← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunzo wucewa ne aminullah ne ya hangesu, kwala kiran samiha yayi, juyawa tayi zata tafi ita kuma azzahra ta wuce ciki domin ita batasan kallo, hakanma dik a takure take ganin jama'a sunyi yawa matuka a gidan, shigarta falon taji wata muryar namiji na magana, bata daga kai ba sai ji tai ance sajeedah, ba wata bace khair ce ke kiranta, karasawa tayi.

Khair ce tace"dan allah jeki kitchen ki dakko min abinci, toh tace sannna ta mika mata noor taxe"dan allah ajiye sa na dawo, ganin yana bacci yasa khair karbarsa, wucewa tayi a ranta tace"amma lallen nan yayi kyau, bata dade ba ta dawo da katon plate da abinci, ajiyewa tayi a table din gabanta sanan tace"gashi aunty kokarin daukar sa tayi kanta a tsugunne, mamaki ne ya cika khalel daya ke zaune a ransa yace kamar nasan wannan face din,ita kam hucewa tayi tana shiga daki noor na farkawa.

Bata dade da shiga ba ta fito tai hanyar kitchen, khalel ne ya tashi yabi bayanta ba tare da kowa ya sani ba, abinci ta zubo sannan tazo zata fice ganin mutum a bakin hanya yasata saurim daga kai, take idaninsu suka hade nan suka fara kallon kallo,janye idanunta tayi zuciyarta na bugawa da sauri, ahmad ne yazo shigewa yaga khalel ya kura mata idanu, dafasa yayi firgigit ya dawo dai dai, sannan ya jasa zuwa dakinsa daya ke part din su.

Bata damu b yana wuce wa tai daki ta fara bawa noor abincin itama tana ci, jin kamar ana kallonta ne yasa ta dagowa ba kowa bane nuraddeeen ne ya kalleta, noor ne ya kallesa yace papa, murmushi nuradeen yayi ya baza hannu da gudu ya dafe sa yana dariya, kallon yarin yake a sati daya jibi yadda ya warware, sosai yayi kiba, yadda baiyi tinani ba, zama yayi a kan gadon yayin da Azzahra take a takure kamar ace arr ta gudu, dik hirar da suke tana jinsu amma ta kasa magana.

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
FATEEMAH Y ZAKARIYYAH
Oum ameerah
Follow on Arewabooks@MatarUncle
Follow on Wattpad@mataruncle
08067574868
37&38
Noor ya kalla yace "boi an maka wanka kuwa, noor ne yace" papa tayi min wanka dazu,papa munje saloon da aunty sajeeda bata ankara ba bata ji lokacin daya sakko ba kawai ji tayi an zare mata mayafin kanta take gashin ta wanda yasha gyara ya bayyana, da sauri ta dago ta kallesa tana fadin"aa noor meye haka kuma, idanunsu ne suka hade a waje daya shi kuma noor da gudu ya shige toilet yana dariya.

Sun dau mintuna sannan sajeedah tai saurin janye idanunta daga idanunsa, bata ankara ba taji noor yana dariya daga toilet can kuma yace"paoa duba kagani harda lalle tayi, mikewa yayi yana murmushi ln gefen baki yaja hannun noor har zai fita ya juyo yace"bani kayansa zamu shirya kuma kema ki shirya tare zan kaiku.

Mikewa tayi ta karasa bakin wardrobe budewa tayi sai kuma tace"ai bansan kayan da za'a saka yau ba, karasawa yayi ya janyo wasu sabbin 'yan kanti masu matukar daukar hankali kallo daya kasan kayan ba na nan kasa nigeria bane, kallon kayan ya tsaya yi sai kuma yace"ki saka wannan orange din, fitowa yayi ya huce dakinsa yana hira da noor.

Da shigarsa ya rufe kofar hadi da saka lock, noor ya kalla yace"baby zauna anan, zakaci abinci, cikin maganarsa yace" papa aunty ta bani abinci kuma na koshi, daga haka ya girgixa kai ya kishingida akan gadonsa,lumshe idanunsa yayi sannan ya budesu ya kara lumshe wa ba komai yake gani ba sai tsantsar kyau irin na sajeeda, lalle ubangiji ya tsara wannan halitta a jikin wannan yarinyar, bude idanu yayi yana murmushi sai kuma ya kalli noor dayake game a wayarsa.

Kallon kayan yayi sai a lokacin ma ya tina da kayan daya gani na sajeeda a ransa yace"allah sarki saidai bata da kaya dika kayan da kala nawa ne, kuma dole nai wani abu akan wannan lamarin, hannunsa ya dora kan saitin zuciyarsa yace"tabbas ina sonta, noor ne yace" papa nima inason aunty tsaya kaji karatun da take koyamin, nan ya fara rera karatu, mamaki ne ya cika ran nuraddeen ya tabbata ko a gaban mahaifiyarsa yake bazai iya wannan karatun ba.

A can kuwa bayan ya fita kayan dayace za'a saka su ta kalla tai murmushi da murna tace"allah har na matsu nasaka kayan nan domin nasan zan saka sabbin kaya, shigowar samiha ce ta kalleta tace"wai me kike jira ne sajeedah har yanzu baki shiga wanka ba kin tsaya sai nuku nukutu kikeyi, dan allah ki hanzarta ki shiga karkija mu makara, kowa fa ya shirya.

Ummulkhair ce a kusa da amarya khairat sai fadila sai tsokanarta suke yi ita kam tayi shiru tana kallonsu, fadila ce tace"to ni khair na rasa ya abin nan zai kasance iya wadanda sukai anko ne zasuyi karatu ko kuwa, kallonta Ummulkhair tayi da murmushi tace"eaa mana iya wadanda suka saka wannan orange din abin sune zasuyi karatu, jin karar waya ne yasa kowa kallon screen din wayar amarya, ganin ansaka mrs khairat yasa su fadin"eyeeee wato ango ne wannan da alama kam ya matsu a dan jima ko, ita dai bata kula su ba ta dauki wayarta, sauran kawayen ne guda 5 suka saka dariya, harda shewa.

Tana katsewa tace"to sai ku taso ai tinda dik yawanci al'umar gidan sun fice sai mu kadai ne kuma sai munje za'a fara saboda..

Bata karasa ba wata kawarta tace"nima dai na matsu a tafi, fadila ce tace"nifa wallahi aseeya dadina dake gaggawa dole ai sai mun jira time.

AFTER 30 MINUTES
Gaba daya gidan ba kowa sai iyaye da 'yan uwa, a dakin nuradeeen kuwa fess suka fito shi da yaronsa wanda sai a yanzu ne ma naga matukar kamarsu kamar an tsaga kara,fitowa sukayi sukai zuwa falon sa, noor ne ya kallesa yace" papa aunty tana dakinta tace idan ka shirya ni naje mu tafi, da to ya bishi sannan ya fito a kofar dakin ya kyalesa shi kuma ya wuce.

Sanye take da orange din material din dayaci dinki riga ce mai kyau, wadda tai matukar karbar material din, sai kuma black din veil datai rolling dashi, ta saka takalmi baki, a tsaye a gaban mudubi noor ya hangeta, da gudu ya karasa wajenta, jin Turaren sa ne yasata juyowa tana dariya, sai kuma ta hade rai taxe" sai yanzu zaka zo dubi ba kowa, kasan idan bamu samu kowa ba sai dai mu hakura da zuwa ko.

Noor ne yace" kiyi hakuri aunty papa ne bai shiryani da wuri ba kuma na fada masa cewa zasu iya tafiya, sai yace"dama so yake su tafi din, murmushi sajida tayi ta kawar da kanta daga zancen sannan ta mike ta fito, iya rungumar da tayi masa ne turaren jikinsa ya ya kama jikinta.

Harabar gidan ba kowa, dubawa tayi amma bata ga kowa ba, kallon noor tayi tace"munyi late kaga sai mu fasa zuwa ko,noor ne ya tabe baki yaxe"amma aunty nace fa zanyi karatu ko, a hankali ta tsugunno gabansa tace"muje sai kai a daki kaga ba kowa a gidan ko boy.

Wata mota ce tai horn noor da murna yace" papa ne, hangawa yayi ya hangosa, kama hannunta yayi yafara janta, har bakin motar sannan suka tsaya, nuradeeen ya juyar da fuskarsa ga boy yace"to kacewa auntyn ta shigo mu tafi ko, juyawa yayi ya kalli sajeeda yace"tohmm muje ko aunty, daga nan suka shiga suka bar gidan.

Tafiya suke a saman titi, cikin abinda bai fi mint 20 ba suka shigo filin, gaba daya filin komai a nutse yake, noor ne yace"to papa amma ka tsaya ka tafi damu, lakuce masa hanci yayi yace"aa boy zan tafi wani aiki ne amma idan na dawo da wuri zandawo kaji, murmushi yayi masa, fitarsu shi kuma wayarsa ta fara ruri.

Shiga sukai tin daga nesa kallo ya koma kansu,noor ne yaje ya tsaya yana kallon mai yin karatun wata babba ce take karatu cikin suratul an'am, amra ce ta hangi sajeeda ganin tayi mata kyau ne yasata jan dogin tsaki tace"ita kuma wannan ballagazar in ata samu kaya irin namu, ni banason wannan sakarcin, wata kawarta ce tace"amrah ina kuka samu wannan kykkyawar a gidanku kodai ahalinku ce, tabe baki tayi ta juya mata keya.

Zama sukayi Samiha ce ta zagayo wajenta tace"ke yanzu sai da kika tsaya noor, kallon noor din tayi tace"kai dai kam ka tsayar da ita da yawa, sai fara surutu ne dajida tace"shitt bana hanaka idan ana karatu ba'a surutu ko, tasan idan ya fara magana to zai dade bai daina ba.

Kallon wajen tayi wajen ya hadu da kujeru na alfarma, can gefe ango da amarya ne cikin shigar fararen kaya sunyi kyau kamar ka sace su ka gudu, kusa da su wata katuwar shimfida ce yayin da wata a kan kujera take karatu.Sai sauran dining din mai guda 4 ko ina da abinci da lemo na alfarma, kayan ciyeciye ne gasu nan birjik.

Baya da kamar mint 5 budurwar ta sakko daga kujerar, da sauri amrah ta karbi abin maganar tace"alhamdulillah allah ya saka da alkhairy to yanzu kuma sajeeda ce zata cigaba da karatun, ita kanta sai da kirjinta ya buga yayin da kallo ya koma kanta,yawancin mutanen wajen ba abinda suke furtawa sai masha allah, wannan kyakkyawar kuma fa.

Tasowar ta yasa tai tozali da fadila tana kallonta, take ta fara tino a inda ta santa sai kuma khalil da gaba daya hankalinsa na kanta, noor ne ya biyota a baya yana kallon mutanen wajen, gefe daya kuma na hangi shugaban a kan kujera yana kallon wajen nikam nace to ina uzurin nasa.
Chapter 14 · 0% Book details