← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 87

Sashe 80

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jikin *hanna* duk yagama yin sanyii wato namiji ba d'an goyo bane, agabanta ma yake gwada mata yanda suke soyewa."
Kawarda kanta tayi hawaye yana zuba, a idanuwanta shikuma duk maganarda yakeyi idanuwansa yanakan *hanna*
yaushe aka d'aura auren?" yatambayi intisar, hmm d'azu ko 2hour's ba'ayiba, dan Allah kadawo yau wallhy ina bukatarka, murmushi yayi yace, dole ndawo yau, tunda burinki ycika, wata dariya tayi tace tabbas burina yacika, ok tom dama sak'o ne nakeson fad'a miki kanna iso, dan nasan idan na iso ba lallai nasamu damaba, hayaniya da kuma abubuwa, cikin kissina tace hakane kam my love inajii."
Intisar nasakeki saki d'aya, dasauri *hanna* tad'ago tana kallonsa, 😳intisar nasakeki saki biyu, intisar nasakeki saki ukuu, Wallhy banta6a sonki ba, bakuma na tunanin zansoki, koda nan gaba, Wallhy bazan ta6a son wata mace ba, bayan *hanna* murmushi ne yahad'e da hawaye fuskar *hanna* idanuwanta nacikin nasa kamar yanda shima nasa idanuwan ke cikin nata tunda yafara magana."
Idan kinsamu miji ayanzu and'aura miki aure, baki da idda, Wallhy sau dubu za'a d'auramun aure, aranar saina saki matar."
*Hannan* nandai ita kad'ai nakeso, kuma bazan daina sontaba har k'arshen rayuwata."
Yafad'a had'eda kashe wayar itakuwa intisar tun kafin yagama magana tasume, sai kqwayenta dasuka gamajin komai."
Suka ruga kiran umma (kilishi)."

Sukam su i'shaq anbarsu da kallon abun al'ajabi."
Ware mata *hannu* yayi dasauri tana tatashi tana guduu ta fad'a jikinsa tana, kuka kamar ranta zaifita, shima rufeta yayi ruff, yanajin, wani irin farincki."
Sunfii 20minute ahaka bbu wanda yagajii, dan kanta yana dai-dai zuciyar sa, tanajin bugawar zuciyarsa, ta lumshe idanuwanta."
D'ago kanta tayi tafara dukan k'rjinsa hannu bibbiyu, dariya kawai yakeyi dan bazai iya hanata ba."
Ta turo baki tace, da tafiya zakayi kabarni ko?" girgiza kai yayi yace duk yanda kike jikina yana bani."
Bazan iya barinki ba." yanzu harna kama hanyar airport najuyo jikina yabani kina nan."
Murmushi tayi tace, tun jiya nake zuwa wajanka, tanuna wani soldier wancan mummunan ya hanani ganinka, nida mijina."
Kama kunne yayi yace, amai afuwa cutie baisonki bane, nasake sabon soldier 's."
Sai a lokacin ta tunoda da su inne kunya takamata, tafara kokarin kwacewa yak'i sakinta, ahankali tace ana kallonmu fa honey, d'aga gira d'aya yayi yace ina ruwana."
Dakyar takwace tajuya garesu tace, diddi ga mijina nan, da fara'a diddi tace ainagani, yanzu muje gida amiki wanka sai kutafii naga yana hanya."
Tajuya ta kalleshi tace sune way'anda suka rik'eni tsawanon 8month, dinnan."
Marshall yabawa i'shaq da sadik hannu suka gaisa, yagaidasu diddi yace, yanzu please muje gida, sai muyi magana acan, sunfara, mota suka nufa."
Amota yake ce mata, cutie cikin yazube ko?" girgiza kai tayi tace, A'a jiya nahaihu, matarda kabawa jini a hospital niceh, murmushi yayi yace jikina yabani kina asibitin." yanzu ina gudan jinina."
Harara ta wulla masa tace ni kad'ai fa nayi nak'udar, marairaicewa yayi yace cutie kinsan da ina nan, da tare zamuyi, yanzu ina yake ya fad'a cikin zumud'i."
Yana wajan diddi bari mu isa."
Suna isa marshall bbu kunya yazage yatambayi d'ansa kawo masashi akayi." kallon yaron yakeyi kamar ya had'iyeshi dan soyayya, kamninsu d'aya, sai peck yake bawa yaron, inne tatsaya tana kallon yaran zamani."
Aka shigada *hanna* wanka." Sanda diddi tamata wanka tace, takawo mata abincii, tazauna takii, dan tunda sha tea takicin komai tun jiya."
Ai kuwa cin abincinta tayi sosai."
Tana gamawa marshall yaroqi akan dan Allah su tafii nigeria tare, yanzu yasan ana jiransa agida."

Dake bawani abuu sukeyi ba, yasa suke amince aka dugunzuma duka akayi nigeria."
Nan jirginsu yad'aga."

To be continued
[25/10, 01:49] Zaynab M Bawa Fbk: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

_Here is your third Page my *HAJJA CE* ILYSM_

*NOTE*_ _naga sakonninku dayawa nacewa wai baikamata marshall yasaki intisar ba, kusani cewa Allah yace ka aurii mace d'aya idan zakayi mata adalci, sannan yace idan kaza iya adalci zaka iya auren mata biyu, idan zaka iya yiwa uku adalci, ka auresu har izuwa hudu, amma kowanne sai ankira adalcii atsakani, d'ayanma idan baza ka mata adalci ba and'auke maka baizama wajibi ba, kusani cewa bawai sonkai bane yasa marshall yasaki intisar ba A'a saidan yana nemawa kansa adalci, baiso yatashi gobe kiyama b'arinsa d'aya ashanye, yasan bazai iya adalci bane yasa Bai cutar da itaba."_

.
================

Page 97

*
Hafsat da hameeda, duk gidan mai martaba za'a fara kaisu, dake ita hafsat mijinta d'an libya ne, shikuma G. Ahmad gidan yatashi." daga bauchi duka aka d'aukosu, sukayi kano."

Kilishi atsorace tajuyo jin irin kiranda, k'awar intisar take mata."
Tashi tayi dake tana cikin k'awayenta tana tambaya, manene yafqru haka aikin tsoratani."
Agigice tace intisar tasume." Saka hannu akayi, Kilishi tayi tace, wana irin tasume manene yasameta, ke kinada hankali kuwa."
Yarinyar tafara wallhy umma ba k'arya nakeyi ba."
Angonne yanzu yakirata waiya saketa saki uku shine......?" aibata k'ara saba, Kilishi ta danno wani ashar dan babban,,,,,,, ta mako shi, dan uwarsa k'arya yakeyi, ba'ahaifi kakar uwarsa bama."
Tana danna ashar tawuce zuwa shashin mai martaba, danko takan intisar batabii ba."
Yana tareda bak'ii amma taso shiga aka hanata."
Zuciyarta tana zafii tawuce shashin ummii, wanda ke zaune batasan abunda ke faruwa bama."
Tana shiga ko sallama batayiba, kuma gamutane ashashin y'an uwan ummii tasukazo, bikin ahmad, dake dan k'anwartane mamanshi da babanshi sunrasu tun yana yaro duka iyayensa larabawane, kasancewar and'auke marshall lokacin yatafii makarantar army, yasa tanemi abatashi, bawanda yamata gardama, aka batashi tagoyashi."

Tana bankad'owa tasamu ummii acikin en uwanta, tatsaya tak'ara musu kallo, sannan tace matsiyata(😳😳kajimun mata, wai su ummii ne matsiyata 😂😂😂kishiii) shegu munafukai, tajuyo ga ummii tace, munafukar uwa kin zuga d'anki yasaketa ko?" To wallhy kijira kiga abunda zaibiyo baya." idan wannan shrgiyar matar tasace, yarabu da ita har abada, yacire raii da ganin tama."
Tabisu da kallo wanda suka tsaya suna kallon ta, batareda sunsan abunda take cewa ba, idan kacire ummii, itakuwa bata tanka mata ba, har tagama tafice."
Har cikin ran ummii bawai tajii dad'iin sakinda marshall yayi bane, duk da cewa bason auren takeyi ba, amma kuma aitunda anrigada and'aura yakamata yayi hak'uri." ba tasan lokacin da taja tsaki ba, en uwanta suka tsaya kallonta suna tambayarta menene yafaru?" nan tashaida musu abunda marshall yayi, masu yawan cikinsu sunyi murna wasu kuma suka jajanta abun."

Bayan mai martaba ya sallami bak'insane zance yakai kunnensa, ransa ya bala'in baci, bai ta6a neman abu yarasa wajan yareema ba saiyau."
Tunfarko dayace bazai iya aurenta ba, bai maida masa yarinya bazawara ba."
Duk da cewa amatsayin budurwa take, bahakanne zai hana mutane ce mata bazawara ba."
Yakira layin marshall yafii sau 80 amma baishiga ba."

Intisar bata farfad'o ba sai da tayi 2hour's, da kuka tatashi, takasa magana, babu abunda yake cimata raii kamar yadda ko 2hour's ba'ayiba da d'aura auren yasaketa, dake ita kad'aine daga ita sai Kilishi yasa tace, Wallhy ummma gobe gobennen kije kiyi abunda za'akashe wannan yar banzan, Wallhy tamutu kawai, natsaneta, ta dalilinta yamun wannan cin mutumcin." wallhy umma shima kada ki kyaleshi, duk sonda nake masa yanzu najii natsaneshi."
Kawai kimin maganinsa, yadda bazai k'ara wulakanta wata mace ba."
Kilishi tace haba y'ata aikema kinsan wannan zaunannan zance ne."
Dole zan hukuntashi dai-dai da laifinsa, yanzu ki kwanta ki huta." futa Kilishi tayi tabarta tana, jin zafii da yanzu tana shirin zuwa wajan diner."

Ummii takira afeeya ta fad'a mana, afeeya harda ihu da tsallan murna." tana cewa wallhy yaya yareema yabiyani arayuwa, tsaki ummii taja tace kyajida shirmanki, sannan takashe wayan."
Da yamma aka kawo su hameeda da hafsat, nan shashin ummii aka saukesu, dan Kilishi bazata sauraresu bama."

Harda mama akawo amare tadubii, ummii tace, amayar yarona tana inane, danni tawajnta zanii."
Murmuahin k'arfin hali ummii tayi tace, kayya wana yaronki mai jawowa mutane abun fad'ah, kamar yaya mama ta tambaya."
Ummii tace ana d'aura auren yakirata ya mata saki uku."
Salatii mama tad'auka tama kasa magana, sukuwa y'an uwan *hanna* dake wajan dad'ii ne yakamasu."
Mama takasa cewa komai kawai tayi Shiru, fahimtarda ummii tayi Jikin mama yayi sanyii yasa tace, kinsan Allah bazan masa fad'a ba."
Lokacinda da suka yi shawarin auren bbu wanda ya shawarceni." ballantana natausheshi, gabaki d'aya nunawa sukayi banda iko." Sannan yanzuma daya gwada musu halinsa nima bazan tsawatar masa ba."
Allah yakyauta mama tace, sannan tace amma yarima baikyautba gaskiya."
Chapter 80 · 0% Book details