← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 87

Sashe 36

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

*
Bayan suna da kwana biyu, Zaune suke ad'aki su shida,suna hira, *hanna* , Hameeda, amira, hafsat, adda hindu, rabi'ah,"
Amira ne tad'an gyara zama, ta kalli *hanna* tace, ke nifa wajenki nazo, biki sai k'aratowa yakeyi, amma ko zancen anko banji kin fara ba. "
Ta6e baki *hanna* tayi sannan tace ni wasu k'awaye nake dasu da har zan wani fidda anko."
Harara adda hindu ta galla mata, sannan tace da'allah tafi kibawa mutane waje, "
Amira ne tace" adda wallhy bakiga yanda 'yan matan level d'inmu masu shegen girman kai suke kirana akan idan an fidda anko nakawo masu."
Daa se shegen girman kai ko kallo mutane basu ishesu ba."
Amma yanzu sai wani kirana sukeyi, wato sunsan cewa nice frnd d'inki insasu acikin frnd. "
Dariya Hameeda tayi tace ai wollah ko nice zan yi haka, dariya dukkansu sukasa." "
Adda hindu ne tace wallhy kuncika yarinta da yawa, "
Harara *hanna* ta galla mata tace wai dame kika girmenine?"
Wani irin kallo adda hindu ta watsa mata tace" ke nifa inada yaro. "
Saidai yaronkan injii rabi'ah,"
Dan kinsan nidai baki girme niba. "
Yakamata dai kufara bani girma danni yanzu na wuce sa'ar ku." inji adda hindu,
Hafsat ce tace nikam dan Allah kubar wannan abun yanzu musan abinyi,"
Dan gaskiyar amira ne yaci ace yanzu munfara shirye shirye. "
Ana cikin haka Massages ya shigo wayan tana dubawa taga MG ne."
Anrubuta zankiraki 8pm plz pick it. "
D'an siririn tsaki taja wanda yaja hankalin Hameeda ta kai kallonta kan screen na phone d'in,"
Rike baki tayi tahau salati, yanzu ke *hanna* idan zae kiraki Sayya nemi izini? "
Ina ruwanki bansan munafurcii," inji *hanna*
Rabi'ah ne tace kyaji dashi anaso ana kaiwa kasuwa."
Idan ba haka ba waye zai samu mijinda samunsa na wahala kuma kice bakyaso inbanda gulma. "
nifa kun fara isata inji *hanna* idannace bana sonsa ina ruwanku?" ai ba'aso dole."
Hameeda ne tace ku rabu da ita duk munafurcii ne."
Allah adda baku ga ranarda muka fara had'uwa dashiba dan ya tsaya yimun magana shinefa ranta yabacii ta koma Cikin gidanki da b'acin rai. "
Kuma idan ba haka ba gata ku tambayeta,"
*Hanna* ganin batada na cewa yasata yin shiru da suka isheta ta fice tabar musu d'akin."

Ummii ce zaune a falonta, itada afeeya da anty hibba da kuma afeeya,"
Shirye shiryen zuwa had'o kayan lefe sukeyi, jibi zasu tafii Yayinda intisar kuma nanan wani irin zazza6i ne yarufeta, har kullum wani irin son MG ne yake rufeta wanda, tarasa yanda zatayi duk wani hanya dazata bi wajan nuna masa tana sonsa abun ya faskara dan baimasan tanayi ba."
Yana chan yana son maso wani kamar yanda itama intisar takeyi,
Koda affan yaji mai yake damunta hakuri kawai yabata dan ya tabbata cewa yayansa yayi nisa baijin kira, "
Dan irin sonda MG ke yiwa *hanna* Koda ta aureshi wahala kawai zatasha,"
Da haka yayita bata hakuri sannan yace har in dai mijin kine to bbu makawa sai kin aureshi, komin dad'ewa, dan yayi aure hakan bawai yana nufin bazai k'ara wani ba kenan."
yayi mata haka ne kawai dan kokad'an baison intisar ta aurii MG dan aganinsa kokad'an basu dace ba."
Kamar yanda yakejin intisar amatsayin yar uwa haka yakejin *hanna* bazaiso ko d'aya ta cutu acikinsu ba,"
Da haka intisar tasamu ta warware, dan yanzu tasa aranta ko bayan auren saita samu hanyar da tayi ya aureta."
Chapter 36 · 0% Book details