← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wano dogon tsaki ta ja tace" aikin banza ni nadauka wasu saurayin azzahra ne ko kuma yaron nan mai bani kudi, ashe kune to azzahra dai ta koma dangin uwarta can lagos, dan haka idan kunga zaku iya binta sai kuje, har ta huce su ta dawo tace "to yanzu dai bani ladan tsayar dani din da kukayi.

Munaya ce tace"yanzu inna idan munje lagos din ina zamu sami Azzahra,inaya ce ta miko mata sabuwar dubu, sai da ta linke sannan tace" nan fa daya nima bansani ba dan haka sai anjimanku, tafiya tayi ta barsu a tsaye.

Inaya ce tace"kinga munaya tinda muna shiri sosai da khaleel kama ta yayi muje mu samesa ko mu kira sa a waya, kallonta munaya tayi tace"aa ba haka za'ai ba gidan zamuje domin ko bamu tarar da shi ba, sai mu fadawa fadila ko zamu samu masaniya a wajenta, domin kuwa ita kadai ce zata iya tunkarar sa ba gargada.

Yadda tayi da shawarar munaya sannan tace 'toh muje mana kinga magariba ta gabato, juyawa sukayi sannan suka shiga mota, tafiya sukayi suka bar gidan.

JIGAWA STATE
Al-islam company nigeria limited
Jerin motoci ne suka fito daga cikin company, gaba dayansu black ne kirar jeep, tafiya suke saman titin dayake hanyar, a slowly suke tafiya, binsu nayi domin naga ina suka nufa.

Tafuya suke dikda ba wata tafiya mai nisa suka yi ba Sannan suka shiga wani lungu, inalillahi wani katafaren gida ne mai matukar fadi da girma, kodan na bar muku ku kiyasta da kanku, domin ni bazan iya fadin irin tsarin da gidan yasha ba.

Sai da motocin suka gama shiga sannan na shiga, wata nutsattsiyar budurwa ce mai matukar kyau da aji ta fito tana rike jakar hannunta, wani saurayi ne ya matso zai rufe mata motar, da sauri tace"no barshi kawai zan rufe da kaina.

Gaba daya bodyguard ne sanye suke da bakaken kaya, tafiya take suna binta hadi da kallon gefensu, ko zasu ga wani abin cutarwa, parlorn gidan ta shiga, ohhh ni matar uncle bazan iya kiyasta wannan falon ba yadda zai kasance.

Kamshin turaren jikinta ne ya hade Palon da kamshi banda kamshin burner da aka saka domin fitar da daddadan kamshi.wani dattijo ne sanye da glass fari ya fito kana ganinsa kaga jinin boko.

Da gudu ta fada jikinsa shi kuma ya rungumota yana fadin"daughter yanzu da nace karki biya company amma sai da kika biya ko, cikin shagwaba tace"dahh to yanzu ba shikenan na gama da wannan matsalar, naje naga kowa bodyguard din ya sallama su kuma suka zauna a falo.

Wata dattijuwar mata ce ta fito, sai wasu yara su 2 kamar su daya kallo daya ya tabbatar min da twince ne.

Zama sukayi gaba daya akan kujera, suna mata sannu da zuwa,da murmushi ta amsa musu sannan ta kalli dattijuwar tana cewa"mum da dan sauri ta fado jikinta tana kara lumshe idanu, a hankali ta furta"mum ni har na manta rabon danaji dumin jikinki sai yau, gaskia nayi missing ta fadi hakan cikin shagwaba.

Mum ce ta dubeta tace"ai dama ke kikaso,in banda abinki ina Nigeria ina Spain da zakije ki zauna a can, kuma ni banga abinda kikeyi acan din ba tinda karatu ne ai kin gama ko.

Cikin yaren Spanish tace"mum na zauna zaman jiran result ne kuma ni ban ga dadewar ba tinda dika fa 2week na kara, mum ce tace"dama ai idan so cutata haka kike juya harshe kina min wasu zantukan banza da wani yare daba na garinmu ba.

Gaba daya falon dariya sukayi sannan ta huce zuwa lifter ta danna ta, sama tayi tana fadin, a shirya min lunch yanzu zan dawo ba dadewa zanyi ba.Dariya gaba daya sukayi suna mamakin sauyawarta lokaci daya.

Mum ce ta dubi daddy tace"nayi mamaki kwarai da sauyawar ummulkhair gaskia, daddy ne yace"dama na fada miki idan har tai nisa da gida to komai ma zai chanja zai zama kamar ba ai ba, kuma ai dole ta dau dangana.

Mum ce tace ai shikenan, kallon twince tayi tace"kira min cook kice ya shirya table nan da 5mint, dayar ce ta dauki wayarta kirar iPhone pro max ta danna kiran cikin second daya ta fada masa sakon mum sannan ta ajiye wayar.

G.

R.

A
Kano state
Motar su inaya ce t shiga gidan su khalil paking sukai sannan suka fito, gida ne mai kyau hadi da daukar hankali, babban falon gidan suka shiga, amma ba kowa hakan yasa suka kira fadila a waya, can sai gata ta fito.

Falon baki suka zauna sannan suka fara gaisawa munaya ce ta fadawa fadila komai hadi da bata hoton azzahra, fadila dadi taji domin yarinyar tayi mata kyau, sannan kuma ga zuwan kawayenta 2 wanda rabon data gansu har ta manta.

Bayan gabatar da wannan hirar ne suka barke da wata hirar kuma ta daban.

Matar uncle
Ina fateema
Ya jikin dareib
Wacece ummulkhair
Ku biyo ni domin jin wannan amsoshin
FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
Follow on Arewabooks@MatarUncle
Follow on Wattpad@mataruncle
08067574868
27&28
Wata kara ce ta karade gaba daya gidan, wani saurayi ne ya shigo da sauri yana kallonta, cikin rashin sanin inda take yasa ta fara kallo sa tana fadin ku kyaleni, ni bansan ku ba, bansan a ina nake ba.

Gaba daya mutanen gidan ne suka yo dakin, ganin mutanen dake dakin yasata kara birkicewa, allah sarki azzahra lalle sahura ta zalunce ta.

Kokarin taba ta suke amma taki basu dama sai sambatu take tana cewa"ku kyaleni, ku kyaleni na koma nafison can akan nan, dan allah ku kyaleni.

Kowa mamaki yakeyi da kyar aka samu wata budurwa tayi mata allura sannan bacci ya dauketa,gaba daya fitowa sukayi suna kallon junansu.

Babban cikinsu ne ya sharce gumin face dinsa, sai kuma ya kalli wata tsohuwa yace"hajiya wallahi laifinki me gashi yanzu kin dakko mana mahaukaciya, wai yanxu ya kikeso muyi.

Tsohuwarce tace"kaine mahaukaci ba ita ba, ka kiyayeni wallahi aminullahi banason shashancin nan naku na samarin yanzu, naga ko ubanka bazai dubi idona ba yace wa wannan yarinya tawa mahaukaciya.

Budurwar cikinsu ce tace"to hajiya kiyi hakuri ba mahaukaciya bace amma idan haka ne ai sai ki fada mana sunanta kin barmu sai bulayi muke cikin duhu, dan jim hajiya tayi sai kuma tace"sunanta sajida, kuma wallahi ku kyaleta saboda bakusan ta ba, ni kallon farko da nayi mata kawai naji yarinyar ta birgeni.

Aminullah ne ya kalki budurwar yace"khairat nifa nayi nayi hajiya ta fada mana a ina ta samo wannan yarinyar amma abu ya citira, taki fada tace sai abeeh da ummee sun dawo daga dubai kuma har yanzu basu dawo ba.

Hajiya ce tace"eaa bazan fada ba, wato kema khairat ina ganinki shiru kamar bakyasan gulma ashe so kike ko, yanzu a gabana zakuyi gulma ta keda dan uwanki ko, shikenan ai sai kuyi lokacinku ne.

Khairat ce tace"aa hajiya ai yaya tambaya yayi kuma kinga tinda yayi tambaya kamata yayi ki bashi amsa ba kibarmu a duhu ba, dan tsaki hajiya taja sannan ta mike ta kallesu tace"ke khairat tashi huce daki kai kuma ka huce ka tafi ka kwanta naga dare yayi yanzu sai ka kara lokaci fiye da awanni ko.

Aminullah ne ya kalleta yace"dama ko baki fada ba ai, mikewa yayi ya haura sama, dakin ya shiga wani saurayi nagani yana danna waya, kallon sa yayi yace Nuraddeeen wai kai me yake damunka, kanaji yarinyar nan tana ihu amma ko ka fito kazo ka duba ta.

Kamar bazai basa amsa ba sai kuma yace"am so what dan tayi ihu, ni nakawo ta gidan nan, naga bani na kawota ba ko, tinda bani na kawota ba wallahi ko mutuwa zatayi bazan je nace zan ganta ba,tinda taki fada mana inda ta samota waya sani ma ko aljana ce.

Aminullah sanin halin Nuraddeeen yasa bai kara masa magana ba sai toilet daya shige domin yayi wanka ya kuma dauro alwala.

Hajiya dakinta ta shiga anan ta tarar da fateema da take bacci hankalinta kwance kamar ba abinda yake damunta,kllon yarinyar ta karayi a karo na 2 tace"allah ka raya wannan yarinyar domin dik inda ta fito nasan na santa.
**************
Daddy ne ya kalli aryan yace"to kai yanzu ka daukesa ka kaisa kasar waje, wallahi aryan ka sani bada yawu na ba, domin naga gaba dayanka kanka rawa yake,da mamaki aryan ya kalli daddyn nasu, domin shi dai a iya saninsa irin wannan maganar bata taba fitowa daga bakin daddyn nasu.

Shigowar sahura ce yasa ya fara yiwa aryan fada"karka ga kamar bana gani nan nan ka daki sabra bance maka komai ba yanzu shi ne zaka wani dauki dan uwan ka kace zaka tafi dashi kasar wahe ko, to wallahi yadda ka daukesa ka tafi dashi ka sani cewa karku kara dawo min gida domin yanzu sam bana buqatar ku, da mamaki yake kallonsa.

Sahura ce tai murmushi a ranta ta furta"uess aikin sarkin aljanu yaci, yanzu in banda aikin nan yaci ta ina alhaji zai fara yiws aryan fada.

Aryan ne yace "amma daddy me mukai maka nida dareib, hannu ya daga alamar yayi masa shiru sannan yace" ba abinda kuka mon naga ganin dama ta ne ko kuma naga tinda gida nawane ai dole sai abinda nayi niyya za'ai ko.

Shikenan abinda aryan ya furta sannan ya mike ya fice,yana fitowa daga falon daddy room dinsu yayi, gaba daya komai na dareib ya debo ba abinda ya bari sai wasu tsirarin kayan sawa, har ya fito yajiya ganin wata karamar drawer yasa komawa ya bude, wani dan karamin diary ya gani, dan haka ya dakko sa ya fito.

Ummi ce ta fito tana kuka domin ita samta rasa me ke damunta kamar taso tayi mantuwa kamar ta bar wani abu mai muhimmanci, ganin aryan da jaka yasata tsagaitawa tace"broz ina zuwa bai kulata ba ya huce yana kallon hanya.

Sahura kuwa leko ta farayi ta windown sama, tana kallon aryan ya juya ya kalli gidan sanann yafito yaci gaba da yafiya kamar yadda mahaifinsa ya buqata, taxi ya tarar ya shiga sannan ya kwatanta masa inda zai saukesa.
Chapter 10 · 0% Book details