Sashe 2
Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gida ta shiga ta fara jero kira wajen azzahra badan taso ba ta fito tace "inna gani, inna ce ta kalli kudi tace" fati maza kije wancan dan albarkan yana jiranki, badan taso ba ta tafi tana zuwa ta iske shi, bakin kofar zaure ta tsaya tana raba ido, a hankali yace "kuma ki tabbata kinzo idan ba haka ba kinsan sauran, a hankali tace" bazanzo ba kuma kasan allah ban zuwa, cike da rashin gane maganar yace "me kikace ran nan a hade kamar bai taba dariya ba..
Cike da dauriya tace" tohm zanzo, saurayin ne yace ki shirya karfe 9 za a zo a dauke ki daga haka ya juya ya koma motar sa daga nan suka bar unguwar.
Fati na shigowa inna tace "amma dai fati zaki fara zuwa aikin nan, shiru tayi inna ce tace" wai fati ba magana nake miki ba, da sauri tace "eaa zanje.
Inna mamaki take dama zata iya rike wadan nan makudan kudaden haka masu matukar yawa a rayuwarta.
Azzahra abinci take ci tana tinanin farkon abinda ya fara shiga tsakanin ta da wannan saurayin da bata taba ganin face dinsa ba sai yau.
*FLASH BACK*
_THURSDAY_
Dauke take da robar tuwon tana zaune wajen sana'arta, wani dan saurayi ne yace "azzahra kawo min tuwo na 500, sai da ta zuba tazo tsallakawa ne,wasu jerin motoci suka taho saura kadan su bigeta, hakan yasa sauran securityn sauka, da farko fada yake, amma dataji yace" sorry sir ya tabbatar mata da ea shi ma umarni yake karba, hakuri ya fara bata, a hankali azzahra tace "bakomai kawai ni ma ai laifina ne ban kalli gaba na ba shikenan kuzo ku huce.
Tin daga wannan ranar kullun sai sun wuce a kalla yau kimanin wata 4 kenan indai yazo hucewa yakan bata kudin tuwon yace" ta raba wa mabuqata sannan ta tafi gida, a yau shi ne tagaji har ta nuna fushinta.
Kiran inna ne ya dawi da ita tace "fati wai nikam a ina kikasan wannan saurayin, azzahra ce tace" nima inna bansani ba amma yau na fara ganinsa, yake hakora inna tayi tace "kai amma allah ubangini yayi wa wannaj yaro albarka, kinga kenan sai na ruguje wannna yar banzar katangar na gyara, bata kulata ba zata mike taji kudin dazu, a hankali tace" inna ga cinikin tuwonki wadan nan kuma shi ya bani wai na rike nikam inna banaso na bar miki, washe hakora inna tayi tace "yawwa fati fatiti 'yar albarka kawo nan ni inaso, maza wuce kije ki rufe gidan dan naga dare yayi daga nan kizo ki wuce ki kwanta.
Zuwa tayi tai addua kamar yadda annabin rahama ya koya mana ta rufe, sannan taiwa inna sallama ta wuce dakin ta, a wata" yar karamar tabar ma take a kwance.
Gaba daya tinani take, to shi wannan saurayin wanene, a ina yasan ta, ya sunansa, shin dagaske wannan company nasa ne ko kuma dai kawai karya yake mata.
Da wannan ta samu bacci ya dauketa, cijin baccin ne taga al'ameen yana daga mata hannu hadi da murmushi yace "azzahra karki manta da ni karki tafi ki barni kinsan ina sonki, firgigit ta mike tana murza idanu, yanayin bugun zuciyarta ne ya karu, salin alin ta mike ta dauro alwala sannan ta dawo ta fara jero addu'o'i.
*FATEEMAH ZAHRA*
Written by
A'ishatu Bint Muhammad
Matar uncle /Queen Waleedah
Zinariyar Nazari Writers Association
NAZARI WRITERS ASSOCIATION
_Kyawawan Nazari kafin rubutu na
amfare da bin
a'idojin rubutu._
_Cikakken Nazari kafin rubutu kan
ayata duniyar Adabin hausa._
Alkalami yafi takobi
Dedicated to
Fateemah Y Zakariyyah (Oum Ameerah)
Marubuciyar Ahalin Mu Daya
And Idan So Cuta Ne
Episodes 5&6
Da sayin safiya ta fara kokarin hada 'yan kayan wanke wanke, wanke su tayi tsaf ta kife, sannan ta fara shara da sharce inda ruwa ya kwanta.
Sai wajen 7 inna ta fito, wata katuwar randar goro ce kan kace kwabonta cikata da kunu, kallon azzahra tayi tace "tohm maza ki wuce kije ki dauka kuma banason shashanci, kuma kinsan dai zakije aiki ofishin wannnan dan albarkan ko, bata ko bata amsa ba ta wuce nemo wanda zai daukar mata, da harara inna ta bita tace" shegiya ina miki magana kina banza dani sai naci jakar ubanki.
Bata dade da zama a wajen kunun ba, ya kare dan haka ta fara hada robobin, wanda ya kawo mata ne tace"sale dan allah ka maida su gida idan inna ta tambayela kace na tafi na amso sauran kudina, sale da toh ya amsa ya wuce.
Wani layi naga ta yanka tana ta tafiya, sauri take sosai, dai dai wani gida naga ta tsaya gida ne madaidaici na ginin bulo d bulo, da sallama ta shiga amma ba'a amsa ba sai can ta amsa, shiga tayi wata dattijuwar mata ce ta leko tace "aa yau kuma zahra ce a gidan nawa, to bissmillah shigo.
A hankali ta karasa kusa da matar tana yar fara kadan, gaishe ta tayi ta amsa cikin sakin fuska, azzahra ce tace" dama nga kwana 2 al'ameen bangansa ba ne tin jiya shiyasa na biyo naji ko lafiya, da murmushi dattijuwar tace"ina zuwa, dakinta ta shiga bata dauki wani dogon lokaci ba ta fito da takarda a hannunta, mikawa azzahra tayi tace"to wannan inji al'ameen yace idan kinzo na baki, karba tayi ta tsaya jimami sai kuma ta mike tace"to baabah ni zan koma sai anjima, daga nan sukai sallama ta bar gida.
Tin daga kofar gidansu idanunta suke hango mata wata mota black color, karasawa tayi anan naga ashe kirar honda ce sai kyalli take, kana gani kasan sabuwa ce.
Security ne ya fito yace"madam ke ake jira a company, kallinsa tayi tace "to ni kuma nayi muku me bayan ni 'yar goge goge ce kawai, a hankali ya furta" aa madam karki saurin yanke hukunci domin haka kizo mu tafi.
Dan karamin tsaki taja tace"kai ni dan allah karka dameni kaje kawai zanzo ai nasan hanya, tafiya tqyi tana fadin"shima wannan MD din ya cikw fitina ina ruwansa da ni har zai wani turo min da mota sai kace an ce masa bani da kudi, abin ne ya bani mamaki a fili na furta 'ohhh su azzahra an samu waje ai shikenan.
Shiga gidan tayi tin daga zauren gidan take jiyo ihun inna tana fada, a hankali ta furta kai wannaj tsohuwar akwai fitina, sai kuma naji tayi saurin kama bakinta tana leke.
A tsaye ta tarar da ita shigarta kenan ta fara fada tana cewa"ke yanzu gani kikayi kinyi daidai ko fati yanzu ga wannan alhajin ya turo da fyalleliyar mota azo a daukeki har gida amma shi ne kika tafi yawonki ko.
Azzahra ce ta turo baki tace"to inna ya kikeso nayi yanzu idan na baro miki kudi a wajen mutane kiyi tayi min fada, nabi ina karbowa ma ban tsira ba, inna ce tace "naji toh yanzu dai miko kudi jeki ki sanjo hijabi kizo ki huce, da sauri ta kalleta tace" to inna kenan bazan yi wanka ba, kuma bazanci abinci ba, inna dai tinanin kudin jiya ya hanata sakat dan haka da sauri tace"to shikenan maza jeki ki wankan nan kizo ki cuccusa gurasar nan, nifa na kagu naga kin tafi, yadda kikasan ni zan haye wanga motar.
Bata dauki mintuna masu yawa ba har ta fito a shirye sanye take da wani milk din hijab, hakan ne yasa nayi tinanin sabo ne a kayanta domin ban taba ganinta da shi ba, gashi sai wani kyalli yakeyi.
Inna tayiwa saallam ta fito, inna tsabar zumudi harda rakata waje, abinda ya bawa azzahra mamaki shi ne har zuwa wannan lokacin securityn da drivern suna nan suna jiranta, dan haka ta shiga daga nan suka dauki hanyar su ta SADDAM AND BROTHERS.
Zaune yake a katafaren office dinsa, wanda kamshinsa ke fitar da kamshin airfreshner na swiss flower, wata katuwar television ce keyi yayin da hankalinsa ke kan laptop dinsa, wani kira ne ya shigo dan haka yayi saurin dagawa hadi da furta, Good day bro, na kasa hango dayan dik iya leken leken da nakeyi haka na hakura na juya na dawo, banji me suke fadi ba daga haka ya katse ya mike, masha allah.
Yau kuma sanye yake da riga da wando gaba dayan su sun kasance black ne sai jikin rigarne akai rubutu da blue paint wanda ya kara haska rigar, sumar kansa tasha gyara, ga wani sau ciki kirar companyn gacuzzi, fitowa yayi yana kalle kalle inda zai hango abinda yake buqata.
Parking motar tayi nan fa ta saki baki tana kallon aljannar duniya, a hankali ta furta "kar na bada kai na fateema rike kanki mana, daga haka suka cibgaba da tafiya security na gaba.
Dai dai reception ya tsya gaba daya mutanen wajen ne suka mike ba ma ta kula da su ba saida ta zauna sannan suka zauna, a hankali suka fara kallon ta, bata dade da zama ba wata mace tazo tace"an ce ki shigo ranki ya dade, kallon ko in kula ta bita dashi tace"tohmm sannna ta mike ta bi bayanta.
DAREIB COMPANY
Garin Kano ta dabo
Zaune yake yana tinanin, wani dan saurayi ne a kusa dashi ya dafasa yace"ya kamata ka rage wannan tinanin mafita muke nema, dan karamin tsayi yaja yace"Faruq kana da matsala na rasa tayaya zan iya wannan aikin amma wallahi bazan taba barin wannan fansartawa ba ta tafi a a banza domin anyi min abinda bazan taba mantawa ba, dan haka ya kamata nai hanzarin daukar mataki.