← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 87

Sashe 22

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suna shiga gida dakin suka nufa, tun suna bugawa hankali kwance abu kamar wasa har hankali yatashi bbu irin bugun da basuyi ba amma taki bud'ewa, tsabar rikicewa Dakyar umma tagano extra key's na d'akin tazo ta bude."
Lokacin su amira ansha kuka kamar ransu zai fita. "
Ganinta azaune akan sallaya yasasu sauke ajiyar zuciya."
Cikin kuka amira da hameeda suka nufeta rungumeta sukayi sannan sukaci gaba da kuka. "
Kallonsu d'aya bayan d'aya tayi sannan aranta tace ku dad'i ma kukeji tunda harkunsamu damar kuka."
Shigowa sauran sukayi tambayar duniya bbu wanda basu mata ba amma taki tankawa."
Tsaki mama taja tafice abinta, haknne yasa umma matsowa ta rungumeta, tafara lallashinta sai alokacin tasamu bakin kuka, kuka kawai takeyi bbu wanda yatsareta, ganin haka yasa hafsat da rabi'a suma Jan tsaki suka fice adakin ".
Sanda tayi mai isarta umma sai shafa mata baya takeyi sai Can ta kalli umma tace"
Umma mai na tsare musu? "
Umma wallhy insonsa amma sun rabamu, Cikin rikicewa umma tace suwaye?" idanfa bakin tsaya kinyi min bayani ba bazan gane ba. "
Nan takoro musu duk abinda yafaru yau da irin zaginda yamata."
Bawanda ransa bai baci ba ad'akin, barin anty maman amal datasan cewa k'anin mijinta ne jitayi dagashi har yayansa haushi suke bata. "
Matsowa samha tayi ta riqe hannuwanta sannan tace asiff habibty, ai nafad'a miki kika k'i yarda dani alokacin gani kikeyi kamar wanda son rabaki nakeyi dashi."
Kayya anty samha dama tafad'a tace in tana raye bazanyi aureba, Cikin kid'imewa umma tace wacece Shiru tayi, ta sunkuyar da kayi, hameeda ce tabata labarin komai, Cikin matsanan Cin bacin rai tafara masifa, lallai tabbas halima ta isa,
In sha Allahu sai Allah yamana sakayya. "
Tana fad'in haka tace 'yata share hawayenki in sh Allahu sai kin auri mijin nunawa duniya."
Tana fad'in haka tafice Cikin k'unar rai. " haka suka zauna sukayita rarrashinta har tayi bacci."

Washe gari ma Dakyar taje walima."
Shikuwa najeeb ya d'an samu sauki aikuwa yace shi gida zaikoma, bayadda basuyi ba ganin haka yasa abba yi musu driving komawa garin bauchi, "
Itakuwa labba tana komawa duk aburkice yasa ummii tamabayarta mai yafaru tana fad'a mata taga ummii tafita birkicewa, tsayawa kallonta tayi, ummii ya haka menene ya faru,
Ai batad'au lokaci ba ta shaida mata tanaga kamar itace yarinyar da yayanta yakeso dukda bata da tabbaci amma tanada yak'inin hakanne, ai labba najin haka tafashe da kuka dakyar ummii ta rarrasheta, kiran wayar amira tayi tana d'auka tafara tambayarta *hanna* shaida mata tayi batajin dad'i ne yasa ta koma gida da wuri amma yanzu tayi bacci. "
Aikuwa sassafe labba tashirya zuwa gaida ita, sallama tayiwa ummii tafita jitayi kamar ta bita taga jikin amma dai haka sukayi sallama tabata aika takai mata."
Haka aranar tare suka inii da *hanna* ko awajen walima ma hannunta yana jikin na *hanna* . "
Yau takashance Saturday ranar d'aurin aure sai shirye shiryen d'aurin aure akeyi inda k'arfe 11:30 za'a d'aura."

To be continued

Ur's
_z33yyb3rw3r_
[12/2, 9:32 AM] Anty Jamila D Ili: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

My first novel

_Fans ga garon sallan ku, gaskiya yau bansoyin typing ba amma naga yakamata abaku garon sallah eid mubruq dearest_

Page 38

*

Yau takasance ranar asabar, ranar d'aurin auren samha da Abubakar. "
Wanda za'a daurashi k'arfe 11:30."
Tun safe hankalin *hanna* yake tashe sakamakon kiran da abba abokin najeeb ya mata, " yashaida mata cewa najeeb nakwance a asibiti bbu yanda yake dan ko mutane baya iya ganewa."
Bata k'arasa jin mai zai fad'a mata ba takashe wayan kuka tayi sosai wanda har fuskanta da idanuwanta sun kumbura, sunyi jazir fuskan ta yayi luhu luhu. "
Tun safe ko abinci bata iya cii ba ko ruwa batasa abakinta ba."
Muryarta gabaki d'aya ya dashe dan kuka gabaki d'aya tausayin Najeeb ne yacikata tasan ko meye yasameshi itace sanadi. "
Kuka takeyi ad'aki kamar ranta zai fita, tana kuka tana cewa kayafemin dear wallhy nayi danasanin saninka har nasaka acikin wannan halin, kayafemin."
Har kusan k'arfe goma 10 umma tashigo tasameta Ahaka, dkayr ta rarrasheta,
Umma najeeb ba lpy umma natsani kaina najeeb yashiga wani halin ta dalili na. "
Shhhh my doughter bakene sanadii ba Allah yarubuta hakan sayya faru."
Maza tashi kije ki k'ara yin wanka maza kinji 'yata Ahaka tayi ta rarrshinta hartayi wanka tafito, kaya ta za6o mata tabata ta sanya amma ko powder batasa afuskanta ba. "

K'arfe sha daya da rabii 11 :30 aka d' aura auren samha yusuf dambam da Abubakar umar waziri akan sadaki duba dari lakadan ba ajalan ba."
Bayan and'aura can na hango MG kusada ango kaikace shine wannan ango a irin kyau da yayi, fararen kayane k'all ajikin sa, sai fara'a yakeyi yasan yau tabbas mai martaba da moddibbo zasu nema masa auren *hanna* abinda ya dad'e yanajira shekara kusan goma. "

Bayan angama d'aurin auren, mutane sun watse sosai saura d'ai-d'ai ku,
Moddibbo ne ya kalli baban *hanna* wanda ko ba'afad'abaa sunsan shine mahaifinta danshi yakar6i auren samha ma."
Cikin mutumtawa suka k'ara gaisawa, sannan ya d'aura da cewa, in sha Allah hu akwai maganar da nakeso muyi amma kuma tun da mune masu nema nafiso mubika zuwa chan Bayan kakoma. "
Dan murmusawa baba yayi sannan yace ai tunda Allah yahad'amu anan sai muyi kawai basai kunje ba aikomai sauki ake nema,
Da mamakin su mai martaba ne ya amshe maganar wanda a iya saninsu saidai dogarawa suyi magana amma shi baicikayi ba."
A'a dakun bari dai mubiku tunda mumuke neman arziki sai mubika har mazuninku mu nema yafad'a had'eda fad'ad'a fara'ar fuskarsa. "
Jin haka yasa sukasan maganar mai matukar mahaimmacii ne."
Abba ne yad'an gyara zamansa akasan dayake sannan yace, Allah ya huci zuciyar ranka shi dad'e bawai naja da maganrkaba ba amma ai anan d'in zqifi sauki, Allah yahuci zuciyar ka,
Shiru mai martaba da moddibbo sukayi wanda sukansu sunfi san hakan amma hakan dasukayi shizai nuna damuwarsu da abun. "
Moddibbo ne yayi gyaran murya sannan yace to hakan ma yayi, amma sai mud'an sami wajenda bbu matane."
Tashi sukayi dukansu da waziri da mai martaba da moddibbo suka wuce gidan Abba, kai tsaye falon Abba suka wuce. "
Zama mai martaba yayi shida moddibbo akan kujera yayinda Abba da baba suke kokarin zama ak'asa."
Saurin tsaresu mai martaba yayi A'a katashi kuzauna a kujera kada kud'aukeni a matsayin shugaba ko wani mai mulki ku d'aukeni qmatsayin ubanda yazo nemawa d'ansa aure. "
Had'a baki Abba da baba sukayi suna tambayar aure?"
Moddibbo ne yace kwarai kuma a yarima mukazo nemawa auren d'iyarku, gaba ki d'aya tunani nasu ne yatsaya a iya tunaninsu sunsan d'ansa yarima shine sojan da duk kasar guda d'aya akedashi, kuma kakansa ne mai shagon gwala gwalan dasukafi kowanne ak'asar dubai (abu-dhabi). "
To kuma me zayyi da d'iyarsu?? Mutuminda saninsu ko'yar sarkin saudi yanema zai samu."
Kansa ne ya d'aure, shirunda sukayine yasa moddibbo tamabayar ko kunyi mata miji ne??"
Girgiza kai Abba yayi gumina tsattsafo masa, dan yanzu baba yafara tunanin hameeda akazo neman aure. "
Bayaninda da moddibbo yafara ne yak'ara hargitsa musu tunanin,"
Idan kun amince muna nema masa auren yarku *hannatu* wanda yad'au tsawon shekaru yana dakon sonta, adalilin tana yasa har yanzu baiyi aureba. "
Koda anahaka maganar aure yakan shaida mana yanada wacce yakeso tun muna d'aukan abin awasa harmuka dawo tunanin ko aljance ta aure shi Iya addu'a da rokon Allah munyi amma ko sau d'aya baita6a budan baki yace mana ga garinda yarinyar takeba. "
Koda sunanta bai ta6a ambata ma wani ba."
A'ina gayanta shikadai yabarwa kansa sanii dan baima zauna da wani yayi labari ba balle ya fad'a masa, abinda muka sani shine kawai yana matuk'ar sonta, ak'alla shekarunsa 35 aduniya amma har yau baiyi aureba da'an masa magana zaice lokaci yake jira."
Kuma bana tunanin yarinyar tasani. "
Abba da baba sunrasa awani yanayi suka tsinci kansu farinciki ne kokuma akasin haka."
Shiru Abba sukayi sai can yace hakika wannan lamarii akwai rud'ani aciki, baznce kunyi batar kaiba amma fa yarima kukace da d'iyarmu. "
Allah yaja ran mai martaba, kunsan cewa dai yafi k'arfinta kokadan shiba sa'an auranta bane ina yariima ina *hanna*."
Mai martaba akan yaji zafin maganarsu sai ma sanyi dayaji aransa, dan ba kowa bane za'a ce sunje neman aure yafad'ii wannan maganar ba, " Sai marassa son abun duniya,"
Gyara zama mai martaba yayi sannan yace, har inde kun amince ku kira yarinyar mujita bakinta. "
Shiru sukayi dan tunda dakansu sukazo bbu dad'ii ace basu amince musu ba."
Abba ne afili yace Allah ya za6a mana mafi alkhairi, hakan kuwa yafaranta musu rai alamun sun amince. "
d'aga waya yayi yakira umma cemata yayi kuturomin *hannatu* ina falo na yanzu, sannan yakashe."
Umma dake gefen hannatu ne tajuya ta kalleta,tashi kije abbanku nakiranki yana falo. "
Ba gardama ta tashi ta zura k'atoton hijabinta har k'asa sannan tafice."
Chapter 22 · 0% Book details