← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 87

Sashe 9

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*
Fita yayi cikin sauri dan amsa wayar da mahaifin sa ke kira.
Ga baki d'ayan sojojin suka bi bayan sa cikin sauri. d'aga musu hannu yayi alamun su koma. Bbu musu suka jah suka tsaya a inda suke.
Captain Ahmed ne ya bi bayan sa
Dan ya san hatsari ne barin shi yafi ta shi daya.

Amsa wayar ya yi sannan suka gai sa. tambayar sa ya keyi da cewa.
Yareemah...!!! Kana lafiya?" cikin murya mai cike da da muwa yace "lapya na klau abba, wani abin ne ya faru?"
A'a bbu babu komai ka kula da kan ka kaji ko?
Kuma na kira mahaifiyar ka tace mun bata san lokacin fitar kaba.
Ya kama ta Karin ga sanar da ita, ai addu'ar mahaifiyar ma yana da Amfani kaji ni?"

Yareemah yace "In sha Allah."

"To Allah ya kare ka daga sharrin ko wani irin halitta."
Ameen yace sannan ya kashe kiran.

Juya wa yayi zai tafi Sai ya ga daniel tsaye yana murmushi tare da sosa kyeya kaman Wanda yake neman wani alfarma.
Kallon sa yayi sannan ya kawar da Kai yana kokarin mai da wayar sa cikin aljihu.

"Sir MG please ina son magana da kai."
Kallon sa yayi tare da cewa "Ehem! ina jin ka."

Yace "Sir Idan ba zaka damu ba mudan matsa tacan? ya nuna wani waje da bbu mutane ta cikin hotel d'in.

Kallon sa yayi batare da wani tunani a ransa ba ya nufi wajan.
Sanda suka isah MG ya d'an jin gina ya lumshe idanuwan sa ba tare da ya kalle shi ba yace "Kai nake sauraro."

Duk wani abin da yake faruwa akan idon captain Ahmed ne.
Amma da yake Shima ba abin da ya kawo a ransa yasa ya tsaya nesa dasu sosai.
Ganin daniel na shirin ciro Abu daga cikin aljihun sa ne kuma ya nada tabbacin bindiga ne ya sashi fara shan jinin jikin sa.
Ga shi Kuma idon MG a rufe yake. Da sauri ya fara kara sawa wajan da suke a tsaye.

Amma dake da rata a tsaka nin su kafin yayi rabi harya karasa fitowa da bindigan. magana ya farayi cikin garaji Wanda hakan ne yayi sanadin bud'e idon MG amma kafin ya bud'e ido Sai sau kan harbi kawai yaji a gefen cikin sa.

Karar har binne ya jawo hankalin jami'an tsaron da ke wajan.
Bud'e idanuwan sa tarr yayi ya zuba su akan na daniel. Wanda ke wani irin dariyar mugun ta. A lokacin Idan kaga MG baza ayi tsammanin a kwai harbi a jikin sa ba. Sai dai Idan ka lura da yadda jinin kebin jikn sa.
Wani irin huci yake fita da shi Wanda duk d'auri yar mutum a wannan lokaci Idan ya gan shi sai ya razana. Dan idanuwan sa sun sauya kala sunyi jawur.

Wani irin shaqa ya kai wa daniel. Kan wani Dan lokaci idanun daniel ya fara zazza rowa. ganin yana shirin hallaka shine ya sa ya kara d'aga bindigan ya sake masa a gefen kirjin sa.
Ganin Haka yasa captain Ahmed cira bindigan sa Kan ya 'iso ya sakewa daniel ita a goshi.

A lokacin jami'an tsaro suka isoh wajan a kayi saurin rirreke MG da jikin sa gaba ki d'aya ya 6aci da jini. captain Ahmed ne ya kara so ya tallafe shi.

Ga baki d'aya gun ya cika da sojoji. kai kace wani taron sojoji akayi. ga baki d'aya hankulan su a tashe yake Ganin shugaban su cikin wannan ya nayin.

Motar tai makon gaggawa ne tazo in da yan jaridu sun cika wajan makil. kowa koka rin d'aukan abun da ke faruwa ya keyi.
Nan da nan a kayi dashi babban asibiti dake cikin dubai. inda moto cin sojojin dake gaban su da Wanda ke bayan su sun Kai akalla mota sha biyu.

Kai tsaye *_(mass general hospital bostoon International)_* aka nufa da shi.
Manya man yan likitoci ne suka shiga theatre dashi. kokari su keyi na ganin sun ciro harsashan dake cikin jikin sa.

Ummii ne zaune a falo ita da wata 'yar aikin ta tana matsa Mata kafa. ji tayi ga baki d'aya ba ta cikin nutsuwar ta.
Hakan yasa ta umarci d'aya 'yar aikin da take yan ka mata friut data kunna Mata TV.
Hankalin ta baya Kan tv d'in Amma labaran da taji a nayi ne yayi saurin jawo hankalinta wajan.

Idan ba kunnuwan ta karya suka Mata ba, taji a na cewa an harbi MG Abdullahi Abdul-Aziz lamido. Wanda a halin yanxu ba'a san yana raye koh yana maceh ba.
Hawaye ne ya fara bin fustan ta bbu abin da take nana tawa Sai inna lillahi wa'innah ilaihi raji'un.! Wanda hakan ne yaja hankalin yan aikin ta suma ju yawa su kayi Dan kallon abin da ya razana ta. ihu d'aya daga cikin su Wanda ya jawo hankalin sojojin dake bakin gate da cikin harabar gidan shigowa.

A razene suka yiyo cikin gidan, dan ganin abun da yake faruwa. Kan Wanda tasa hanu akayi tana kwalla ihu su kayi suna tambayar ta abunda ya faru dan basu lura da ummi data dade da zama mutum mutumi ba a kwance. Wanda bata gane komai a lokacin. TV ta nuna musu da ga baki daya hankalin su ya Kai kololuwa wajan tashi.
Ihu da sambatun sojojin ne ya dawo da Ummii han kalin ta tashi cikin tashin hankali ta musu umarni da su kaita a sibitin. Dan kuka yaki zuwa Mata gani ta keyi kaman karya ne.

Fita suka yi Dan rakata asibitin motoci uku ne suka cika da sojojin Sai Wanda Ummii take a cikin d'aya. Kai tsaye asibitin suka nufa dan ganin abun da yake waka na....

To be continued

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

*Dedicated* *to* *_ummi_* *_aysha_* (haske Writter )

Page 18

*
Wata irin faduwar gaba ne yake damunta ayau, kuma tarasa dalili.
Hakanne yasa ko waje batayi sha'awan fita ba.
kasan cewar ranar asabar ce, bbu lectures, zama tayi kawai tana tunanin dalilin wannan faduwar gaban tata
Can zancen mutanen na shekaran jiya yafado Mata.
Addu'a tasamu kanta da kara yimasa na Allah yakareshi.
Dakyar taya kice damuwaar aranta, domin kar hameeda ta fahimci wani Abu.

Cigaba sukayi da hidimominsu kamar bbu abinda yake damunta,
Amma Can cikin zuciyarta damuwa ce sosai.
Kusan karfe shadaya 11:00
Tashiga falon babansu dake yana gida bbu office.
Da Sallama Tashiga ya amsa Mata cikin farin ciki,
Nadauka yar tawa yau baza tazo taya abbanta hira bane, saboda akwai yar uwarta kusa da itah.

Murmushi tayi sannan takarasa shigowa ciki, tazauna akasa kusada kafar sa.
Dama wannan ka'ida ne duk ran asabar tana tareda mahaifinta tana tayashi hira "sannu da hutawa baba, yawwa sannu *hannatun* baba.
Murmushi tayi najin dadin sunan da baba ke kiranta dashi.
Tad'i suka fara yi "irin" na d'iya da mahaifinta, cikin farin ciki da annashuwa.

Aljazeerah! Yake kallo, Amma hankalinsu gabaki daya yanakan tad'insu, tunda ta shigo yamaida hankalinsa kanta, danjin ko akwai Wata damuwa atattare da ita.

Saurin daukan remote yayi "yana kara sauti, subhanallahi, Kai mutane babu Imani, wato duk wani mai gaskiya Sai sunga bayansa.

TV take kallo haikam.
wanda tagama tabbatar wa wannan da yanxu ake fadin an harbeshi, A Aljazeerah"
Shine Wanda ranar sukaji Ana zancen kasheshi,
Batasan lokacin da hawaye yafara bin fustan taba, tsan tsan tausayin sane ya cika Mata ruhi,
Lallai wa 'yan nan mutane sun ciki azzalumai marassa imani.

Juyawa baba yayi gunta dan yimata magana,
Tsintar ta yayi hawaye daya nabin daya.
Juyawa yayi yaga yanda take kallo.
TV takurawa idoh, sanin zancen da' akeyi a tv din yasa yayi tsammanin tausayi,
Yabata.

Dan yasan itah! Mutum ce" mai tausayi.
Lallashinta yashiga yi" sannan yace taje daki ta kwanta ,
Tashi tayi ta fita, yabita da kallon tausayi,

Shiga d'aki tayi, takwanta rub da ciki akan gado, Sai zullumin wayannan mutane takeyi aranta.

Hameedah ce" tashigo daka Mata duka tayi, ke Ina kika shiga inata nemanki, saida ta'iso kusa talura da halin da 'yar uwar tata tashiga.
Zaunawa tayi kusa da ita!! Taci gaba da Lallashinta, dan ganinta awannan yanayin tasan ambata Mata rai ne.

================

Koda zuwan su Ummii basusha wahalan shigaba.
Dan akwai abinda sojoinsa suke d' aurawa adam tsen hannunsu.
Ganin haka yasa bbu bata lokaci suka cika cikin asibitin.

Cikin dakin Theatre kuwa,,
Angano dayan harsashin rigar bullet proof dake jikinsa ta tare,
Inda dayan na gefen cikin sa " harsashin bulawa yayi ya fice.
Amma dayake ba Kowani irin harsashi bane, anyi shine na musamman mai hade da guba yasa yaratsa jikinsa sosai.
Gubar mai karfi ce.
Koda kirjinsa da yake da riga Amma sanda wajan yayi shatin baki.

Sun dauki akalla awah hudu akansa.

Kafin sukayi iya kokarin na ganin sun kashe karfin Gubar.

Saida suka kammala komai. lokacin awansu hudu da rabi da shiga theatre.

Inda haryanzu maganin bai fara aiki ba, Sai yayi 1hour ajikinsa kafin yafara kashe Gubar.

Lokaci daya suka gama aka futo dashi, ko numfashi bayayi.

Aka kaishi zuwa wani d`aki mai tsaron gaske.

C I D camera ne takowani sako na dakin.

Nan aka ajiyeshi.

Dan zuwa nan da 2hours numfashinsa zai iya dawowa.

Yanxu roban numfashi ne amaqale a hancinsa.
Wajen dakin kuwa sojojine masu tsaransa birjik, tundaga gate din asibitin.
Ummii kuma na kofar dakin da yake, addu'a kawai takeyi, kokadan tunaninta bai kawo ta "khira mahaifin sa ba.

================

Mai mar taba ne zaune a faadaa.
Wayar sa da ke hannun wani bafade ne, tadauki ruri.
Kallon sa sarki yayi alamun ya amsa, amsa kiran yayi tareda karawa mai martaba akunne.

Sallama akayi ya amsa.
Meh????? Yaushe???? A'inah?? Shine abinda sarki yace, inna lillahi wa'inna ilaihi ra'ji'un kawai yake nana tawa, wanda hakan yaja hankalin fadan.
Rike kansa yayi dayake wani irin sara masa.
Lokaci daya kuma yafara ganin duhu.

To be continued

_Ur's_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_Wannan_ _shafin_ _nakine_ *nafii* _nagode_ _da_ _yadda_ _kike_ _nunawa_ _liittafina_ _soyayya_
_Kodan_ _ke_ _Sai_ _na_ _kara_ _yawan_ _pages_ 😜

Page 19

*

Duk wani tashin hankali, mai martaba yashigeshi. Jin cewa d`ansa mafi soyuya yananan, rayuwa akwai ko babu.

Ganin mai martaba, cikin wannan yanayi yasa akatashi fada Alokacin.
Chapter 9 · 0% Book details