Sashe 21
Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau azzahra tinda ta tashi take jin jikinta da zafi, ko wankan ma bata samu yiwa noor ba, haka kuma tana kallon kiran papa amma bata daga ba, tana cikin bargo ummieh ta shigo tace"sajeedah ki tashi kici ko abinci ne, shiru taji tayi, shiru tayi sai kuma ta karasa ta yaye mata bargon, gaba daya bata motsi ga jikin ya dauki wani zafi kamar tafasasshen ruwa.
Da sauri ta kwalawa mannal kira, nan fa suka fara kokarib sa mata ruwa amma ko motsi, ganin jikin ya kara tsananta yasa ummieh fadin"kira min family doctor, hanna ce ta dauki wayar ummieh ta fara kokarin kiransa, bai dauki wasu mintuna ba ya iso.
Dubata yake yayin da dik suna tsaye suna kallon yanayin jikin nata, doctor aliyu ne ya dago yace"hajiya a gaskia kara kawai ku dauketa ku kaita wajen malam domin wannan abin sai dai malam, domin ni dik gwajin da nai komai dai dai yake bani, mamaki ne fall ran ummieh daga nan sukai sallama da aliyu.
Yana fita ita kuma tana kiran limamin masallacin dayake sallah a unguwar, kasancewar baya nan yaje unguwa ya dan tsaya, yayin da gidan kuma kowa yana zaune yana jiran malam.
Sallamar da akayi ce yasasu dagowa, malam ne ya shigo, bayan dik wata gaisuwa anan aka gabatar masa da sajidah,malam yana kallonta yayi murmushi yace"a kawo min ruwa mannal ce ta mike taje ta bude fridge ta kawo ruwan, bayan ta ajiye ne yace a dakko masa roba.
Ruwan ya juye a roba sanan ya dauki carbinsa ya fara ja yana mai ambaton allah, ya dan dauki a wanni sannan ya kalli ruwan ya tofa a ciki, yayi haka ya kai sau 3 sannan ya dauki ruwan ya watsa mata.
Wani gurnani ne ya fara fitowa, yayin da dskin ya dauki rawa, wata murya ce mai kauri da ban tsoro ta fara fadin, malam daka kyale mu ma tafiya zamuyi domin mungama aikin mu, aikin mu ya kare.
Malamn ne yace"wane irin aiki kuma, dariya ce ta karade falon sannan kuma yace"a ka'idar aikina bana fadar abinda nayi amma idan kunason kuji dik wani abu da ya faru ku hanzarta zuwa gwagwalada wajen sahura wadda tai accident jiya, gaban kowa ne ya shiga faduwa sannan take kuma aka ji tsitt ba motsn komai, ummieh ce ta ja mayafinta, sannnan ta kalli daddy tace"yakamata muje dama bamu san ko wacece wannan yarinyar ba, kaga kuwa tinda mun samu inda zamuji sai muje naji an ambaci sarkin shaidanci wato sahura, gaba daya falon na'am sukayi da maganar, sajidah ce ta motsa daga kwancen da take idanunta jajir ba wanda yace da ita komai domin ita kanta tasan a yau ta samu canji na tsawon watanni,ba 6ata lokaci s daga nan suka fito sai asibitin wajen sahura.
Inna ce a zaune a fili take ihun wai ku yaran nan bazaku ta6a dai na fada ba, Mariya ce ta juyo tace"wallahi inna kika kara nin magana sai na kasheki uban kowa ya huta, inna ta fashe da kuka dai dai lokacin dayyabu ya shigo kallon dayyabu tayi tace"lalle dayyabu ka tara 'yan iskan yara masa mutunci, yanzu ni mariya zata ce zata kashe, dayyabu ne ya zaburo.
Mariya ce tace"aa baba tsaya, gefen zanenta ta bude ta dakko 1k ta mika masa tace"gashi nan na fanshi kaina, dayyabu ya yake hakora ya huce yana fadin "ko banza na samu nacin abinci, daga nan ya fice.
Inna ce ta fashe da kuka tace" shikanan nima dan iskan son abin duniya ta kenna, gaskia sahura kin cuceni allah ya isa tsakani na dake, yanzu kina ina, allah ya isa sai kuka, yaran gidan nan suka taru a kofar dakin nata ne suka dakko kwanuka suna bugawa suna mata kida, nan fa inna ta ture ta fara wulla dik wani abu daya ke hannunta..
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
Shatu Graphix
Matar Uncle
No:-08067574868
Page 57&58
Ummy ce ta shigo tace "daddy sabra fa tana wajen 'yan sanda kuma an kira wayarka baka dauka ba, kallonta yayi sai kuma yace" nasani ai kuma ni bazan shiga abinda ba ruwa na ba, domin diik abinda mutum yayi shi ya janyowa kansa, ummy ce ta kallesa tace"daddy me tayi, bai kalleta ba yace"wani ta harba da bindiga a hannu, anci sa'a ma bai mutu ba, an tambaye ta an tambayeta amma taki magana, taki fadin a ina ta samo gun.
Ummy zatayi magana ta fasa hango kyawawan samari guda 3 kara murza idanunta tayi ganin kamar su yah dareb ne yasata kwasa da gudu, sai da ta dan tsaya sannan ta karasa hade da gaishe su bayan rungumar da tayi musu, zo kaga farinciki wajen ummi ta rasa wazata tsaya, ita kanta yau tayi mamaki ganin aryan yau fuska ba yabo ba fallasa.
Mota suka shiga yayin da driver ke jansu, basu tsaya ko ina ba sai asibitin d sahura take ciki, ba wanda yace da wani komai haka suka fito bayan driver yayi parking.
A can kuwa dakin da sahura take kallon safina tayi tace"ina ummy kuwa, bata gama rufe bakinta ba taji wata murya mara dadin sauraro ta babbake da wata iriyar dariya, take gabanta ya fadi a hankali ta furta "boka kati hakuri karka tonamin asiri, maimakon dariyar ta tsaya sai ci gaba yayi da fadin" ki tabbata yau kin gama domin kin karya dokarmu, dik kuwa wanda ya karya dokarmu karshen sa bayayin kyau, ita dai safina t tsaya domin ji tayi mahaifiyar tasu na wani surutai, a daidai lokacin daddy ya shigo.
Safina idanunta sun rufe da gudu ta tari daddy tana nuna masa halin da mahaifiyar tasu ke ciki,affaaan ne yace bara na kira likita, dakatar dshi daddy yayi yace"wananna ba maganin likita bane, abinda ta shuka take girba, ka kyaleta domin kuwa da mun zauna komai zai dawo daidai.
Rufe bakin sa kenan boka ya bayyana a matsayun suffarsa cikin shigar kayan fata, kallon sa daddy yayi, aryan dareib affan safina da ummy ba wanda bai tsorata va, bokan ne yace "karkuji tsoro na domin nazo ne domin na fede abinda wannan matsiyaviyar matar ta aikata, da fari ku bani mintuna 2,a wannan lokacin ya 6ace,yayin da aka bar sahura na 6arin hawaye ita ala dole tayi nadama, a haka da zaka duba kwayar idanunta ba wata nadama a yanda na lura amma bansani ba ko da gasken tayi.
Kowa na dakin shiru yayi yana sauraron zuwan dr, sallamar da akayi ce yasa su kallon kofa, idanun azzahra ne suka kai kan na dareib da affaan,kallonsu take cike da mamaki yayin da suma din ita suke kallo, dareib ya matso ya kamo hannunta yana fadin "daddy ka ganeta wanann fa azzahra ce bakuwar mu wadda muka nemeta muka rasa, da mamaki take kallonsa tace" yaah dareib ina ciwon naka, lokacin da zan tafi an fada min cewa kayi accident yaya kaji sauki kenna.
Murmushi yayi mata yace"karki damu azzahra komai yana lafiya ai yaci ace na warke tunda akalla yau kimanin wata 2 kenan, zaro ido tayi tana mamakin kwanakin, a wannan lokacin ne boka ya bayyana yaba fadin hajiya ummieh da kuma kai alhaji hafeez, hajiya bulkisu, malam sannunku da zuwa, sannunku domin nasan kunzo nan domin jin gaskia.
A can gida kuwa mannal, hannah, samiha sai amra suna zaune sun zabga uban tagumi, mannal ce taji shirun ya isheta,kallon amrah tayi tace"wai nikam amrah yaushe kika dawo bayan sajida har kike kaunarta, amrah ce ta nisa sannan ta mike tace"wannan kuma ki tambayi samiha ai tasan komai tinda kinga mu twince ne, hannace ta saka dariya domin ta gano jirgin, samiha ce tai saurin cewa wallahi amra karya kike min nidai bansan anyi ba.
Ganin abin zaiyi yawa yasa amra fadin ku taso mu tafi part din yayah dan kunsan baya nan, dan naga mutanen gidan nan bazasu dawo a yanzu ba.samiha ce tace"ayrah nifa wallahi ba ruwa na da haka dama party mukayi kawai, suna shirin mikewa call ya shigo wayar samiha, dubawa tayi ganin khair yasa ta fadin "ku kutaho aunty khair ce nasan tyi missing din mu dan ma babu sauran.
Boka ne ya kyalkyale da dariya malam ne yayi kokarin dakatar dashi amma sai boka ya tsayar da malam da fadin cewa, "kai ba sai ka tsayar dani ba domin nazone domin na fada muku gaskia, wani waje ya nuna take wata halitta ta bayyana a wajen, da mamaki suka fara kallon wajen, ba kowa bace face wata dattijuwar mata cikin bakar doguwar riga yayin da gashin kanta yake a warwaje.
Dareib, aryaan, daddy kowa ya zuba ido,gaba daya falon kamar an hada baki suka furta, Ammah ce ai, daddy ya fara kiran sunan ta, khadija, khadija, mma shiru, sahura cike da 6acin rai tace"sam boka bakamin adalci ba, ashe dama baka kashe khadija ba, she dik tsawon wannan sgekarun baka kasheta ba,kowa zaro ido yayi yana kallonta, domin a yanzu sun gasgata abinnda kunensu yake ji.
Boka ne ya kallesu yace"to kunji da kunnenku, a yanzu nadawo da ita amma kuma ku sani cewa tabbas zan dauki fansar abinda wannan mata ta aikata ba dan haka kuyi hakuri domin a yanzu zan tafi da ita can inda bawanda ta sani ko kuma ya santa, malam ne ya kallesa yace"karka sake ka ta6a komai har sai ka bamu labarin abinda ya faru na tsawon shekara 10 domin munason jin abinda wannan baiwar allah tayi maka har ka aikata mata wannan aikin.
Boka ne yace"karka tamvayeni domin ni bazan fada maka komai ba sai dai zan bawa sahura dama domin ta fada muku abinda ta aikata da bakinta.
Daganan ya kalle ta take bakinta ya fara karkarwa.