← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki tace"hukuma kuma baffah, da fadansa yace
ea hukuma kuma ki tabbatar kin isar da wannan sakon, tafiya yayi ya barta cike da tambayoyi a ranta, da kyar ta gyara zaman jakarta sannan ta shiga gidan.

Ganin ba wanda zai bata amsa ne yasata chanja kaya ta fito, chanjin hannun ta ta kalla ganin zasu isheta zuwa ne yasata tare mai nafef ta shiga, mai nafef din ne ya fara tafiya.

A ranta tace"to wai me inna take shiryawa ya za
ai ace mu da gidanmu amma ace na kai mukulli, kai ya ilahi, karar wayar me nafef ce yasata dawowa hayyacinta, cikin dan sauri tace"ya hakuri dan allah saddam and brothers zaka kaini, dan karamin tsaki yaja yace"da hajiya kinsan da cewa da can nan zaki je amma kika barni nake ta tafiya dake wallahi ko, tarar numfashinsa azzahra tayi tace"ya hakuri kaji dan allah laifi na ne.

Hafeez ne ya fito kiran farouq ne ya shigo wayarsa a hankali yace kai bazan samu dsmar shigowa school ba amma kasan mene mu hadu a club, daga haka ya katse wayar, a falo ya tarar da dad dsn tsaki yaja yace"hajiya ni na tafi sai na dawo, addu
a taci gaba da kwarara masa, daddy ne yace"kanku ake ji daga ke har yaran naki.

Affan ne ya fito sanye da riga da wando sai wayarsa kirar iPhone a hannunsa, daddy ne ya kallesa sai kuma ya mike a fili ya furta"kallesa kamar mutumin kirki, amma sai dai kashh, daga nan ya huce.

Dakinta ta zauna ta rasa wane mataki zata dauka wajen gyara alhaji domin ya fara son yaranta, amma ko ma dai mene wayarta ta dauka, banji me aka ce ba sai ji nai hajiya sahura tace"dan allah kizo akwai matsala wallahi, da sauri ta katse tana kallon screen din wayar.

Daidai lokacin daya sauketa a nafef ne ta shiga da sauri, cin karo tayi da wasu motoci a gefe daya, kallon motocin tayi sannan ta kawar da kannta gefe,office din MD tayi direct shiga tayi ganin na kowa yasata fara aikinta cikin sauri sauri, domin tasan tayi late, kamar daga sama taji kofa tayi kara, saurin juyowa tayi take ta fada jikinsa, kokarin zamewa be yasata saurin rukota yana fadin ma
Sorrie fateemah, kallonta yake can kuma ya dagata, zama yayi a kan kujerar sai kuma yace fateema zo nan.

Jikinta na rawa ta karasa ta zauna tana kallon kasa, a hankali yace"me yasameki har kin dawo daga makarantar ne, sai a lokacin tinanin khalel ya kara fado mata, dan haka tace
eaa yallabai na dawo, da wuri na fito ne shisa, kallonta yake kallon tsanaki yace
shikenan tashi kije ki gyara office din manager sai ki dawo ki gyara nawa, da sauri ta ta mike don dama jira take ya bata space ta gudu, ganin tana sauri ne ya kalleta a hankali yace"komai naki abin burgewa ne azzahra.

Bata dade da fara aikin ba taji alamun shigo wa, bata damu ba taci gaba da aikinta, fitowarta daga toilet ne yasata ganin mutum sankamkam a gabanta, da sauri ta tsaya ta fara karanto addu
ar da tazo bakinta, affan dai tsayawa yayi yana kallon ikon allah, a hankali yace"to ke da kike wannan adduar an gaya miki kama ki zanyi ne, da sauri ta girgiza kai.

Zama yayi yace"to ke me ya kawo ki nan kuma ke din wacece, da sauri tace"md ne ya aikoni na goge office din na tsaftace sa, sannan kuma sai na ganka, yallabai sir bansanka ba, amma bansani ba ko kaine mamallakin office din,dan murmushi yayi ganin wayarsa tayi haske yasakashi mikewa, ya fice bai mata magana ba.

Tin bayan fitowar ta daga office din manager, office din MD ta shiga ganin baya nan nr yasata zama, kamar wadda aka mintsina sai kuma ta mike, hanyar private room ta nifa, ganin wani inji a wajen, da gani na saka finger ne yasata jiyawa ta koma, kwanciya tayi akan kujerar office din, bata dade ba bacci yayi gaba da ita domin kuwa ta gaji matuka.

BAYAN AWA 3
DAREIB ne ya shigo dauke da file a hannunsa, kallon watch din hannunsa yayi yaga 5 tayi lokacin campanyn ba kowa sai sauran securities.

Sai da ya gama hada jakarsa kamar ance daga idanunka anan yaci kicibis da fatremah na ta sharar bacci abinta, tsayawa yana kallon tsari da zubi da allah yayiwa wannan baiwa tasa, ya dade yana kallonta fuskar nan tasa dauke da murmushi, rasa ta inda zai tashe ta yayi.

Wata dabara ce ta fado masa, wayarsa ya ciro daga aljihu kirar iPhone wani sauti ya kure cikin surar bakara aya ta karshe data biyun karshe,ya kara mata a kunne, a take tai mika tare da furta addu'ar tashi daga bacci.

Wurgigi tayi tana kallon a ina take, a lokacin ta fara gyara hijabinta da kayan jikinta tanayi tana hamma, DAREIB ne ya kalleta yace"nan wajen bacci ne dama, shiru tayi tana murza dan yatsanta, cikin dakewa yaxe"ke wai ba magana nake miki ba, da sauri ta dago ta fara girgixa kai, shikenan kawai ya furta, da sauri ta mike itama ta bar office din, fitarta shima ya fito.

Fitowa yayi bayan yayi sallama da security din ya dakko hanya, a hanya ya ganta tana ta zumbuda sauri, a fili ya furta"to ita wannan da take wannan saurin ina kudin nafef din,bai jira komai ba ya fara danna mata horn cikin kwarewa,da kamar bazata juyawa sai kuma ta juya ganin motar dareib ya isa ya saka ta gane abinda yake nufi, dan haka juyawa tayi ta shiga suka tafi, dik da a cikinsu ba wanda ya sake wa wani magana.

Tin daga kofar gidan inna azzahra ta hango dandazon al'umma, ga kuma kaya a waje, sn zubar tin kafin ya karasa take kokarin bude motar, badan allah yasa yayi lock din motar ba da sai dai wani labarin.

Cikin zafin abinds tayi masa yace"ke wai baki da hankali ne Fatima bakiga ban parking ba amma kike kokarin fita, bata kulasa ba cikin taushin mirya tace"ya hakuri nagode.

Karasowa tayi taga inna a tsaye ga kayansu fik a waje ga kuma gida an saka masa lock, inna ce tace yawwa kara da allah ya kawoki fati dama ke nake jira, ni na tattara yanawa yanawa sai allah ya sake hadamu kuma, cikin rashin fahimta Fateemah tace"kamar ya inna ni bangane ba.

Inna ce tace ya za ai ki gane, dama ke allan da yayiki kwakwalwar kifi gareki, to ki sani ni bansan ki ba, kawai dai na tsinceki ne, kuma bata karasa ba, fati ta fara jin kanta na juyawa.

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
The Stars
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
Wannan page naki ne
Billy pinky Much love
13-14
Ba ita kadai ba hatta MD sai da maganar inna ta dakesa matuka, bai gama mamaki ba yaji taci gaba da fadin
"ah toh dan haka kije ki nemi iyalinki, tsawon shekara 18 kenan da tsintarki Fateemah, dan haka a yau nima zan tattara na koma gidan yaro na domin na saida gidan nan.

" da kyar da bude baki hawaye na sintiri akan face dinta tace"kenan inna kina nufin bani da iyaye ba wanda yasan.....

Muryar tace ta rike tari ya tirnike ta, lokaci guda ta fadi a wajen ba tare da wani wadataccen numfashi a tare da ita ba.

DAREIB ne ya tsugunna yana mai riketa yana jijjigata, amma jikinta gaba daya ya saki alamu ne kamar ba rai a tare da ita.

Sauran mutanen wajen ne ke fadin gaskia hakan bai dace ba, tayaya zata fadi mata hakan.

Wata budurwa ce tace"to fa kaga shi kuma wannan da banzan fi'ili aikin banza wai shi tausayi, bai saurari abinda zasu ce ya dauketa cakk, alama yayiwa securityn daya bude masa kofa, yana budewa ya sakata sannan ya shiga ya jata sai hospital.

Anan ya bar inna a tsaye, kayan azzahra ta dauka ta bawa maman anas ajiya, a cewarta idan tazo sai ta bata kawai, ita dai bata kara zama a unguwar nan, haka ta tafi batare da wani darr a ranta ba.

A bakin hospital suka tsaya yadda ya dakko ta kadai ya isa dik wanda ya gansa a wannan lokacin zai iya zata matarsa ce, domin da sauri ya shige cikin hospital din yana kiran doctor.

Wasu nurses ne dake tsaye suka taho da sauri yayin da daya ta koma dakko gado, dorata sukayi take suka shiga da ita zuwa wani room, ruwa suka saka mata sannan suka fito, kallonsu yakeyi can ya hango doctor da sauri yana gyara rigar jikinsa wato lab court.

Yana zuwa bai tsaya wani abu ba ya shiga yafi awa 1 a ciki, wayar dareib ce take kara ganin sunan bro yasa shi kallon watch din hannunsa, domin kuwa ya manta sam bai Kirasa ba, karfe 11:00 agogon ya nuna masa.

Bai daga kiran ba yana ji tana ringing amma bai daga ba daga karshe yasakata a flight mode sannan ya koma ya zauna, bai dade da zama ba doctor din ya fito yana kallon dareib, a hankali ya furta "ka biyoni office please.

Zama sukayi doctor ne ya dubesa yace" a gaskia yarinyar nan idan a haka za'a ciga ba zata iya rasa rayuwarta, domin kuwa hawan jini ne da ita wanda a lokaci daya yayi mugun sama, dole sai dai ana kulawa da ita, sannan kuma dik wata damuwa da take ciki ayi kokari a kawar mata da damuwar, kasantuwar yanayin da take ciki, idan ba haka ba gaskia zata iya rasa rayuwarta.

Dik wannan bayanin darrib ya saurara sannan yace"to doctor yanzu yaushe za a sallameta, dan jingina kansa yayi yace"i think nan da gobe ma is ok indai jikin yayi yanda muke so.
Chapter 5 · 0% Book details