← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Filin jirgi ya kaisa cikin kankanin lokaci jirginsu ya tashi zuwa india, domin shi baiga amfaninzaman nigeria ba, tinda har daddy ya budi baki yace baya sonsu su tattara su tafi, to shi bai ga abinda zai dawo dashi ba.
__----________-------______
Dinner suke cikin farinciki, daddy ne ya dubi ummulkhair yace"kinga company amma baki bani labari akan managern dana dora ba, kllon daddyn tayi tace"daddy ai lokacin da naje baya nan sun tafi kano domin gudanar da wani company amma abin ya birgeni gaskia, domin naga company ya tashi fiye da yadda na barsa.

Amma daddy ya sunan managern, kowa shiru yayi yana kallon daddy, mum ce tace"aa wannan kuma ai sai idan kinje kinji ko 'yammata, dariya gaba daya sukayi, a ransa ya furta"ya ilahi allah ka dawwamar da farinciki a zuciyar ummulkhair.

Kallonta twince sukai dayace tac "amma aunty khair baki bamu tsaraba ba har yanzu kodai ba abinda kika siyo, ummulkhair ce tai murmushi tace" mannaal ke kuma baki da aiki sai tambayar tsaraba, inda hannah ya fiki kenan ita sam bata tambayar tsaraba.

Wadda aka kira da mannal ce tace"ea mana ai bazata tambaya ba saboda ita kullun rayuwarta rayuwar game ce, nikam dole na tambaya don gaskia inaso, khair ce tace"mata ai shikenan sai ki bari sai gobe,haka suka gama dinner sanann suka danyi hira daga nan kuma kowa ya huce zuwa dakinsa.

Mum ce da daddy a daki, mum ce tace"yanzu idan taje ta tarar da sunan wannan managern da kuma kamanni irin na sa ya za ai kenan, dassy ne ya nisa yace"dalilin kenan dana basa aikin company domin so nake ummulkhair ta auresa, cikin mamaki mum ta zaro ido tace"kamar ya ta aure sa alhaji, dariya yayi yace"eaa ta auresa domin naga har yanzu da soyayyarsa a cikin zuciyarta dan haka dole na bata abinda takeso.

Da wannan lamarin suka rufe hirar Kasantuwar dare yayi
FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
Follow on Arewabooks@MatarUncle
Follow on Wattpad@mataruncle
08067574868
29&30
Da sallama ta shigo falon ta ajiye basket na abinci, khairat ce ta fito sanye da abaya sai lab court a hannunta,ganin matar ne yasata fadin"aa maman amrah bakya gajiya dai ko,wadda aka kira da maman amra ce tace"ina fa zan gaji khairat ai ba komai, kallon watch din hannunta tayi tace"shikenan maman amrah ni zan wuce hospital saboda nayi late ina da theater by 10 daga nan ta fito farfajiyar gidan, wurin motoci tayi sai da ta zabi mota mai kyau sannnan ta shiga ta bar gidan.

Maman amrah kuwa data ajiye basket din dakin hajiya ta tafi, a zaune ta ganta tana jan carbi wato lazimi, sai kuma sajida a gefe da take ta faman bacci, maman amra ce tace "hajiya barka da safiya, bayan sun gaisa ne hajiya tace" bilkisu to ki shigo da abincin nan mana ko kin tarar da wani a falon.

BILKISU ce tace"eaa naga khairat na kokarin fita, jinjina kai hajiya tayi tace"eaa ai daga nan ta ke tana sauri ne shisa da tace min zata biya ashe da rabon ma zaku hadu, shikenan ai.

Hajiya wannan ita ce sajidar, ta na tambaya hadi da kallon sajida da take kallonta tin maganarta ta farko, sajida ce ta kara kallonta sannan ta juya kai tana kallon hajiya.

Hakiya ce tace"sajida kin tashi to jeki bandaki ki dauro alwala kinji, bata iya magana ba ta mike domin ta dauro alwala.

Hajiya ce tace"bilkisu bari dan allah idan ta fito sai ku tafi nasan yau b makaranta sai su zauna da su samiha ko zata dan warware, saboda
yanayin ta bata saba da mu ba sai a hankali, bilkisu ce tace"to shikenan hajiya dik yadda kikace ai hakan za ai, bata gama rufe bakinta ba ta fito tana kallonsu.

Sallah ta gabatar sannan ta gaishe su cikin dakusassiyar murya, bilkisu ce tace"to sajeeda taso mutafi akwai su amra sai ku zauna kuyi wasa da su ko, da kyar tace"toh sannan ta mike tana kallon jikinta, a ranta tace"jebeni dik nayi dauda kamar bani ba.

Fita sukayi daidai nan suka hadu da aminullah yana sakkowa zuwa dining, ganin maman amra yasa shi tsugunnawa ya gaisheta, faram faram ta amsa, kallon sajida yayi yace"sannunki ya jikin, da sauri tace"ina kwana jiki alhamdulillah, ganin yadda ta basa amsar ne da gaggawa yasa shi sakin murmushi kawai ya bude flask domin yayi breakfast.

A can kuwa bangaren maman amra suna shiga taga 'yammata su biyu kansu daya, gaba dayan su zasu yi kai daya da sajida sai dai da gani ta girmesu, kuma ta fisu kyau dik da dai ba laigi suma da kyansu.

Samiha ce ta mike tace"laa mama tre da ita kuka taho, jiya da yamma da mukaje hajiya haka tace bazamu ganta ba amma kuma yau harta baki ita, bilkisu ce tace"to sarkin 'yan magana wato ke allahn da yayi ki bakinki baya shiru ko, ba kamar amrah ba.

Wadda aka kira da amra ce tai murmushi ta kau da kanta, domin haka kawai yau takeji bata son yin magana, zama sukayi sannan mama ta kallesu tace"samiha kodan ma amra kin fita hankali idan mungama breakfast kuje sai tai wanka ki bata kaya t
a saka.

Yatsina face amrah tayi tace"to mama ita din wacece haka kawai ni bansanta ba, nifa mama tinda na ganta kawai naji batayi min ba, nifa allah banasonta sam bana kuma kaunarta, domin kina ganinta kinga zubin aljanu allah mama na tsaneta.

Tsawar da mama ta daka mata ne yasata dakatawa da fadin"baki da hankali amra ke wace irin shashasha ce, a gabanta zaki ce kin tsaneta, kuka amra ta saka hadi da tashi ta wuce room dinta.

Samiha ce tace"mama ni ki kawo ta kawai basai muje ba kawai dama amrah tin ranar data ganta tace min ita ta tsaneta wai bata sonta, kuma ita daka tar da ita bilkisu tayi tana fadin'to fadi ba a tambayeki ba ki rufe min baki kuje kui breakfast ni bara naje na lallasheta tin kafin ta fara min halin nata.

Ita dai sajeeda ta zama 'yar kallo domin abin mamaki ya bata, dama a ranta tasan ba kowa ne zai ganta yace yana Sonta ba da wannan ta bar zancen ta mike domin bin bayan samiha.
**************__***************
Gaba dayan suna jere suke akan dining area daddy ne ya dubi ummulkhair yace"amma yau ba fita ko ummulkhair, kallonsa tayi tace"eaa daddy dama sai nan da wani week din zan fita kasan ana bikin kawata maryam ko, 'yar gidan katseta mum tayi tace"kedai badai surutu ba, wai ba' yar gidan senator hafeez ba, da sauri ta daga kai.

Mum ce tace"allah ya bada zaman lafiya saura ke ai tinda sa'anninki sai aure suke ko, kallonta tayi idanunta suka ciko da hawaye, lokaci daya ta rikice ta zama kamar ba ummulkhair ba, hawaye ne ke zuba a idanunta, cikin muryar kuka tace"mum bazan auri kowa ba sai muhammad koda kuwa baya so na ni shi nakeso.

Mum ce tace"shittt ki min shiru banason zancen banza, ke wace irin yarinya ce mara zuciya, dik abinda Muhammad ya miki amma har yanzu kina makale dashi, tsawon shekaru3 kenan amma kinkasa gano cewa yaudararki yayi.

Daddy ne yayi saurin katse mum yace"ya isa dan allah, daughter tasowa yayi yana shirin zuwa inda take, da sauri ta mike ta bar falon kallon mum yayi yace"to yanzu wa gari ya waya jiddah yanzu kalli abinda ya faru, kin riga kinsan yarinyar nan bata da lafiya.

Jiddah ce tace"alhaji ba dole na mata magana ba, lamari na khair ya fara yawa haka zalika ya fara bani tsoro, yanzu ace yarinya ta kekashe kasa ita dole sai wamda yace amanarta shi take so, yaushe khair zatai hankali a kalla yanzu wajen 24 year ne watan jibi zata shiga ta 25 amma kullin bata da zance sai na muhammad haba alhaji a duba lamarin nan.

Mannal ce ta kalli hannah mikewa sukai suka fice daga falon duka wuce dakinsu, mum taci gaba da fada yanzu kalli twince gaba dayansu shekarun su 18 har an fara neman auren su, amma ita ta tsaya ta makale akan wannan mayataccen da baisan tanayi ba.

Daddy sanin halin mum idan tana fada yasa shi bai mata magana ba, tashi yayi ya tafi dakin khair knocking yake amma a banza anki a bude, sai shashshakar kuka sama2 da taje tashi, ganin bazata bude ba yasa shi wucewa dakinsa.
_____________+++++++_____________
A yayin da jirginsu ya sauka a kasar india fitowa yayi fuskar nan a murtuke kamar bai taba fara'a ba, motace kirar glk ta tsaya a gabansa bayan ya fito da tantancewa.

Shiga yayi ya bar filin jirgin, har yanzu book din daya dakko a dakin dareib yana hannunsa yana kuma juya book din, domin wannan littafin yasanshi tin kafin ya bar kasa nigeria.

Wani katafaren hotel ya sauka, masu aikin ne suka dkko masa kayansa sannan ya huce zuwa room din daya tanada ta yanar gizo, a dakin suka ajiye masa kayan sannan suka juya.

Rufewa yayi ya huce zuwa toilet domin yin wanka, bai dau lokaci ba ya fito hadi da yin sallah sannan ya fara jero addu'o'i, wayarsa ya janyo bayan ya saka wata riga da wando harder, cikin yaren hindu yace"bai farka ba, shikenan nagode.

Ajiye wayar yayi ya janyo diaryn shafin farko ya bude anan yaga wani rubutu da red biro, an saka MAFARIN RAYUWAR MU, Da mamaki aryan ya kalli rubutun, shafi na 2 hoton wata mata ce, kyakkyawa mai matukar kyau babba ce zatakai a kalla 40 to above, sanye take da bakar doguwar riga tana dariya aka dauketa, shafa hoton aryan yayi yace"nayi kewarki ammieh ubangiji ya sakaki a aljannarsa.

Kubiyini da ruwan like da comment
Domin jin labarin yadda zai kasance.

Ni ce taku
Queen Waleedah
Matar uncle.

Don't forget
Dedicated to
Fatima Y Zakariyyah
Mrs J /Oum ameerah
FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
SHATU GRAPHICS DESIGN
We make any kinds of graphics design like.
Chapter 11 · 0% Book details