← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turus tayi ganin sajida a makale da wata dattijuwar mata, wadda da gani tada wahala, dikansu mikewa sukayi, hajiya ce ta mike sai kuma ta zauna tace"ohhh ni Larai wa nake gani kamar khadijar hashim, dama ke khadija kina nan tsakani da allah kika barni da wannan shegiyar matar wadda ta asirce min yaro, kai duniya allah sarki khadija, sai kuka,kowa na dakin kuma sai ya saka dariya yana kallon hajiya harda noor wanda yake kuka, tsamm ya mike ya koma kusa da sajida, ganin kamar bata gansa ba shima ya juya ya koma dayan barin na hagu ya makale a jikinta.

Hajiya ce ta kallesu daidai lokacin hashim da hafeez suka shigo, ita dai safina tana can kusa da step na bene na falon ta zauna ta rafka uban tagumi, ummy ce ta zo kusa da ita sannan tace"safina dan allah zo muje zan fada miki wani abu, safina tasowa tayi domin tasan tabbas ummy tasan komai, shiyasa ita bata kaita a dammuwa ba.

Falon gaba daya kowa ya zauna yana nan daddy hafeez ya bude taro da addu'ah, baya ga haka kuma aka gabatar da zama a wajen, sannan kuma aka juya hirar zuwa hirar yaushe gamo, dareib ne ya kalli fatima domin shi tin kallon farko da yayiwa wannan yarinyar yasan da cewa jininsu ce ita.

Ummy ce tace"safina ki daina damun kanki a kan lamuran momi, nasan momi zata dawo sannan kisani na riga dana saani cewa momi tana zuwa wajen bokaye da malaman tsibbu, saurin dagowa safina tayi tana kallon ta cike da mamaki, a ranta tace"kenan ita ta sani amma ni nakasa fahimta, cigabatayi dayi mata magana tana kara fadamata wasu abubuwan.

Da daddare kowa yana kan dining area noor na makale da sajida, cikin gwaranci yace"aunty ina kika tafi yau tin safe banganki ba, dariya sajida tayi tana kalln ahmad da shima ita din yake kallo, cikin farinciki tace"wajen mamana, noor cikinnzance yace"nidai bazanje wajen mamana ba domin ni bata so na, idan naje aunty allah bata kulani.

Sajida ce tai murmushi sai kuma tace "to ai ga wata mamar ka samu ko,dariya yayi sanann kowa ya fara kokarin tafiya, haj bilkisu ce ta mike tare da yiwa kowa da kowa sallama ta tafi yayin ds sauran yaranta suka mara mata baya, nan kowa ya watse ya rage daga khadija sai daddy da yaransu,suma basu wani zauna ba suka mike sajida ce tace"ammah zan biki muje, aryan ne ya sakar mata rankwashi a ka yace"eaa wato kin manta dasu mannal wuce ki tafi kuje ku kwanta, badan taso ba ta wuce, yayin da dareib yace"amma kaidai aryaan wallahi mugu ne, yanzu ya mutuniyar taka, wani kallo ya watsa masa sanann yace"munyi fada, dareib ne ya dafe goshi yce"omg kana sani a matsala sai nayi dik yadda zanyi na samomaka mata amma sai ka bulamin kasa a ido kai a tinaninka hakan ya dace ko, dareib mikewa yayi ya bar falon.

Acan daki daddy shi da khadija suna zaune daddy ne ya kalleta yace"khadija ki yafe min nasani tabbas ban kyauta miki ba, domin saurin dakatar da shi ammah tayi tace"haba daddy meye kuma ba bani hakuri ni bakami laifin komai ba, domin kuwa dan adam ai dama haka yake, dole na baki hakuri khadija domin ni ne sila ni naje na aurota da ban auro ta ba da dik hakan bai faru ba.

Khadija ce ta janye hirar da fadin ina aka samo wannan yaron, daddy da fari shiru yayi sai kuma yayi murmushi yace"noor ai dan gidan nuradden neh, da mamaki khadija ta tace masha allah to ina mamansa, kawar dakai yayi yace"ammah dogon labari ne wannan amma ki bari zan fada miki wani lokacin yanzu ki fada min meya faru a tafiyarki.

Khadija ce taja dogon numfashi sanann tace"a yanzu hashim ba abinda zan iya tinawa
a game da tafiya ta da kuma iya adadin shekarun da nayi, ni yanzu nagode allah daya saka har yanzu yarinya ta tana raye dik da nasan tasha wahala amma inason zuwa kano domin zuwa naje naga a inda tayi rayuwa.

Daddy zaiyi magana tayi saurin katsesa,da fadin dan allah hashim karkace aa bahaka ba, dan allah ka kyakeni, daddy ne yayi murmushi yace"wannan dik mai sauki ne amma ki bari sai nan da wani week din sai muje ko, kallonsa tayi badan ranta yaso ba haka tabar zancen.

Fatima ce akan sallaya tana sallah, noor yana game jin karar waya ne yasa noor saurin dagawa yana fadin"papa banji me yace masa sai dai naji yace tana sallah ne, murmushi noor yayi nan suka fara surutu.
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
No:-08067574868
Page 63&64
BAYAN KWANA 4
A wannan lokacin hajiya ta yanke zaman hashim da iyakinsa a wannan gida, gaba daya sun tattara sun koma nasu part din, komai ya huce domin aryaan ya fra kokarin konawa india inda zaije ya samo transfer a dawo dashi nigeria da aiki, kasantuwar akwai reshen campanyn anan.

Shi kuma dareib na kokarin komawa kano inda zaije ya kai ziyarar zuwa campany domin ganin yanda abin ke tafiya.

Gaba daya 'yammatan ne a dakin ita dai safina har yau abin momi mamaki yake bata,daddy ya shigo shi da abbah, saurin sakkowa sukayi kowa ya zauna a kasa,suna zama dad na shigowa, mannal ce da hanna cike da farinciki suka mike harda' yar kararsu suka rungume baban nasu,shima cike da farinciki yake kallon yaran nasa wanda tubarkallah sai yaga sun kara girma.

Sauran ne yammatan kowa ya watse bayan angaisa harda mannal da hanna da suka bi bayan sajida, a falo suka tarar da ammah akan kujera tana kallon television, zama sajida tayi sannan ta kalli noor dayake gefen ammah tace"kai noor nifa yanzu bangane maka ba, dani da ammah wakafi so, ammah ce ta dungureta hadi da cewa zahra ki dagani kewai meyasa san jikinki ya miki yawa ne ke wai bazaki girma bane,turo baki tayi cikin shagwaba tace"kai ammah dan allah amma dayake noor ne shi kikafi so dani shi ne har da dorasa akan cinyarki ko, cike da mamaki tace"gidanku zahra sai kuma ta matso ta janyota, dariya sauran su mannal sukayi.

Sun dan jima ammah ce tace"safina zauna ku kuma ku bamu wuri zamuyi magana,fita sukayi suka tafi garden, ammah ce tace"safina na'am cike da kunya, domin ita ta rasa dalili najin kunyar ammah,ji tayi ammah tace"ki dauke ni a matsaayin mahaifiya sannan ki daina jin kunyata, kiyi koyi da ummi mana safina, shiru tayi sai kuma tace"toh ammah insha allahu zanyi hakan, ammah ce tace"ameen daddynku sunyi magana da anwar nasan me may be kinsan da maganar cewa gobe zasu kawo lefe sai kuma nan da wani month din biki ko, cikin dakewa tace"eaa ammah ya fada min zai kawo lefe amma baice min za a saka rana ba, murmushi ammah tayi irin na manyan tace"dama nasan ba lalle ya fada miki ba,da murmushi safina tace"ammah dik yadda kukayi shi ne daidai, sannan dan allah inaso ne naje naga sabrah.

Shigowar aminullah ne ya katse hirar safina ce ta sunkuyar da kai, aminulkah ne ya zauna yana fadin washh ammah nagaji wallahi, murmushi tayi sai kuma tace"safina jeki kitchen ki debo masa abinci nasan dai tatsuniyar gizo bata huce ta koki,dariya aminullah yayi sannan ya kalli safina yace"ke kam ki sauri mana kinji yunwar dake ci na kuwa.

Da yamma kusan dik matasan gidan na harabar gidan sun shimfida katuwar dardauma, kowa na zaune ana hira yayin da iyayen kuma ke cikin gida,mota ce ta shigo gidan amma ba wanda ya kalli motar har ta gama parking dareib ne daya fito yanzu da akwati a hannunsa ne ya ga mai shigowa gidan, da murmushi ya karasa yace"nuradden kai ne tafe, kaga wani ikon ina shigowa kai kuma kana fita fadin nura, dariya dareib yayi sannan ya huce suka fita.

Gaba daya hankalinsu yana kan game din da suke yi, tsayawa yayi yana kallonsu, can ya hango sajida ba dankwali ga dankwalin can gefe, Cike da kulewa ya bar wajen domin idan ya tsaya yi musu magana ma wani babban lamari ne, noor ne ya hango sa cikin daga murya yace"laaah ga papa nan fa kowa ya fara daga kai yana kallon sa.

Baiyiwa kowa magana ba ya bar wajen, ba wanda ya tsora sai zahra da tini ta fara neman dankwalinta tana dubawa,noor ne ya mije ya bisa, falo ya shiga nan ya tarar da iyayen nasa, cike da fara'a ya ajiye akwatin ya zauna akan kujera yana kallonsu, cike da mamaki karara a face din sa yace"ummieh kamar ammah, ko shiyasa naga dareib yanzun nan yana kokarin fita, bilkisu ce tace"ea mana dole ai ka gansa, ummieh ce tace"eaa ammah ce dai gatanna, cike da farinciki ya matsa hadi da rungumeta.

Hajiya ce tace"to sarkin sakarci nifa banason wannan shegioyar al'adar taka ta rungume mutane,juyowa nuradden yayi yace"dama ai ke bazaki waye ba,dukansu dariya sukayi, ummie ce tace" to ai ammah itace mahaifiyar sajidah, a fili yace"wace sajida,hajiya ce tace"gidanku ai ka fimu sanin sajida wadda noor yake hannunta, saurin kallon ammah yayi sai kuma yayi murmushi ya sunkuyar da kai hadi da sosa kai ya mike tare da fara kokarin hawa sama.

Hajiya ce tace"to sarkin rashin kunya ai nadauka zakaci gaba da abinda kake ne, da mamaki ammah tace"me ya faru naga kuma ya tafi, ummieh ce tace"ba dole ya tafi ba ammah, shi ne fa keson sajidah,cike da mamaki karara a fuskarta take jinjina lamarin, cike da farinciki akan fuskarta domin kuwa tasan wanene nuradden.

Tinda nuradden ya shigo zahra taki yadda su adu domin ta riga da tasan me tayi, ta sani a rayuwar sa bayason a bude kai a gaban mutane, dan haka tana dakinta ita da noor suna game, ammah ce ta shigo dakin kallonta tayi sannan ta matso ta zauna, da murmushi tace"noor kaje wajen papa yana kiranka,saurin dagowa sajida tayi tana zare ido kamar wata mara gaskia.
Chapter 23 · 0% Book details