← Book details Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Fateemah Zahra Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
FATEEMAH ZAHRA
Written by
A'ishatu Bint Muhammad
Matar uncle /Queen Waleedah
Labari ne daya kunshi:
Tausayi
Cin amana
Juriya
Hakuri
Da kuma uwa uba soyayya
Da ma wasu abubuwan
Basai na fada ba
Yana tare da nishadantarwa
Fadakarwa
Da kuma wa'azantarwa
Kudai ku saurari alkalamin
Matar uncle
_Wannan labari nawa kirkirarrene banyi shi dan musguna wa wata ba, idan labarin yayi daidai dana rayuwarki to kiyi hakuri akasi aka samu_
Na sadaukar da wannnan littafin ga babbar kawata
*Fateemah Y Zakariyyah (Oum Ameerah)*
Marubuciyar ahalin mu Daya.

And Now Idan So cuta ne.

NAZARI WRITERS ASSOCIATION
_Kyawawan Nazari kafin rubutu na
amfare da bin
a'idojin rubutu._
_Cikakken Nazari kafin rubutu kan
ayata duniyar Adabin hausa._
Alkalami yafi takobi
Na ajiye littafin a gidanmu sakamakon wani dalili nawa da bazan iya fada muku ba amma ina fatan zakuyi farinciki da sauraran wannan littafi nawa mai suna *FATEEMAH ZAHRA*Allah ka bani ikon fadin daidai.

Zinariyar Nazari Writers Association
EPISODES 1&2
YUSUF MAITAMA SULE UNIVERSITY KANO
Tafe suke sun nufi hanyar theater, a bakin theater suka zauna suna 'yammata ne guda 3 2 sanye suke da riga da skirt da veil, ita kuma dayar da hijabi coffee, mai hijabin ce a tsakiya janyo handbag dinta tayi ta fara janyo wasu papers.

Mai ash din mayafi ce tace "azzahrah nifa wallahi kina bani mamaki wajen jotting wannan shirmen subject din in banda lissafi ba komai a ciki.

Murmushi wadda aka kira da azzahra tayi tace" ai dama bazaki gane ba munaya domin ke allahn da yayiki kin tsani mathematics ni kam burge ni yake.

Mai blue din veils din ce tace "ni kaina yana burgeni wallahi, amma kinsan me yake birgeni yadda sir Haseeb yake yi, domin mutum ya hadu da tsantsar kyawu, irin wanda ba'a taba samu.

Azzahara ce taja tsaki tace" nifa wallahi dik kun isheni ku kyaleni na duba wadan nan papers din kunsan dai idan naje gida bana samun lokaci ko.

Munaya ce tace "Inaya ni fa wallahi da za a ce za a bani zabi ko, to allah da azzahra zan zabarwa haseeb, domin ba baya ba wajen kyau, dik kyansa azzahra ta fisa domin ita, azzahra ce ta mike tace" tinda bazaku bar hirar ba ni natafi, daga haka suka bita suna bata hakuri.

Azzahra ta kasance budurwarce a kalla zata kai irin 19-20years ta kasance kyakkyawa fara ce sol, bata da wata makusa.

Yalwataccen gashin gira ga wani siririn hanci kamar an zana biro, idanunta masu matular daukar hankali domin a irin idanun nan ne ash wanda sai wanda allah ya bawa wannan baiwar.

Dan karamin lips din ta wanda yake ja ne sosai domin ko bata saka jambaki ba, to yana zaune a jan sa ne, "yan kana nan hakora masu kyau da kyalli abin sai wanda ya gani, sihirtaccen dimples da sai ka kasance mai matukar sa'a zaka gansa.

Tafiya suke dai dai bakin gate suka tsayar da mai napep munaya ce ta shiga sai inaya datake kokarin bin bayanta, azzahra ce ta rike ta tace "wai ke dama da gaske kike bakizo da motarki ba, tabe baki tayi tace" to da azzahra zan miki karya ne.

Shiga sukayi daga nan suka bar school din gaba daya, azzahra ce a ranta ta furta "allah yasa idan na koma inna bata nan domin nasan idan tana nan shikenan komai bazai zo da sauki ba, dafata munaya tayi firgigit tayi ta dawo hayyacinta, inaya ce tace" dan allah ki dai na wannan tinanin da kike komai zai farko zai karshe azzahra, murmushin yake tayi kawai tace "ba komai.

Dai dai tudun yola aka ajiyeta sauka tayi sannna tace "to inaya munaya ku gaida gida sai mun hadu jibi insha allah dago mata hannu sukayi daga nan suka wuce.

Tafiya take wani mutum ta hanga tin daga nesa naga tana daga masa hannu, shima murmushi yayi saurayi ne amma matukar wahala ta maidashi ya zama wani iri abin ba kyan gani, karasawa tayi tace "Al'ameen kasan tin yaushe nake nemanka kazo amma shi ne kaki zuwa sai yau ko, bokitinsa na kwashe kwata ya janyo yace" azzahra bafa haka bane wallahi abubuwa ne sukai yawa kinsan da cewa ina aiki a wasu unguwanni kuma kinsan yanzu lokaci na ruwa, bai rufe bakinsa ba aka fara yayyafa, da sauri yace "azzahra maza ki tafi gida anjima zanzo ki bani labarin menene ya faru a makarantar taku, daga haka ya juya yaci gaba da aikinsa.

Azzahra ce tace " al'ameen amma kuma ana wannan ruwan zakace zaka ci gaba da kwashe kwatar nan, kinga azzahra dan allah ki tafi gida banason ruwan nan ya jikaki badan taso ba ta shige wani dan karamin gida.

Shigarta ta tarar da inna a tsaye da daurin kirji, dan karamin tsaki inna taja tace "wallahi fati sai naci uwarki shegiya mai duffar mayu, kinga idan baki dai na wannan kofkofta idanun ba sai na ballaki shegiya" uwar gantali, daga gidan uwarki kika fito har zaki dawo min yanzu.

To tsaya kiji wallahi aikin da kike gudu sai kinyi, dik wannan la'asar din kuma ki tabbatar tallan tuwon nan tana nan domin saura miya kadai kinsan kuma bazan yi asara ba ko, share hawaye azzahra tayi tace "amma inna taya zaki dinga zagina haka mai nai miki.

Inna ce tace" uwarki kikamin fati, nace uwarki kikamin shegiya yar iska.

Wasu uban kayan wanki ta ajiye sannan tace "wuce kije ki shirya kizo ki wanke min wadan nan kayan tin kan rankinya baci, azzahra wucewa tayi tana goge hawayen face dinta, a hankali ta cire hijabin, wata doguwar riga ce ta atamfa leda wato tamalalo ta dage mata, gashi dik tayi sikuizin.

Fitowa tayi ta fara kokarin hada ruwan wankin, sai da ta hada ana ruwa tana wanki dai dai lokacin da aka kira sallar magariba ruwan na tsayawa ita kuma tana gama wankin, alwala tayi hade da sallah sannan ta fito tace "inna dan allah ina abinci na, wata harara ta zabga mata tace" na cinye dan uwarki Khadija, take gabanta ya bada wani dammmm.

FATEEMAH ZAHRA
Written by
A'ishatu Bint Muhammad
Matar uncle /Queen Waleedah
Zinariyar Nazari Writers Association
NAZARI WRITERS ASSOCIATION
_Kyawawan Nazari kafin rubutu na
amfare da bin
a'idojin rubutu._
_Cikakken Nazari kafin rubutu kan
ayata duniyar Adabin hausa._
Alkalami yafi takobi
Dedicated to
Fateemah Y Zakariyyah (Oum Ameerah)
Marubuciyar Ahalin Mu Daya
And Idan So Cuta Ne
Episodes 3&4
Wallahi fati idan baki kiyayeni ba sai na karki shegiya kawai, zo ki dauki tallan nan kuma karki kuskura ki dawo baki sayar ba domin idan kikayi haka kika ja min asara allah sai kin biya ni, hawayen face din ta ta kara gogewa a hankali ta tsugunna ta dauki uwar roba, sannan ta dauki bokiti da sauran robobi ta fito, tin daga nesa take hangen hangen neman al'ameen amma bata gansa ba, kamar zata saka kuka haka taci gaba da tafiya.

Tin daga nesa mai awara ce ta hango azzahra tafe, wani tsaki taja tace "aikin banza yanzu zatazo ta kwace min customer ko dan taga tana da kyau wallahi inaga wataran sai na babbake wannan fuskar uban kowa ma ya rasa.

Azzahra ce ta sauke kayanta ta zauna tana fadin sannu habiba, banza tayi da ita bata damu ba ta fara baza ido ko zata hango al'ameen amma bata gansa ba, kamar kullun haka ta fara cinikin, wata mota ce kirar corolla l.e black tazo sai wata a tsakiya kirar range rover, sai irin corolla a baya.

Parking sukayi wani dan madaidaicin saurayi ne ya tsaya da suit a jikinsa, kana ganinsa kaga security, a hankali ya karasa gaban azzahra, wasu kudi ya mika mata yace "gashi nan inji ubangida na ki gaggauta rabar da tuwon nan ki tashi.

Dan karamin tsaki taja tace" bazan bari ba wai ku me kuka dauki kanku ne, ko nace mai ogan nan ya dauke ni ne da kullun zai dinga kawo min kudi yana cewa na gaggauta siyar da abinda nake saidawa, to yau bazan tashi ba sai na tabbatar da cewa ya kare, kuma wallahi dik wanda ya kuskura ya kara zuwar min nan sai na bata karasa ba taji securityn yace "yess sir, bai wata wata ba ya janyo hannunta gaba daya mutanen wajen a tsorace suke, dan haka ba wanda yayi gigin fara yi masa magana.

Har motar nan kirar range rover ya wulla ta sannan suka fice, tin da ta shiga ta kifa kanta ganin kamar ba abinda zai mata ne yasata dagowa hawaye shabe shabe a face dinta, dagowar da zatayi taga sunyi nisa a tafiya, ga wani hadadden saurayi a gefe iya kamshin turarensa ma abin shaka ne cike da sanyi.

A hankali ya furta" azzahra cikin cool voice, saurin dagowa tayi tace "dan allah yallabai ka maidani inda nake wallahi idan inna taga ban dawo ba, to kashe ni zatayi kuma ni ina tsoron saba mata.

Tinda ta fara magana ya zuba mata kyawawan idanunsa, ko mai yake tinani oho masa, wani dan karamin tissue ya janyo ya ja hannun azzahra ya fara kokarin goge mata hawayen, cikin murmushi yace "to amma sai kin daina kuka kuma da kike wannan abin yanzu ai kaka bazata neme ki ba.

Abinda nakeso ds ke shi ne na daukeki aiki a company SADDAM & BROTHERS Ki tabbatar kin fara zuwa, nan da gobe nake buqatarki, sannan kuma batun makaranta nasan zaki min, baki da matsala dan haka sauka gashi nan mun dawo dake, sannan kice wa inna zan shigo dan kar taga kin dade, wata uwar harara ta zabga masa sannan tace "bazan fada ba, da gudu ta shiga gida, bata wani jima ba inna ta fito, har ta fara balbalin bala'i sai kuma ta hangi motoci, bude baki tayi tace" aa ranka ya dade, bayanin komai saurayin yayi mata sannan ya ba inna makudan kudade, bude baki tayi ta fara jero masa addu'a.
Chapter 1 · 0% Book details