← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zumburo baki safina tayi tace"nidai gaskia ce sai na fada kuma ai ba wannan yarinyar bace sila, ita da kanta ta jawa kanta jibga har da ce masa azzulumi, taga aikin zalunci ai.

Tsawa sahura ta daka hadi da fadin "tashi ki fita ki wuce dakinki, ai dama dare yayi, ke wato kam dik abinda za a miki sai, bata karasa ba sabra ta fashe da kuka, sahura ce tace" ya hakuri insha allahu sai yazo da kansa ya baki hakuri,indai ina numfashi kinji, murmushi tayi ta janyo mata pill ta bata sannan ta kashe mata hasken dakin.

Safina maimakon ta tafi room dinta, room din ummi take knocking, sai kuma tace "shigo.

A zaune ta gansu suna kallon tashar arewa24 zama tayi sannan ta kalli ummi tace" ke tas
hi ki zubo min abinci, da mamaki ummy tace"amma safeenah wani kallo tayi mata, salin alin ta mike ta fita daga dakin.

Kallon azzahra tayi tace"amm kiyi hakuri da halin sabra, haka take bata da kunya ko kadan, sannan kuma ita bata ganin kowa da gashi, murmushi azzahra tayi tace"bakomai aunty nagode, karon farko da aka fara kiranta da aunty wani dadi ne ya ziyarci ranta, a zuci ta furta"ashe yarinyar nan tana da hankali har haka, kai gaskia idan haka ne kuwa dole mu kulla kawance, gata da kyau masha allah, wannan a wajen bikin.

Ummi ce ta shigo ta mika mata abincin daga tsaye, janyo table din dakin tayi sannan ta ajiye ruwa ta mika mata da lemo sannan ta zauna, azzahra ta kalla ganin tayi shiru yasata dafata tace"wai ke sis bazaki rage wannan damuwar ba, haba dan allah kinsan dai ba lafiya gareki ba ko sisy.

Dan murmushi tayi kawai, sai da ta gama sannan tace"ummi sai da safe mikewa tayi ta tafi tana kara tina yarinyar da yadda allah yayi mata baiwa ta kyau.

Azzahra ce tace"to aunty sai da safe, allah ya tashemu lafiya, da murmushi tace "ameen fateema sannan ta wuce zuwa waje.

Ummi ce tace" wai ke yanzu safinar kike cewa aunty, kallonta azzahra tayi tace"yo ba dole nace mata aunty ba, ta girmeni ba, allah ummi kamata yayi ki fara ce mata aunty, zataji dadi, dik wanda ya girmeka allah yanaso ka girmamasa.

Washe gari bayan sun gabatar da sallar asuba ummi ce ta mike zata koma ta kwanta, Azzahra ce tace"ummi dan allah ina alkur'aninki, kasan wardrobe ta nuna mata cikin wata locker, budewa tayi ta dauka ta fara rera karatu cikin surar Nisa'i.

Sai da tai kusan rabi sannan wayar ummi ta fara kara, cikin baccin ta laluba ta dauka, ganin sunan mama ne yasata tashi ta kara a kunne, tohm tace sannan ta ajiye.

Azzahra ce tace "yadai naga kina yatsina fuska.

Ummi ce ta kalleta," auhh har kin gama karatun kenan, ba dole na yamutsa fuska ba sajeeda tinda allah yayi ni kadai na iya girki a gidan nan, wallahi safina da sabra ba abinda suka iya na girki dai.

Azzahra ce tace"shikenan ai sai ki tashi mu tafi naje na kama miki ko, yanzu kin samu 'yar tayi nima ai na iya, da murna tace"kaii allah nagode maka na kuma godewa ya dareib daya kawo min ke, nima yanzu wataran zan na hutawa.

A kitchen sai da suka kammala komai sannan suka koma daki, ummi ce ta shiga wanka.

Azzahra ce a zaune ta rasa ta ina zata fara, shin ina iyayenta suke, wacece ita, ina ya al'ameen, kuka takeyi sosai, ummi ce ta fito shiru tayi da farko sai daga baya tace"azzahra bazan hanaki kuka ba amma dan allah ki daina wannan kukan, kin samu iyaye na tabbata da cewa a gidan nan zaki zauna har karshen rayuwarki, ba wanda zsi miki magana akan iyayenki, amma kinki yadda ko.

Azzahra ce ta goge hawayen fuskarta tace"ba haka bane ummi amma abin da ciwo na rasa ina ahali na suke, bansan ya zanyi ba, amma shikenan ummi kada ranki ya baci bazan kara kuka akan ahali ba, koda wani ya tambayeni zan fada masa cewa kune ahali na.

Da murmushi a face dinta tace"yawwa Azzahra yanzu dai jeki ki wanka, saboda yanzu nasan lokacin breakfast zai yi,mikewa tayi ta shiga toilet.

Bin bayanta ummi tayi da kallo sannan ta girgiza kai domin lamarin Azzahra ya fara bata tsoro, ga wani mugun tausayi da yarinyar take bata.

Fitowa sukayi lokacin kowa yana zaune, suna zama daddy ya shigo, bayan an gama gaishe gaishe nan suka fara gudanar da break kamae yadda dama sukeyi da can.

Sai da suka gama tsaff sannan suka tattara suka koma parlor, dsddy ne ya dubesu gaba daya yace"ina sabra safina ce tace"daddy tana daki, kirata amsar da ya bata kenan.

Basu dade ba suka shigo wani mugun kallo ta watsawa Azzahra da kanta ma a kasa yake tana kallon carpet din dakin, zama tayi jikinta dik sawu.

Daddy ne ya kalli sabra yace ke bawa yayanki hakuri, badan taso ba ta yamutsa face tace "yaya dareib ya hakuri, a hankali yace" ba komai ai ya wuce.

Daddy ne yace"kamar yadda nake sanar muku yau Friday, a yau ne kuma na samu sakon cewa a yanzu haka ina cikin ministocin da aka nada, gaba daya falon kowa ka ga face dinsa ka gansa cikin farinciki.

Sannan kuma zuwa nan da monday zamu tattara mu koma abuja sakamakon ayyukan da zasu na hawa kaina, na manta ban sanar da ku ba, ministan wasanni aka min, ina fatan dikanku kuna farincikk, kuma ina fatan allah ya shiga lamuranmu ya taimake mu.

Ku tayani da addu'a allah ya bani damar sauke dik wani nauyi daya rataya a kaina, sannan kuma sai batu akan azzahra wanda jiya bamu karasa ba saka makon sabra data shiga maganar da ba ta ta ba.

Azzahra dai daga yanzu ta kasance 'yar cikin wannan ahalin sannan kuma dik wani abu da zanyi muku to zanwa azzahra saboda ita ma' yace kamar kowa.

Sai batun auren sabra da safina, gaba daya nida ahalin angwayen mun tsaida magana, mun saka shi wani month din end din sa, sannan kuma ke hajiya sahura zan baku kudi keda yaran kuje kasar da kukeso kiyi musu siyayya dik da cewa za a zuba musu a lefen su, amma dai ance kogi baya kin dadi.

Safina ce tace"to daddy mungode allah ya saka, hajiya sahura taji batun kudi nan ta yake hakora tana zuba uwar godia kamar ba ita ce take fishi ba, sabra ma haka domin rabon data fita daga kasar nan har ta manta.

Dareib ne ya kallesu yace"to nima zan kara muku da nawa kudin sai ku hada kuje kuyi siyayyar, ai sabra batasan lokacin data saki ranta ba tana zuba addu'a, dareib mamaki ne ya cikasa dama wai sabra ta iya addu'a haka.

Daga nan kowa ya watse ya barsu suna ta murna kamar basu ne suke fishi ba,bayan fitarsu matan ne kadai a daki dan sahura ma ta wuce room din ta.

Sabra ce tace"ke azzahra tashi kije ki gyaramin room di na, ummi ce tace"kai sabra dan allah yanzu da can ita ce take gyara miki ba ke da kanki kike gyarawa ba, tasowa tayi da sauri azzahra tace"dan allah aunty kiyi hakuri ki kyaleta zan gyara miki yanzu zan tashi, da mamaki sabra tace "aunty kuma ni ce auntyn, gyada mata kai tayi ta tashi ta wuce har ta tafi ta juye tace" aunty wanneme dakin nuna mata dakin tayi.

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
Short Story
ZINARIYAR NAZARI WRITERS ASSOCIATION
The Stars
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
Oum ameerah
21&22
Zaune take akan daya daga kujerun falon ta harde kafa daya kan daya ta zabga uban tinani, wata mata ce doguwa mai dan jiki kadan ta fito daga dakin ta karaso zuwa falo, da mamaki matar ta kalleta tace"hajiya sahura yau kece a garin nan kuma da wannan sassafiyar.

Dauke hannunta sahura tayi ta goge gumi ta yake tsatsafo mata, sannan tace"to hajiya nana ba dole ki ganni yanzu ba, ai ni banga ta zama ba, ina baki labarin wannan yarinyar da tazo, kuma nasan ai kinsan ita ce kadai zata iya fito dani da sanyin safiyar nan.

Dan karamin tsuka nana taja tace"ai laifin ki ne, ko menene yanzu da kinzo munje wajen sarkin aljanu amma kinki zuwa ko, sahura ce tace"ai nana nan da kika ganni da shiri na wallahi daga nan sai wajensa domin dole na kori wannan yarinyar mai zubin mayu.

Nana ce tace"to bara na dakko mayafi na yanzu mu tattara mutafi domin kinsan, sai dai ayi sakko idan anaso a tarar da shi.

Tafiya suke a motar hajiya sahura sun shafe kusan awa 3 amma har yanzu basu karasa wajensa ba.

Ummi da azzahra ne kadai a gidan kowa ya fita domin zuwa aikin gabansa, ummi ce yace"azzahra taso muje ki tayani na musu girki domin ina nan da ke wallahi da sun dawo zasu ce mini ina abinci, kamar wata jakarsu.

Tare suka shiga room din su nayi suna hira sama
, shigowar motar sabra ce yasa ummi lekawa ta window, ganin ta tayi sai wani abu takeyi, tabe baki tayi tace"allah ya shiryi sabra, azzahra bata kula ba taci gaba da aikinta.

Cigba sukai da aikinsu, ummi wayarta ce ta fara kara, ganin sunan dareib ne yasata dagawa da hanzari, abinda ya subuce mata ne yasa azzahra saurin juyowa tana fadin"lafiya wai ummi menene me yake faruwa, bata kula ta ba, domin hankalinta baya wajen sam.

Faruq ne a tsaye da waya a hannunsa, cikin farinciki yace"good job ka duba nasaka maka kudinka a account, katsewa yayi ya jiyo yana ihuu ya kalli faisal dayake zukar shishar sa cikin kwarewa.

Faisal ne ya katsesa yace"da alama dai faruq hakarka ta cimma ruwa, da dariya ya nemi waje ya zauna, yace"ba dole ba faisal gaskia sun iya aiki, kai da kasan a ina zaka samo mutanen nan amma ka barni naita bulayi cikin duhu, wow amma naji dadin aikin nan, faisal ne ya tsayar da shan shishar yace"yanzu kuma sai meye next, faruq ne ya saki wani killer smile yace"zaka gani kai dai.
Chapter 8 · 0% Book details