← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 87

Sashe 71

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shiga baisamu ummii apalour ba ad'aki yasameta da gudu yak'araso kusada ita cikin tashin hankali yafara cewa ummii *hanna* ummii *hanna* batada lpy, dasaurii ummii tamiqe ganin halinda d'annata yake ciki, dukda bbu hawaye afuskarsa, amma kuma cikin kwayar idanuwansa ta fahimci irin tashin hankalin yake ciki."
Itama da saurin ta surii himarinta ta bishi abaya, danshi yarigada ya futa."
Tsakanin shashin ummii danasu *hanna* danisa amma few minute ne suka kaisu."
Bud'e k'ofan yayi suna shiga, aikuwa sukayi turuss ganin yanda jinii yake zuba jikin *hanna* ga baki d'aya tayi caka-caka da falon."
Duk ta yayyanka jikinta da gilasai, jin bud'e k'ofa yasata juyawa, aikuwa tana ganin su, ta jefo glass na humra dake hannunta, tarewa marshall yayi da hannunsa, nan da nan, hannun yatsage jinii yafara zuba, dagashi har ummiin kanta sukayi yana zuwa kuwa yariqeta kamar wanda take jira ariqeta, tayii luuu tafad'ii hannunsa, sumammiya." kuka ummii tafashe sosai tanayi tana magana." futada ita mota mukaita asibitii." cikin tsawa tace nace maka mufice asibitii."
Waje yayi da ita ummii nabinshi abaya tsabar tashin hankali tunkafin yazo har an bud'e masa mota tsabar irin kirin da yakeyiwa sajen."
Ganin marar lafiya yasa sajen yanufii asibitii direct."
Suna isa aka karbeta ciwukan jikinta akafara, mata dressing, sannan aka ce tana buk'atan jini dan yazuba ajikinta sosai."
Ajikin marshall aka eba aka fara k'ara mata."
Dakyar yayarda shima aka masa dressing ciwonsa, dan yafii jin zafin ciwon jikin *hanna*, ummii Dakyar tasashi yakoma gida yaje yagayawa mai martaba, dan ita bazata iya tafiyaba, alokacinma jimawa kad'an tashare hawaye jimawa kad'an tashare hawaye." Doctor yasanarwa da momy cewa *hanna* tana d'aukeda juna biyu na wata d'aya kacal, kuma sunyiii iya bincikensu basu samiii wata matsala akwakwalwarta ba."
Kuka ummii tarushe dashi na tausayin *hanna* da kuma abunda yake cikinta."
Roqon Doctor tayi da karya fad'awa marshall, dan batasan irin tashin hankainda zai shiga cikinba."
Kwanan *hanna* biyu a asibitii amma abuu gaba yake dad'awa, ganin haka yasa ummii tayanke shawarar sanarda umma, aikuwa ranar sunshiga tashin hankali barinma hameeda da yaya jalal." umma ne tahana fad'awa mama dan tana gudu mata tashin hankali." lokacii d'aya ummii da marshall suka zabge dan kowannensu cikin damuwa yake."
Idan kagansu zaka d'auka sune majin yatan."
Ganin ciwon yak'ii warkewa yasa mai martaba yacewa affan yaje yad'auko modibbo, sukuma likitoci sun bada shawarar fita da ita wajan likitan kwakwalwa."
Dasaurii affan yafito daga shashinsa, wuce kilishii yayi afalo tana zaune, kwala masa kira tayi, kai inazakaje?" umma wallhy abbane, yace ind'auko modibbo inkaishi asibitii, koda abunda zaiyii akan ciwon, matar yaya yareema,"
Gaban ummane yafad'ii, had'erai tayi tace maza jeka kad'aukomin intisar tana gidan hajiya salamatu, waro ido yayi yace umma, abban,,,, tsawa tadaka masa, kai da'allah rufamin baki, kaje kad'aukota tunda bawai guduwa modibbo d'in zaiyii ba."
Fita yayi ransa yana suya, yana fita takira wayan kawarta, tace ke abu ynason kwabewa, yanzu kiyi saurii kafin yaronnan yaje yadawo, a6atarda ita kawai tabar k'asar ga baki d'aya sannan, sannan arufe bakinta kada hankalinta yadawo bazata iya bud'an baki tafad'ii daga ina takeba."
Daga cikin wayan aka ce mata kinsan shifa baya aikii saida sharad'ii, kilishii tace koma menene nad'auka, yanzu fa ko 30 minute kada ak'ara takashe wayan."

To be continued

Ur's
Z33iiyyb3rw3r

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

*Manzon Allah sallalahu alaihii wasallam yace, ku karanta suratul kahfii ranar juma'a, Allah zaicika maka haskenta har wata juma'ar, zaka kasance cikin haske da farinciki."*

================

*Godiya masu kirana danjin mai jiki, Alhmdllhy jiki dasauki, siyama na amsa gaisuwarku tana godiya, nagode sosai queen najii dad'in, kulawarki sosai, Nagode all, Allah yabar k'auna."*

.

================

Page 85

*
Umma ce zaune itada ummii cikin aminity, suna hutawa, sunfita sunbar *hanna* ita kad'ai hameeda kuwa tatafii yin abinci, ko *hanna* zataci dan idan akayi sa'a, dan wani lokaci akanyi sa'a ta d'ancii abincin ko kad'an ne."
*Hanna* na hango tafito daga cikin d'akin da take, doguwar riga ajikinta, kanta ko d'an kwali bbu." hankalin su ummii kwata-kwata bayi wajan, kamar wanda wani abun yad'auke musu hankali."
Har *hanna* tafice acikin wajan bbu wanda yajuyo, haka harta fice daga harabar asibitin bbu wanda yatsayarda ita, dukda alamomii dayawa ajikinta yanuna ba cikkken hankali atattare da ita."
Tana fita ta tsaya atiti kamar mai jiran abun hawa, wata taxi ne tatsaya da wani mutum aciki mai wata irin halitta, wanda kollonsa kad'ai zai saka cikin shakku, kayi tunani koba mutum bane."
Nikaina zuciyata tafii kar kata, dacewar aljanine, magana yayi cikin wata irin murya, mai rikitarwa yacewa *hanna* shigo muje, bbu musu hanna tabud'e motar tashiga gidan baya, nan kamar wata walqiya yaja motar yayi gaba."
Kusan awah biyu suka shud'e."
Can nahango *hanna* tana tafiya duk k'afofinta sun fashe alamun tayi tafiya sosai."
Tana tafiya har tahau kan titi, unexpected wata mota k'irar jeep tazo wucewa ganin mutum akan hanya yasa tayi gefe da niyyar kaucewa, amma inaaa, sai dayazo dabb kamar wanda aka tunzurata, saijin kawai sukayi sun bigeta, salati mutanen cikin motar sukasa, nan suka samii waje suka tsaya, matan dake baya cikin motanne sukayi saurin fitowa sukayi kanta." ganin jinii yanabin kanta yasasu, kwalawa wanda yake driving d'in kira, dasaurii yafito, wani saurayine kyakkyawan gaske, duk wani alamu najikinsa yanuna, cewa shi cikkken bafulatani ne, dan da fullan cinma suke yin magana, amma saidai yanda najii suna fillancin gabaki d'aya ya banbamta, dana k'asar nigeria, kinkimanta yayi yasata acikin motar dake seat ukune da ita, asibiti suka nufa lokacii guda, dake manyan mutanene ba'atsaya bincikeba aka k'ar6eta aka shige ciki da ita."
Basu dad'eba aka futo aka shaida musu cewa, jikin alhmdllhy bataji, wani ciwo sosai ba."
Sannan d'an dake cikintama lapynsa klau."
D'aya matarne tadubi, D'ayan wanda da'aalamu tagirmi D'ayan, tace, diddii naga kamar k'qramar yarinyace kuma budurwa."
Allah dai yasa bawasu mugayen bane suka mata fyade suka yasarda itaba." nisawa wanda aka kira da diddii tayi tace,"
Allah shi yabarwa kansa sanii hussentu, abunda yakamata yanzu ina shii sadiq yashiga?" nisawa hussentu tayi Sannan tace," ya tafii k'ar6o maganinne, to Allah yadawo dashi lpy."
Bayan yadawo da 1hour *hanna* tafarka, duk iya tambayar duniyarnan anyi mata amma takasa bud'e baki tafad'i ko kalma d'aya," da suka isheta da zantuka kawai saita sheqe musu da dariya, harda kyakyatawa, ganin haka yasa suka nemi likita." yana zuwa yafara dube dube, nan aka shiga da ita d'akin na'urorii, iya bincikensu baigwada musu akwai wata matsala, akwakwalwarta ba."
Hakan yafito yashaida musu sunyii matuk'ar mamaki, tunda duk wani alamu yanuna ta6in hankali attatere da ita." 2days aka sallamesu gidansu suka nufa."
Nan diddii tabuk'acii sadiq daya d'auki pics d'inta yazagaya ya aika gidan redio, television, dasauransu, ko za'a dace, Hakan kuwa akayii, and'aukii 5days sadiq yana sanarwa, amma bbu ko batan hanya da wani yazo dan nemanta."
Agajiye liqis sadiq yadawo yazauna, wata mata wanda daga ganii y'ar aikice takawo masa ruwa, bai iya shan ruwanba, yadubii diddii yace," diddii duk iya cikiya nayishi, aksarnan bbu yanda bankai cikiyaba amma bbu."
Nifa atunanina yarinyarnan ba y'ar k'asar camroon bane, camroon na maimaita cikin raina😳🙆,
Allah kawai yakamata mu miqawa komai mucigaba da mataa addu'a, kuma muna nema mata maganii."
Diddii bata iya cewa komai ba sai Allah yabata lpy."

Basu ankara da cewa *hanna* batanan ba saida hameeda takawo abincin tazo da samesu, aresting room d'inda suke zaune tace," Umma nakawo abincin, dasaurii ummii tamiqe tace barina je toh ko zata cii na rarrasheta, d'akin tanufa tana shiga taga wayam, koda mamaki ne yacikata dasaurii tayi toilet nan ma bbu kowa, fitowa tayi nufii gun Umma tana cewa kinga yanda *hanna* tayine? Dasaurii Umma tamiqe tace banganeba? Aimuna zaune dake anan, *hanna* bata d'akinne? Ummii bata tsaya bata amsaba, tawuce tafara dube dube a cikin asibitin, Umma ma tabii bayanta jikinsu duk rawa yakeyi." duk girman asibitin acikin few minute suka zagayeshi, bbu ita bbu dalilinta, bakin gate suka yi suna tambayar masu gate ko sunga fitarta,"
Aikuwa sukace basu ganiba, dan kamar wanda aka rufe musu ido."
Waje sukayi suna tambaya nanma bbu wanda yace yaganta, sunshiga tashin hankali kam sosai, kowacce kuka takeyi bbu mai lallashin wani."
Wani d'an tsoho dazaikai 80yrs, wanda tun fitowar *hanna* shi kad'aine yalurada ita kasancewar, yanada d'an bud'edd'en ido, yamatso kusada su yace," bayin Allah wa kuke nema haka?." dasaurii Umma tace y'armuce tafice daga asibitin kuma kowa yace baiganta ba." shiru yayi nawasu lokaci kafin yace," kafin yace naganta da doguwar riga ajikinta, dasaurii ummii tatashi tace itace wallhy itace."
A'ina take?" girgiza kai yayi yace kucii gaba da addu'a, Allah zai bayyanata, Su kansu wanda suka d'auketa basufii k'arfin Allah ba." zaro ido sukayi mekake nufii kenan da Hakan?" wata y'ar dariya yayi yace, ai addu'a da kuke yi, da wanda mijinta keyi, da wanda ita kanta keyi yasa basu cutarda itaba, yanzu haka tana hannun mutanen arziki, idannace ku kwantarda hankalinku nikaina banmuku adalci ba." kawai kuyita mata addu'a, bbu abunda yafii k'arfinta, atake ummii tazube awajan sumammiyya, dasaurii sukayi kanta, dai-dai tsayuwar motan abban wanda yad'auko middibbo,"
Dasaurii yak'arso baitsaya tambaya ba, ya kinkimi ummii yayi cikin asibitin da ita, Umma kuwa alokacin suka nemi mutuminnan samada k'asa suka rasa, dasaurii sukayi ciki, duk iya tambayar affan bbu wanda ya iya bashi amsa," ganin Hakan yasa yak'ira marshall ya shaida masa yazo hospital."

_Kuyi hak'uri kuyimun uzuri, bayadda na'iya, amma in sha Allah cikin month d'innan zangama_

To be continued

Ur's
z33iiyybawa

*BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

```Dan Allah kada mu gaza wajan taimakawa y'an uwanmu akan buk'atunsu, dan Allah damuwar wasu ta Zama tamu damuwar, koda bazaka iya taimakawa, ta wani hanyarba, yanada kyau, ka taimakeshi tahanyar addu'a, dan kaima watarana, zaka buk'acii ataimaka maka koda tahanyar addu'a ne danshine babban tainakon da mutum zaimaka aduniya." nidai zaynab bawa ina buk'atar addu'oiinku daga bakunan ku masu albarka."
Balaifii bane kuma ba gazawa bane ko kankastar dakai neman taimako na addu'a ba, tabbas bakasan bakin wani ba, danna roqii alfarmar addu'a awajenku nasan zakuyimunne, nagode."```

================
Chapter 71 · 0% Book details