← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 87

Sashe 12

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dumbin taron jama'a ne suka zo taryansa, inda daga masarautarsu ma gayya gudane. Sannan ga governor da sauran Manya, hadda shugaban sojoji wato chief wanda afuska Sai farin ciki yakeyi sosai, azuciyar sa kuma da dadama daya kasheshi a wajan.

Gabaki daya suka dugun zuma sukayi, masarauta.

To be continued

_Ur's_
_z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Page 23

*
Masarauta duka suka nufa" nan da nan kowani sako da lungu, na cikin masarautar ya dauka " *yareemah* ya isoh, dan ko ba'a fada ba yanda masarautar tadauki kidan algaitu da ko ina hakan ya'isa yasanar da isowar *Yareeema*".

Cikin fada suka nufa kai tsaye" inda mai martaba da mukarrabansa suke jiran isowarsu".

Sanda suka gama kwaasan gaisuwa, sannan suka nufi dakin da mai martaba da iyalansa suke cin abinci ".

Aranan idan kaga fuskan MG koda bai kasance mai fara'a ba" amma fuskansa ya nuna yana cikin farinciki".

Sosai aka tanadar musu kalolin abinci", duk daman sababban abu ne agidan sarauta, amma nayau daban yake".

Duk iyalan mai martaba suna tare awajan".

Abinci sukeci cikin kwanciyar hankali da farinciki, irin wanda suka dade basuji ba.

Dan sundau tsawon lokaci basu hadu haka ba.

Bayan angama cin Abinci ne " duk suka tare a falon mai martaba, tadi sukeyi Sosai irin na yan uwan da suka dade basu zanta ba".

Kana kallon wannan zuri'a sai sun burgeka" sun baka sha'awa irin yadda suke tadi kai ahade, dan awajan baza ka taba banbance cewa wannan dan wannan bane.

Affan ne ya kalli MG yace" ya yareemah wai Yaushe wannan antynmu mai sa'ar tadazo ne???? Kallon sa MG yayi" cikin tsolaya ya kashe masa idoh daya, eh ai ya kamata musanta yanzu gaskiya, nan da nan kamar wanda suke jira ayi magana suka hau kansa kowa so yake koda hotonta a nuna masa, dan sun tabbata tacika mai sa'a, samun miji irin yareemah yana wuya"

Gaban intisar sai faduwa yakeyi, Cikin zuciyarta tana addu'a Allah yasa itace wannan mai sa'ar",

Wacce naji sun kirata da anty surayya ne da karbi zancen, itace first born a yaran mai martaba.

Yareemah yakamata ka duba wannan zancen, tajuya ta kalli duk mutanen falon, sannan tace " ka kalli irin farincikin da muke ciki yanzu, kuma inada tabbaci da'akwai matarka a ciki, farincikin mu saiya fi haka, bakunan mu sayya fi haka budewa.

Duk danginna bamuda burin da yawuce" muga iyalinka kai kanka kasani duk zuri'ar mu babu mutumin da ya kaika soyuwa cikin rayukanmu.

Kokasan iyayaenmu basuda burin daya wuce ace" yau sunga 'ya' yanka, kokasan shiru kawai suka maka dan basasan abinda zai takura ka, amma bawai dan sun hakura da zancen auranka ba" shekarunka fa talatin da biyar 35 'yan mata sun kusa su fara cewa kamusu tsufa, sai irinsu affan, tafada cikin sigar tsolaya.

Ganin kansa akasa yasa suka fidda ran samun amsa".

Mai martaba dama yasan basuda amsar wannan tambayar, yasa bai samusu baki ba, dan sau dayawa yakan zaunar dashi yana masa wannan maganar" amma amsar sa daya na wannan yarinyar, sujira da sauran lokaci, amma da mamakinsa gani yayi ya dago kansa da murmushi.

Wanda duka falon Sanda abun yabasu mamaki, dan irin wannan murmushin yin su awajan sa nada wahala",

Cikin zumudi wanda kwata kwata basusan shi da hakan ba yafara magana cikin muryarsa mai dadin sauraro baga mata ba har maza" wanda jinta yakanyi tsada", kodan yasan hakanne yasa yake rowar jinta" ohow"🤷‍♀ idan wannan ne karkudamu matsalarku tazo karshe, nan da 1 to 2 month mai martaba zasuje nemamin aure" gaban kilishi ne ya fadi cikin razana da dubur bur cewa tace " a'iinah???

" Bauchi" yafada batareda kawo komai aransa ba".

Wuta ne ta daukewa intisar da kilishi"

Inda duk dakin sai farinciki ya lullubesu gabaki daya sun rasa yadda zasusa kansu don murna.

Affan harda taka rawa, inda mai martaba da ummii kuwa yanda kasan anmusu albishir da gidan al'jannah, Sosai baku nansu yaki rufuwa.

Inda duk Abinci akeyi kilishi da intisar basa fahimtar komai.

Halima ce ta zakud'o cikin zumudi sanda tazo gabasa taruko hannuwansa, *ya* *yareemah* itace wannan wanda kake dakon santa kusan shekara goma,??? d'aga mata kai yayi " yaya kaima Allah yasa tasoka kamar yadda kake sonta.

Affan ne yayi saurin karbe zancen da'allah malama rufa mana baki, wacece zata kalli yaya tace bataso" ke kanki kinsan duk zur'ar mu bbu mai kyau da kwarjininsa, kallon ummii yayi cikin tsolaya yace" aiko ummii wanda take cikakkiyar balarabiya bbu abinda zata nuna masa, duka ummii takai masa tana girgiza kai irinna shirmen affan.

Kayyyah" affan barta tamun addu'a dan banida wannan tabbbacin akan zata soni, akwai mutanen da kyau da kudi da dukiya bai damesu ba, batasan koni waye ba balle tasoni.

Amma inada tabbbacin arananda nayi asarar ta aranan rayuwata amfaninta kalilan ne, kuma har inde narsata toh bazan iyayin aure ba, yakarasa maganar cikin sigar da duk wanda yake zaune awajan sanda matsanancin tausayinsa yqamasu,

Ummii har idanuwanta ya cicciko dan ita take zaune dashi ita kadai tasan irin son da yake yima wannan yarinya".

Mai martaba ne cikin sigar kwantar da hankali yace " *Yareeema* na karfa kamanta kai soja ne, mai juriya da kuma gwarzon taka, eyyah abba ata wannan fannin gaskiya ni rago ne.

Yana fadin yatashi da niyyar futa, wanda bayar iyayensa da yan uwansa da dumbin tausayinsa, affan ne yayi karfin halin cewa yaya baka fada mana sunanta ba".

================

Nayi tafiya ya plz fans kuyi hakuri dan banida tabbacin kullum zakurunga ganin post dina harsai danawo zai dawo normal bye love uuuuu olll

To be contunieud

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

*BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Page 24

*

Juyowa yayi ya kalleshi sannan" da murmushin dake boye da damuwa acikinsa".

Girgiza kai yayi yajuya daniyar futa" mai martaba ne yatsareshi" yareemah " fadamun sunan surikata kaji".

*"Hanna"* wow"😍 halima tace" hadeda hada yatsunta biyu waje daya sannan taware guda ukun amma sunan yayi ".

Murumushi yayi kawai sanna yajuya ya fuce.

Sojojinsa ne" suka rufa masa wasu na gaba" wasu na baya" suka sashi atsakiya, harzuwa wani tangamemen sashi wanda idan kagani, za'a iyacewa na mata hudu ne", amma gefen MG ne wanda yake rayuwa shi kadai".

Gefe daya gida ne mai hawa biyu" sainabiyun wanda suke jere amma shi plat ne mai matukar kyau duk yanda zan kwatanta muku kyawun wannan gida bamai yiyuwa bane, iya karshen kyau" gidan yayi kyau " plat din ya nufa" wanda kofarsa duk ta glass ne' irin glass din da ko bullet baya 6ulashi".

Wasu lambobi aka danna ajikin kofar, da'alamu kofar mai sucurity ce ", kofar ne tabude inda wasu daga cikin sojojin suka fara shiga, sannan shima yashiga", wani falo ne dan madaidaici mai kyawun gaske" komai na falon farine sol har daukan ido yakeyi",

Daga dukkan alamu dai yafisan kalan farii".

Har mamaki irin kyawun falon yakeban, amma nace bafa abin mamaki bane dan idanna yi la'akari da falon MG ne, kuma sanin kankune kunsan waye MG".

Daki kai tsaye yawuce dan yin wanka ".

Can cikin falon mai martaba kuwa, farin ciki ne da kuma tausayin *yareemah* da yabarasu dashi, sa6anin kilishi da intisar Wanda bakin cikine fall a zuciyarsu, intisar jitakeyi kamar zuciyarta zai futa dan bakin ciki ga wata irin kishi daya lullubeta, har cikin ranta ba karamin so takeyiwa *Yareema* ba" ita kuwa kilishi zafin dukiya da mulki yakusan kubucewa ahannun su " amma duk yanda za'ayi bazata bari ya auri wannan yarinyar ba" duk rintsi sai ta rabashi da itahh".

================

*Hanna* sun gama exam lafiya", inda se shirye shiryen zuwa kano, inda zuwansu yahadu da bikin anty samha da za'ayi sati biyu masu zuwa, inda soyayyarta da najeeb sai karuwa yakeyi kullum idan basa maqale a waya toh suna gidan anty suna zuba soyayya, abu daya dayake damunta shine yanda najeeb yayi shiru da zancen turowa gidansu kokadan yadaina mata maganan,

Yau sauran kwana biyu sutafi kano, yaya jalal ne zaizo yadaukesu, sai shirye shiryen tafiya sukeyi.

*Hanna* ce" tafito cikin sauri " daga alamu wani waje takeson zuwa, ammah ce azaune acikin gida, lokacin hanna tafuto wayan tane tafara ringing, hankalinta baikai kan Ammah dake zaune acikin gidan ba, daukan wayan tayi tana cewa, myn gani fa ahanya inazuwa, gaban Ammah ne yafadi dan dagajin wayan da wani take" kuma da alamu saurayinta neh, me hakan yake nufii kenan???? Ta tambayi kanta".

Fucewa tayi cikin sauri dan zuwa gidan anty dasu hadu da najeeb, yaso ace shizai kaisu Ammah yasan hakan ba mai yiwuwa bane, bbu yanda za'ayi iyaye subar yayansu yakaisu" yana matsayin saurayi ba muharramunsu ba".

Bayan isarta gidan anty, tasamu najeeb ya dade dazuwa, sun dade suna hira, sweety" dagowa tayi ta kalleshi" kinji haryanzu bance komai gameda maganar turo manya ba ko???"

Sunkuyar da kanta kasa tayi"

Yaci gaba da cewa"!!!!!

Narasa mai yasa duk lokacin da zansamu abba da wannan maganar, sai wani abu yatsareni" kuma nakan dade bankara tunowa ba kuma akowani lokaci nayi tunanin zuwa hakanne take faruwa " muringa yin addu'a dan jinakeyi kamar akwai wanda keson rabamu, narai narai yayi da ido" idan narasaki zan shiga wani hali, irin son da nake miki ni kaina bazan iya fadin sa ba", wani irin tausayin kansu ne yakamata'.

Murmushi tayi, addu'a ne yakamta muyi dan babu abinda yafi karfin addu'a".

Shima murmushin yayi zanyi kewarki" amma zanbiyoki kano, kinji sweety, umm lokaci yana tafiya, hameeda tana jirana zamu shiga kasuwa," ok bari inkaiku" no kabari" kollon tuhuma yamata" wai meyasa haka" hah" nafarko idan na baki abu bakya karba" idannace ko makarantarku zanzo saikikii" dan bakyaso kishiga motata?? Eyehh??

Langa6ar da kanta tayi" hava myn tayaya zan karbi abu ahannunka" ace a'iinah nasamo?? Kaikanka kasani dole sai an tuhumeni".

Sannan zancen zuwa makaranta kuma" kaikanka kasan zancen duniya baya buya idan akaje akasamu, babanmu akafada masa fah," mai zai dauka yaturani karatu natafi soyayya??"

jikinsa ne yayi sanyi" yasan duk laipinsa ne, in sha Allah yakusan zuwa karshe kinji sweety,"

Murmushi kawai tayi amma aranta itama tana fatan faruwar hakan".
Chapter 12 · 0% Book details