← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba daya dariya sukayi ganin suna neman juya zancen yasata saurin kawar da zancen tace"ya zakuje kai amaryan,hanna ce tace"amarya daga ita sai ango zasu tafi dan haka ba wanda zai bisu, kawai ku bari mu taki rana 1 kawai muje mu gaisa.

Samiha xe tace"da kike fadin hakan kina nufin mah anan zata barku ta koma ita kadai, dariya tayi sannan mannal tace"yo dama ai muna sane hutun semester muje dan haka muna nan sai nan da wani satin, ihu suka saka na farinciki da murna, mannal ce tace"kunga kenan ba wanda yake a problem sai ummi, dariya ummi tayi tace"ba wani problem malamai ai yanzu koda gudu sai naje gida, domin kuna tsakiya mu kuma muna karshe dan haka bani da wata matsala.

Dariya sukai gaba dayansu, nan fa hira ta chanja, samiha ce tace"ummie dan allah me yaya aminullah yayi miki haka kike wahalar mana dashi, yau na lura kusan sati 2 kenan bashi da sukuni, ummi ce ta ta6e baki tace"kadan ma kenan wallahi sai na gasa sa, ni zai wa abinda yayiwa, mannal ce tace"king aki daina wahalar da kanki domin kinsan allah bazata ta6a fada miki abinda ya hadasu ba, sai ki gaji da tambaya.

Sajida ce ta haye saman gado tace"sai kuyi tayi ni bacci ma nakeji, bata ankara ba tayi wani duka bata waigo ba tace"wallahi nasan ko wacece mannal ki kyaleni kwana 2 nan naga take takenki so kike kawai ki hanani hutawa,zata fara magana kenan wayarta ta fara ringing hannah ce tace"kuyi shiru ga mrs mannal na kira, ko kallonsu batayi ba ta tashi ta shige toilet domin tasan ta tsaya sai sun samu damar kunnata.
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
Shatu Graphix
Matar Uncle
No:-08067574868
Nazari Writers Association
51&52
AFTER TWO WEEKS
_Bayan sati biyu_
Ummieh ce zaune a falon kasa ita da hajiya suna hira, yayin da amrah da samiha suka shigo da murmushi, zama sukayi bayan sun gaisa da ummieh.

Ummieh ce tace"ohhh duba kiga dik wannan saurin da sujeyi sai dai kuka rigasu fitowa, ai hakin wadan nan yaran wallahi sai hakuri, gashi yanzu sajida tinda ta samu su mannal ita ma ta koyi shirirta irin tasu, ku tashi ku hau sama suna chan abinda ummieh ta fada kenan.

Hajiya ce tace"ai dama rashin ganin 'yamnata ne yasa taje takura kanta, ummieh ce tai murmushi tace"su ki tattarasu ku tafi tare domin ni rabon da suje kauye ma har na manta, hajiya ce tace"afff wallahi zainab kamar kin shiga raina, nima abinda na ke shirin yi kenan.

A can sama kuwa a zaune suka tarar da su sai hira suke, gaba dayan su sanye suke da Abaya kowacce colourn nata daba, yayin da ta sajids ta kasance maroon mai wani stones masu sheki da kyalli.

Shigowarsu yasa suka saka ihuu, amrah ce tace"dama ai nace sai mun rigaku fitowa amma kunce a'ah yanzu suwaye winners, da karfi samiha tace"mune mune, hanna ce taja dan siririn tsaki sai kuma tace"to anji su winners anji jiki, yanzu dai ku tashi mu tafi kar wanann sarkin mita ta shigo gidan, gaba daya suka hada baki wajen fadin"ummy bah, daga nan suka nufi sakkowa, kowa da wayarsa a hannunsa.

Noor ne ya ruga ya rungume ummieh da taje zaune, a hankali tace"noor inaga dai sai ka karyani sannan zaka huta, cikin muryar gwara ci yace"kaiii ummi daga zama, sai kace zan karyaki, hajiya ce ta kallesa sannan ta kalli 'yammatan tace"ohhh ni dai yau angama birgeni, duba kiga shigar maigidana, gashi nan kina ganinsa kinga babban mutum, kai sajida allah yayi miki albarka wallahi.

Sajida ce tace"aa hajiya mu duka zakiyi wa, yayin da a zuciyarta tace"ameen hajiya,hajiya mikewa tayi yace"nidai idan kunje gidan khairatun kuce ta bani abin dadi, wanda tasan wannan bakin nawa zai iya ci, murmushi amrah tayi tace"kuma dai hajiya allah kin fiye kwadayi, hajiya ce ta juyo tace"ungo naki mara kunyan karya, mannal ce tace"nidak kuzo mu tafi gaskia saboda kar ummy ta shigo, daga nan sukai sallama suka fice.

A harabar gidan suka tarar da driver, kallon kallo aka shiga yi,amrah ce tace"ku tsaya kugani, karasawa gabansa tayi tace"ina wuni amsawa yayi sai tace"hajiya tace"ka bamu key din mota, ba tare da wani Dogon tunani ba ya mika mata.

Dariya sukai su dika sannan suka nufi katuwar motar kirar jeep black colour, mannal ce ke driving una zuwa karshen layi sukai parking suna jiran ummi, hanna ce tace"gasjia nidai bazan iya jiranta ba kawai bara na kira ta, karar waya sukaji kusa da su,samiha ce tace"to ai gatanan ma, bashi kenan ba, kowa ya huta, daga nan suka dauki hanyar zuwa gidan khairat.

Sun dan jima a gidan sannan suka taho, a wani katon shopping mall suka tsaya sannan suka shiga, sai d asuka gama shopping dinsu, sannan suka dawo gida.

Sabra ce ta mike sannan tace"mama ki kyaleni da su ni zasu rainawa hankali, kuma wallahi ba zan fasa ba, kuma ban saduda ba,tsawar da aka daka mata ni kaina sai da na tsora amma ita ko gezau, police din ne ya kalli wata sergeant mace yace"taho da ita, domin nayi alkawarin sai ta girbi abinda ta shuka, janyota sukai suka sakata a motarsu, yayin da sahura take ta basu hakuri akan su kyaleta amma inaa furr sunki jinta, daga nan suka fice daga gidan ita kuma tabibbayansu da gudu, ganin motar tayi nisa yasata dole ta dawo tana haki, safina ta kalla tace"ke maza ki kiramin daddynku, safina cikin 6acin rai tace"mama sai kiransa nake amma rejecting yake, da mamaki karara akan fuskarta tace"kuma waya ta ce, safina ce ta nuna mata, a take ta furta shikenan na shiga 3 tabbas asirina yana dab da tonuwa.

Wayar ta kar6a sannan ta shiga wata mota kirar corolla yayin da safina ke fadin"mama ki dawo baki da mayafi fa, ko kallonta batayi ba tasaka kai ta fice daga gidan a wani matsiyacin gudu, gudu kawai takeyi domin tasan a inda zatayi maganin matsalamta.

Sabra kuwa tafiya suke yi amma samm har ya zuwa wannan lokacin bakinta bai mutu ba, sai rashin kunya taje mus, daidai office din su sukai parking sannan suka fito, police din ne ya kalli sergeant din yace"ki shigar da ita sannan ki sakata a cell zan ga karyar rashin kunya a wajen nan, yayin da tace"ok sor, ba'a 6ata lokaci ba aka sakata a cell.

Allah ne kadai ya kaita tana shiga ta fara jin wata mahaukaciyar dariya, da gudu taje gabansa tana afi tace"boka ka taimaka min, tsawa yayi mata yace"ke sahura ki sani bakin alkalami ya riga daya bushe, domin kuwa a halin yanzu kin karya mana doka, kuma tinda kika karya mana doka, ki sani dik wani aiki na tsawon shekaru ya ruguje, dan haka ki tashi ki bani waje, maimakon ta tafi sai ta tsaya tana kara rokonsa, da karfi yace"ki sani kin karawa kanki laifi dan haka yadda kika gani dik zamanki anan kanki kike kara tonawa asiri acan, dan haka ki tattara ki bar wajennan, haka ta fito jiki a sanyaye ta fito ta shiga motarta, gaba daya kanta ya kulle ga wani tinani dayake ziyartar kwakwalwarta, tana shigowa abuja bata ankara ba taji motarta ta bigi wata katuwar mota, take motar tai sama, abinda taji anfada shi ne, wannan yana daya daga cikin hukuncin kin tafiya da kikayi tukunna ma a sannu zaki ga sauran, take motar ta fado ita kuma katuwar motar ta 6ace.

Kowa na wajen mamaki yake domin su basuga komai ba kawai sunga mota tayi sama ta kuma fado, da mamaki suka karasa suka cirota, daga nan suka tafi asibiti da ita, da kyar aka samu wayarta da farko sun kira numbern daddy amma ba'a dagawa daga nan suka kora 'yarta safina da tana zaune tana cin abinci hankalinta kwance, jin abinda aka ce yasata fadin" inalillahi wa inna ilaihi raji'un.

Da karfi ta fara kiran ummy!

Ummy!!

Da gudu ta karaso tana fadin'"safina lafiya, da kallo tace" mama tayi accident tana private hospital gwagwalada, ummi ce tace"inalillahi wa inna ilaihi raji'un, to safina me muke jira muje mana, daga nna suka fito suka nufi hospital din.

Ummi ce ta fito da waya tana kiran daddy, kira daya ya dauka yace"ummi nah ya akai, cikin kuka tace"daddy wai mama ce tana private hospital tayi accident, banji me yace ba sai katse wayar yayi daga nan suka ci gaba da tafiya, suna zuwa suka karasa reception nan aka ce musu tana ICU kai tsaye nan suka nufa ganin ba'a fito da ita ba yasa su zama a daya daga kujerun dake wajen.

Sun dan dauki mintuna sannan daddy ya shigo, a lokacin doctor ya fito, kallonsu yayi ya kalli daddy yace"alhaji hashim dan allah ka biyoni office ku kuma ku zauna yanzu za'a fiti da ita, daga nan ya bisa suka tafi.

Doctor ne yace"munyi kokarin ceto rayuwarta amma kuma kafarta guda daya ta riga data fita, sannan kuma taji ciwuka a hannuwanta, a yanzu dai zan iya fada maka ta fita daga hatsari, amma kuma bata da kafa, daddy ne yace"inalillahi wa inna ilaihi raji'un" maimakon yayi wata magana mikewa yayi ya nufi icu din suhail ya gani a tsaye yana kallon su safina da ita take kuka, ita kuwa ummi tayi shiru ta fada duniyar tinani,daga nan aka fito da ita aka chanja mata room, suka bi bayanta.
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
Shatu Graphix
Matar Uncle
No:-08067574868
Page 53&54
Daddy ne ya shigo ya kallesu yace"kuyi hakuri domin a halin yanzu likta ya riga daya fadamin cewa bata da kafa daya, sa kai yayi ya fice, ummi da mamaki fall ranta tace"dama mama nasan za a zo nan gabar shiyasa nake cemiki kidaina wannan hakin, dafata da salim yayi yasata juyowa yace"ku kula da ita zanje nadawo, zama sukayi ssuna kallon junansu, safina ce tace"ummi kinsan da cewa sabra taba gun police.
Chapter 19 · 0% Book details