne nawa ku kyale ummi taje tai ta shirmenta, gaba dayansu murmushi sukayi domin mahaifiyar tasu ta karfafa musu gwiwa.

Safeena ce ta kalli sabra tace"wai ke naji ana cewa wata zatazo gidan nan, sabra ce tace"nima ai haka naji ko tinda daga bakin daddy maganar ta fito, kuma kinsan tinda ya furta sai tazo.

Safina ce tace"zata ci uwarta kuwa domin allah daya sai na wahalar da ita, allah sai ta gwammace ta gudu ta bar gidan nan, sabra ce tace"aikin banza yarinyar da bata da iyaye har zata fada mana wata maganar mu kyaleta.

Mama dai dik wannan hirar bata furta komai ba, mikewa tayi tace"ke sabra ku dora mana girkin rana ni zanje na kwanta na huta.

Kallon kallo suka shiga yi, sai kuma safina tace"haba mama kinsan ba abinda muka iya a kitchen, kawai a jira ummi ta dawo ko a kira laure, tashi tayi tace"auhh na manta ai, shikenan ku tashi kuje ku huta sai ku fadawa Lauren ta dora ko.

Haka kuwa akayi lauren ce ta dora musu abincin rana, sukuma suka shige daki kowacce ta dauki wayarta, tana dannawa, sabra ce tace"ke kinsan allah gayen nan ko ya dameni akan na tura masa pic dina.
Chapter 6 · 0% Book details