← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauke numfashi tayi mannal ce tace"samiha matsa na dubasa, sai a lokacin sajida ta kalli twince din, hankalinta ne ya dawo kansu ta kara kallonsu, sannan ta kalli samiha yayin da ita kuma take kokarin karbar noor a hannunta, kwantar da shi tayi akan gado bayan ta cire masa kayan jikinsa, kallon samiha tayi tace "samo min ruwa da towel, kafin tayi wani yunkuri tini sajida ta shiga toilet bata dade ba ta fito da ruwa a roba da towel.

Ta dau a kalla mintuna 10 amma ba abinda ya sauya kukan ma yaci gaba dayi, samiha ce ta rike kai tace" oh my god kinga hannah dubamin yaya khairat a dakin ta tana nan, idan tana nan na kawo mata shi ta dubasa, fita tayi da dsn sauri hajiya na zaune a falo ta dubeta tace"ke kuma Ina zakije kike ta sauri kamar zaki tashi sama, maimakon ta bata amsa sai tafiya kawai tayi, jidda mahaifiyarta ce tace"hajiya nikam ina su baraka da d'ahare.

Acan dakin kuwa a zaunr tagansu su wajen 5 hange tayi ta hango khairat, ummulkhair ce tace"hannah me kikeyi anan, dan murmushi ta kakalo tace"bakomai ina neman khairat ne.

Karasawa tayi wajen ta janyo ta tace"yaya khairat dan allah zo kiga wani abu, khairat ce tace"lafiya me ya faru, hanna ce tace"dan allah ki biyoni kigani, khairat ce ta bi bayan hanna, ummulkhair ce tace"wai meke faruwa ne, khairat ce tace"ina zuwa yanzu zan dawo.

Suna shiga dakin taga sun zagayesa, ganin haka hankalinta ne ya yo kan noor dayake kuka, da sauri ta haue kan gadon, tallafosa tayi sannan ta kalli samiha datake sanye da hijabi tace"jeki dakina maza ki dakko min first aid box akan wardrobe.

Tana fita ta kallesu tace"tin yaushe yake fama da zazzabi, sajida ce tace"tin dazu da ne bayan sallar azzahar, kuma ba wanda kika fadawa, sajida ce tace"yaya banaso ne na fadawa kowa kinsan kuma hankalin su tashi zaiyi kuma gashi ana biki, ta bude baki zatayi magana samiha ta shigo.

Dubasa tayi hadi dayi masa allurai masu saka bacci sannan ta kalli sajida tace"sajida idan ya farka ki bashi abinci sannan ki bashi wadannan magungunan, karba tayi tace"to aunty khairat nagode allah ya saka da alkhairy, da mamaki ta kalleta sai kuma kawai tai fuska tace"samiha dakko min first aid din nan ki maidata.

Tana fita sajida ta kallesu tace"sannunku ina wuni, bamu gaisa ba, dikansu murmushi sukayi suka amsa cike da kulawa, samiha ce ta shigo ta gabatar mata da su nan fa hira ta barke, ni kaina nayi mamakin yadda sajida ta saki jiki ana hira, samiha ce tace"aa na fuskanci sajida tafison zama da mutane dayawa.

Hirarsu sukeyi sukaji an bude kofa, kallon kofar sukayi jin ba'ayi musu knock ba, ba kowa bace sai ummi, da murna samiha ta tashi hadi da hugging dinta, nan fa mannal da hannah ma suka fara hugging nata, suna fadin"ke yanzu tsakani da allah sai yanzu kika gadamar zuwa bikin.

Kallon sajida tayi tace"sannunki dagowar da zatayi ne taji wani iri zuciyarta take ta buga bammm, da sauri tace"wannan fa nidai bansanta ba, cike da kulawa samiha tace"sunanta sajida anan gidan take 'yar uwarmu ce daga kauye, nan tai hugging nata, daga nan aka fara hira, sun dan jima jin kiran sallah ne yasasu watsewa suje suyi sallah sannan su dawo..

FATEEMAH ZAHRA
**Azzahra**
Written by
Queen Waleedah
Matar Uncle
Shatu Graphics
ELITE DIAMOND WRITERS
Where diamonds shine, words ignite
Dedicated to
FATEEMAH Y ZAKARIYYAH
Oum ameerah
Follow on Arewabooks@MatarUncle
Follow on Wattpad@mataruncle
43&44
Suna fita ta zauna tana kallon noor da har yanzu bacci yakeyi,cike da damuwa ta shafa face dinsa sannan ta tofa masa adduva, a fili tace"ai kam zazzabin har ya tafi ohhh komai da mahadinsa.

Baya da kmar mintuna 20 sai gasu sun dawo lokacin tana zaune tana abinda ta saba yi wato tunanin wacece ita, mannal ce tace"sajida taso muje, wani katon hijabi ta janyo zata saka, mannal ce ta riketa tace"dan allah dan allah sajida ki cire wannan hijabin ki amfani da mayafin abayar ki, da kyar ta yadda ganin suma sunbi bayan mannal.

Sajida ce tace"wato kam dai kunbi bayan mannal ko shikenan ai, gaba dayansu dariya sukayi daidai lokacin noor ya fara murza idanu sannan ya budesu sajida ce ta karasa wajensa tare da kamosa tace"sannu my love ya jikin, murmushi yayi cikin dariya yace"aunty sannu, kallon sauran yayi yace "ainty wannan fa, samiha ce ta rigata magana tace" lalle noor abin naka ya dawo ba wanda kasani daga aunty sai papa ko.

Dariya yayi yace"aunty samiha ina wuni, gaba dayansu dariya sukayi, ummie ce tace"nikam samiha saida kika san yadda kikayi har noor ya dawo tsoranki kenan, dariya sukayi ummie ta kara magana a karo na 2 nifa noor yayai min saurin girma ma, dubeshi duka shekara 3 amma yayi wayau sarai yasan kowa, tubarkallah gashi ya girma ya kara kyau.

Fita sukayi daga dakin falon gidan ne gaba daya da mitane masu cin abinci naci masu hira nayi, amma masu hirar ma sunfi masu cin abinci yawa, kitchen suka shiga ba mutane sosai, dan haka suka zauna a dining din wajen, mannal ce ta fara zubowa kowa abinci, saida suka ci fried rice with chicken mai rai da lafiya sannan suka fita zuwa harabar gidan, ita dai sajida yau taji dadinta domin ko ba komai ta samu kawaye, ita kanta taga saurin sauyawarta.

Samiha ce tace"ummie muje ki gaushe da mamana, daga nan sukai falon su, bayan sun gaishe ta ne suka fito suka nufi gardern domin su huta kan anjima su tafi wani event din.

Gaba dayansu sun baje a kasan grass carpet din, noor ne ya zagayo bayan sajida ya fara cire mayafin, ganin ba kowa a wajen batayi kokarin hanasa ba, nan fa ya fara tabawa, yana zaune akan kujerar sa yana kallon shigowarsu garden ya tsaya yana kallonsu, ganin noor ya bude mata kai take yalwataccen gashinta ya bayyana a fili ya furta ya subhanallah, tsarki ya tabbata ga ubangiji mai kowa mai komai.

Ba wanda yasa ana kallonsu domin dik tagogin a rufe suke kamar bakowa, a kasa kuwa hirar su sukeyi harda ta6awa, kamar dama can sun san juna, sajida ce tace"aa noor bari mana ya isa haka, bai bata amsa ba yaci gaba.

Jin hayaniya ana dosowa garden yasa tayi saurin jan dankwalinta ta maids, bata dade da maidawa ba suka karaso, ba kowa bane su khalil ne ganin su mannal ne yasa aminullah fadin ashe dama nan kukayo, samiha ce tace"lafiya dai ko, khalil ne hankalinsa yana kan sajida yace"eaa bakomai komai kalau, noor ta janyo ta zsunar dashi yayin daya gudu ya barta a zaune.

Jin shiru bai dawo ba kuma ita wannan hirar ta gundureta yasata mikewa, a tare suka furta"ina zakije, ba wanda ta kalla tace "neman noor sannan ta saka kafa ta fice ta barsu nan suna hira.
________________
Wasa wasa jikin dareib yana kara yin sauki yanzu daga nigeria suka ci gaba da tafiyar da companynsu, aryaan ne ya shigo da sallama a bakinsa, amsa wa dareib yayi yace" bro harka dawo kenan, aryaaan yace"dama ai badadewa zanyi ba.

Dareib ne yace"aryaaan nayi aikin banza wallahi, da mamaki yace"kamar ya aikon banza kuma, "jinjina kai yayi yace" eaa na gaya maka yanzu haka azzahra na gida ko, zama yayi jin an ambaci sunan yace "eaa haka kace dareib cikin kosawa da zancen yace" to ta koreta, aryaaan ne yace"ta koreta kuma dareib kai taya ka sani.

Dareib ne yace"zancen taya na sani ba taso ba yanzu dai a ina zan samota, domin kasan allah sai na tona asirin mama, aryaaan ne ya ta6e baki yace"ai dik inda take bazatayi wahalar dawowa ba saboda ai ta sanka ko.

Aryaaan bazaka gane ba mama tayi halinta, amma ka duba waccan wardrobe din zaka yadda da abinda nake fada maka, yqyi masa nuni da wardrobe din, sannan ya taba wata kararrawa, wani ne sanye da kayan aiki, cikin harshen tiranci yace"ka kawo min lemon juice sannan ya tafi.

Nemansa take amma ta rasa ina zata gansa can bakin gate ta ganshi a hannun wata mata, da gudu ta bisa, dik wannnan dramar akan idan nuradeen dayake saman bene, ganin kamar hafsat ce tazo yasa da sauri ya sauko, yana sakkowa abinda yw fara gaishe gaishe da kyar ya samu ya zame ya fito.

Can kuwa sajida janyo rigarta tayi tace"ke wacece kodai ke barauniya ce har da zaki shigo gida ki dauki yaro bada kowa ya sani ba, kardsi kice mon ke din barauniya ce, hafsat cikin wani tukukin bala'i tace"kece barauniya, sai kuma ta tsaya tana kallonta, batasan lokacin da kalmar nan ta su6uce mata ba wato "wannan kyakkyawar kuma daga ina, sajida cikin zafin nama ta janye hannun noor.

Noor na dariya yace" aunty dama wasa fa nzo yi, cikin fushi tace"kai min shiru dama ba saida nace karka kuskura ka bar garden ba amma sai da ka bari ko, hafsat cikin kunar rai da zafin zuciya ta zabga mata mari, sannan ta had'a kanta da mota.

Daidai lokacin nuradeen yace"hafsat wai meyake damunki, da sauri ya taho ya kamo sajida yana duba goshin nata, sai da taji mata ciwo jini har ya fara fita.

Hafsat cikin 6acin rai taxe"wallahi nuradeen daga kai har wannan figigiyar yarinyar sai kunyi dana sanin ja dani, kai din waye har da zaka hanani na dauki dana, ke dallah dakata ya fada cijin tsawa, karki kuskura ki kara tinanin cewa wai kina da yaro a gidan nan, bayan ba irin cin mutuncin da bakiyi mun ba, sannan kuma kizi kice na baki shi, dik inda zakije zakije ammw yaro dai nawane dan haka bazan ta6a yarda na dauka nabawa fasija ba.

Sajida ce ta tsaya kallon ikon allah yayin da jini ya fara wankemata fuska, juyo wa nuradeen yayi ya kama sajida sukar wajen, hafsat kamar ta fasa ihu, a fili ta furta nidaku ka fasa kuma sai kayi danasanin yi min wannan tijarar.
Chapter 16 · 0% Book details