← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khair ce tace"nifa kun cika ni da surutu dan allah ku kyaleni ina sajida take, hanna ce tace"bata da lafiya suna asibiti ita da ummy, bata kawo komai ba tace"ai shikenan yanzu dai ku zama cikin ready ina inviting kowa a birthday party dina, ihu suka saki, mannal ce tace"amma auntu ya akai na manta, khair ce tace"dole ki manta tinda yanzu kun zama ku 6 da ku 2 ne ko, murmushi tayi kawai ta kalli hannah da sauran 'yan uwanta.hajiya ce ta fito tace dan allah kumin shiru kun dameni da ihu nan ta wuce kitchen, dariya duka suka saka suna kallonta.

Sahura ce ta fara magana KOMA MENE NI NA JAWO WA KAINA.

Muhade a wani part din domin jin tarihin sajida ds kuma ahalin hashim babangida.
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
No:-08067574868
Page 59&60
A shekarun da suka wuce a lokacin da khadija take da cikin fatima, na kasance ni kuma da cikin ummy,ni nafita haihuwa saboda kwadayi da kuma son dukiya a ganina idan mijina wato hashim ya mutu na fita samun dukiya, dik zaman da muke akwai abinda bansani ba, ashe dama dik wannan dukiyar da alhaji yake da ita ashe rabi ta khadija ce, a lokacin dana gano hakan sai dik naji babu dadi, hassada,
kyashi da kuma son abin duniya suka taso ni a gaba, har na rasa yadda zanyi, tsawon watanni ina tinanin yadda zan shawowa lamarin har dukiyar ta dawo hannuna nida yarana.

A cikin wannan lokaci ne hajiya nana ta shigo falo na,zaune ta ganni na zabga tagumi, ta6ani tayi firgigit na mike ina zaro idanuwa, nana xe tace"wai sahura mai yake damunki ne, kalleki dubi yadda kika chanja nidai nasan ba rashin ci ba, ba rashin sha ba, ba kuma rashin sutura ba bare kice, kuma kinsan har yanzu alhaji bai, rufe bakinta tayi tana kokarin hadiye maganar, boka ne ya daka mta tsawa yace"naga alamun bazaki fadi gaskia ba har sai nasa baki.

Boka cikin wani kallo yace"hashim a tsawon rayuwarka kasan da cewa sabrah da kuma farouq ba yaranka bane, kowa na dakin zaro ido yayi yana kallon boka, banda daddy da ko kadan maganar bata masa wani bugu ba, murmushi daddy yayi yace"nasani amma nima yau kwanaki 4 kenan da sanin abinda yaje faruwa, boka ne ya tuntsure da dariya yace"kayi kyan kai.

Kowa kallon sahura yayi yana mata wani irin kallo banda safina da ummy da suka koma gefe suna faman razgar kuka, domin sun sani yau abinda mahaifiyar su ta shuka shi zata girba.

Sahura xe taci gaba da fadin"tin daga wannan lokacin da nagano hakan na tabbatar da cewa dole ne sai na tashi tsaye domin na samu rabona, saboda koda antashi rabon gado na tattara na cinye dika nida yarana.

Haka na zauna tsawon watanni ina tinanin mafita, a wannan lokacin ne kuna khadija ta haihu santalekiyar yarinyar ta sak mahaifiyarta dan sunyi kama matuka da khadija, 6acin rai da kuma bakin ciki yazo ya tayar min.

Watarana ina zaune nana ta shigo gidan, ina can cikin dakina na rafka tagumi, ji nayi an dafani, saurin dagowa nayi ina kakaro murmushin karya.

Nana ce tace"sahura bazaki boyemin komi ba, domin tsawon watanni a haka nake ganinki,dan haka ki fadamin damuwarki yanzu na miki magana, da farko sai naki fada mata amma data matsamin sai na fad'amata.

Nana ce taja tsaki sannan tace"ni dadina dake wallahi kanki bayakawo wuta, dik malaman nan da bokayen nan ace sai kin tsaya kina faman sakawa kanki damuwa, yanzu dai ki bar wannan kawai ki kawo kudi ni nasan me zan aikata, kedai ki zama'yar kallo sanann dik abinda nace kiyi shi zakiyi, anan na yadda da sharadin nana na bata kudi ta tafi.

Bayan kwana 2 ne nana tazo da wani irin al'amari cewa na dakko jaririyar da khadija ta haifa, nima a lokacin ina da tsohon ciki amma tsabar hassada banga nawa cikin ba, sai na tafi naje na dakko, da farko na bata ita sai kuma nai maza na rikota nace "ina zaki kaita.

Nana ko a jikinta tace" yaddata zanyi domin boka yace tayi nisa da gidan nan, ganin da gaske take yasani jan mayafina da fadin muje, a wannan lokacin kam khadija tana bandaki batasan wainar da ake toyawa ba.

Muna fita kofar gida na bawa nana wata jaka da kuma kudade masu yawa, nace ta kaiwa wata tsohuwa wato nasanta ne tin ina 'yammata na kwatanta mata gidan ta sannan nikuma nadawo na shige can cikin daki.

Tin daga saman bene nakejin kururuwar khadija da yaranta, suna neman' yarta amma sai nayi shiru na koma na kwanta, dareib wanda shi ne babba shi ne ya kalli aryaan yace"zo muje wajen maman su affaan mugani idan tana can.

Dareib ne ya shigo yana tamvayata kanwarsu, maimakon basu amsa sai na fara zazzaga masifa ta inda nashiga bata nan nake fita ba.

Haka suka fice daga gidan daga yaran har khadija, nidai nasan su dareib sun dawo amma batare da mahaifiyarsu ba, bansan ya akai ba.

Kiran wayar nana ce yasa na fahimci khadija tana wajenta, cikin mamaki nace"to ya kikeso nayi da alhaji ne ga wadan nan yaran sun gansu, wani killer smile nana ta saki tace"karki damu da komai domin idan sun fada masa zai yadda anan kuma zamu mantar dashi wacece khadija daga nan ta katse wayar.

Bayan sati 1 da faruwar wannan al'amari na shirya naje wajen boka nida nana, a wannan lokaci ne ya kalli khadija duba na tsanaki sannan yace me kukeso ai mata, nidai tashin farko nace a kasheta domin na tabbata idan har tana raye to komai nawa ya gama lalacewa.

Bayan mun taso ne nana tace"tayi mantuwa dan haka na jirata ta koma wajen bokan ban san me suka tattauna ba, daga nan muka dawo gida.

A lokacin alhaji ko zancen khadija baiyi ba, sai yaci gava da harkokinsa, amma yaranta sun kasa mantawa da mahaifiyar su da kuma kanwarsu.

Bayan shekaru a kwanan nan ne kuma naga fatima ta dawo ta dalilin dareib a wannan lokacin na tsorata amma sai ban nuna ba, nasan idan har na nuna nasan wacece ita to zargi kaina zan komo, a wanann lokacin ne na koma wajen boka yayi mata kurciya, naso ya haukata ta,amma yace bazai iya ba domin yarinyar tana da addini,sai dai ya tura aljani domin ya shafe tinaninta tsawon wata 2 kenan da faruwar al'amarin.

Kowa na dakin kuka yake a wanann lokacin kuma doctor ya shigo dauke da syringe da kayan aiki domin yiwa sahura allura, turus yayi ganin yadda kowa ke kuka.

Azzahra ce can kusa da gadon da khadija take tan faman rera kuka mai tsuma zuciya, kowa na kokarin lallasar kansa banda azzahra domin ita a yanzu gara tayi kukan, cikin kukan take magana, ashe dama inada gata haka ina da gata kuka ne yaci karfinta, ashe ba yadda inna ke fadi bane cewa banida ahali banida kowa daga ita sai ni, ashe dama inna ba kakata bace.

Dareib ne ya karasa ya dagota, jin jikin nata da zafi yasa kallon dr yace"duba ta dan allah yana kokarin karbarta ne ta zube a wajen sumammiya, a lokacin kuma khadija ta tashi.

Sahura ce tace"dan allah alhaji hashim kayi hakuri, tabbas naci amanarka kuma nasan da cewa ban kyauta va gaba daya a rayuwata, malam ne ya katseta da fadin"to yanzu sahura ina amfanin wannan babbar barna, ki gode allah da sauran kwananki a gaba.

Kai kuma ya sunanka ya kalli boka, boka ne yace"ni cikakken sunana Saleh, kallonsa yayi yace"to ina amfanin wannan ta'asar malam saleh, duba da yadda sunanka yake,boka ne ya babbake da dariyar sa yace"eaa inada sunan musulmai amma ni dai rabona da sallah a yanzu nafi shekara 20, malam ne ya
dafe kai yace"inalillahi wa inna ilaihi raji'un.
*FATEEMAH ZAHRA*
_Azzahra_
A'ishatu Bint Muhammad
******************
Queen Waleedah
No:-08067574868
Page 61&62
Boka ne ya dakatar da malam da fadin cewa"ka daina wahalar da kanka domin mudin shaidan ya riga yayi tasiri a zukatanmu bazamu daina ba, domin mu shedan shi ne komai namu(inalillahi wa inna ilaihi raji'un ina gari ya waya allah ka tsare mana imaninmu da aikata barna, yanzu duba ku gani rayuwar sahura ta kare
danasani.

Boka ne ya ce"ni na tafi na bar ku lafiya, ke kuma sahura bazan barki haka ba domin kin aikata babban kuskure,kara yayi da karfi take ya bace, juyawa sukayi nan fa sukaga wayam ba sahura ba alamunta.

Ummy ce ta mike ta share hawayen fuskarta, sannan taja hannun khadija ta zauna dab da ita tace"ammah a madadina da kuma momi da sauran dangina ina mai baki hakuri dan allah ki yafewa momi, allah yanasan masu yafiya, dan allah dan allah ammah kiyi hakuri ki yafe mana, karki kallemu da laifin momi domin ni bansan me yake faruwa ba.

Khadijeeh ce ta dagota tace"ummy fuska cike da murmushi ta rungume ta tana zubar da hawaye, ummy ce taja hannunta suka bar dakin tare da sauran mutane, dakin da aka kwantar da fatima suka shiga, kallo daya khadija tayiwa fatima take taji sanyi, kallon daddy tayi fuska cike da hawaye, cike da kwarin gwiwa ya gyada mata kai alamun eaa da gaske ne, cikin sauri ta kankameta tana zubar da hawaye, a wanann lokacin azzahra ta farka tana murza ido, kallon khadija tayi take ta rungume hadi da sakin marayan kuka.

Kowa na dakin sai da ya zubar da hawaye, cike da tausayi da kuma kaunar juna, ganin basu da wani abunyi na dawo da sahura dole suka mike suka bar asibitin, kowa zuciyar sa cike da farinciki domin dawowar khadija garesu.

A can falon ummieh kuwa noor ne ke ta kuka, tin daga bakin kofa sajida ta jiyo kukan nasa, amma ta kasa rabuwa da jikin mahaifiyarta, ji take kamar idan ta saketa zata tafi ta barta.

Suna shigowa mannal ce tace"sajida kin tafi kin barmu da noor yaki yin shiru wai shi kullun girma yakeyi amma hankali sam yaki sauka a garesa.
Chapter 22 · 0% Book details