← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 87

Sashe 79

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basukai ga bata amsa ba, nurse tashigo d'aukeda jaririn aciki bed nasu tana turashi, zagayanta uku kenan, tana samu *hanna* bata tashi ba." k'arasawa tayi gaban gadon tace, kin farka, tafad'a tana ciro yaron, kar6eshi ki shayar dashi, kwanansa d'aya bai cii komaiba."
Dakallo tabi mutanen d'akin, ita dai bata ta6a sanin tanada ciki ba balle kuma har yaro, d'aga mata kai inne tayi tace k'ar6eshi, yaronki ne, saka hannu *hanna* tayi tak'ar6i yaron Sanda gabanta ya buga, kamannin yaron d'aya sakk da ubansa." kallon su tayi tace nashiga uku, dama inada ciki ne, yaushe?" k'arasawa kusada ita inne tayi, tace ki kar6i yaron ki shayardashi zanmiki bayani." riqe yaron tayi dakyau,"
Futa i'shaq yayi yabarsu ad'akin."
Tace wallhy bazan shayardashi ba harsai nasan ku su waye." wannan yaronkam ko ba'a fad'aba nasan yaro nane, kama bazata nuna k'arya ba."
Idankuma mafarki yakeyi plz kutasheni."
Ba mafarki kikeyiba injii inne, watanki takwas awajanmu, zaro ido *hanna* tayi tace wata takwas, kwarai kuwa injii, diddi, tun lokacinda muka tsinceki, bamu sameki cikin hankalinki ba, munsameki baki da bakima balle kiyimana bayani."
Kuka tasaka kawai tarungume yaron tsammm ajikinta, tana Kuka tace nagode muku, nagode sosai da kulawarku, samun mutane irinku sai an tona."
Amma dan Allah kada kubarii yatafii agarinnan wallhy yananan, dan inada tabbacin wannan jininsane," a lokacin i'shaq ya shigo da sallama yace." hasashenki bai zama gaskiya ba."
Wannan wani soldier ne yaji ana neman jini yabaki."

Murmushin takaicii *hanna* tayi cikin babbar murya tace, field marshall Abdullahi abdulaziz lamid'o, zaro ido daga nurse d'in har i'shaq dayanzu yaje yatambaya yayi, dan sunanda aka gyamasa kenan."
Takawarda kai gefe dan jikinta ciwo yake mata, k'arfin hali kawai takeyi."
Zama i'shaq yayi baida bakin magana."
Sai a lokacin hussentu ta dawo itada sadik, daukeda kayan tea ahannunta, had'a mata tea d'in akayi sannan aka miqa mata, wata iriyar yunwarda takeji tasakata shanyewa tass."
Sannan tad'an koma ta kwanta."
Diddi ne tace yaronnan yanajin yunwa, kibashi abinci."
Shiru tayi kamar bataji ba, Sanda tad'auko yaron tasaka mata shii agabanta."
Tashi *hanna* tayi tak'ar6i yaron, diddi tagwada mata yanda zatayi, kunya yasa ta sakashi cikin hijab, tafara bashi." runtse idanuwanta tayi tanajin son yaron akowani ga6a na jikinta, yafiii 30 minute Sanda tajii alamun yayi bacci sannan tacireshi."
I'shaq ne yashigo, yadubi *hanna* yace," ganinsa zai mun wahala sosai, yanzu tunda an sallame muje gida kiyi wanka, sannan mutafii wajansa."
Tattarawa sukayi suka koma gida, nan diddi ta wanketa itada yaron tass, cikin kayayyaki masu tsadar gaske, wanda i'shaq yasaya aka sakawa yaron."
Sai yamma liqis suka nufii hotel d'inda yake, amma tundaga compund d'inda yake furr akaqi barii su shiga."
Har magrib suna wajan, receptionist kuma sunki kiransa awaya, tundaga nan *hanna* tafara kuka."
Dakyar suka lallasheta takoma gida."

Washe gari kuwa, can nigeria sai shirye shiryen d'aurin aure sukeyi, kasancewar yanda abun zaifii sauk'ii yasaka, aka d'aura dukkanin auren akano."
Ababban masallaci da farko aka fara d'aura auren *hameeda da Ahmad sannan bilal da hafsat."
Ak'arshe aka d'aura auren marshall da intisar, bayan angama akayi reception." kowa sai tambayar marshall yakeyi amma kuma bbu shii."
Hakanne yasa mai martaba yad'aga waya, yakira shi, cikin zafii yace masa yanaso ayau d'innan yakwana agida, duk abunda yake yi, yabari yazoshi, and'aura aure, kashe wayar marshall yayi tsabar ba k'in ciki Sanda yayi kuka."
Nan danan idanuwansa suka kad'a sukayi jawurr."

Ba'adade dafad'a masa wannan maganarba, kawai saiga wani soldier yashigo sara masa yayi sannan yace, yalla6ai, tun Jiya wasu mutane sukazo wai sunason ganinka." yauma gashi sundawo."
Cikin zafii marshall yace, bazan samu damar ganin kowaba, yanzu haka and'aura aurena, kasanar nanda 30 minute zantashi zuwa nigeria."
Da toh ya amsa yafita yana tausyin agonnasa duk dacewa bawai yadad'e dashi bane, amma anfad'a masa bacewar matarsa dayake bala'in so."
Samun su *hanna* yayi yace, ku tafi oga, bazai saurareku ba, yana cikin wani yanayi, yanzu aka d'aura aurensa."

*Hanna* dake zaune Sanda tazube k'asa, dan firgicii, zata sake magana yayi saurin katseta ya wuce abunsa."

To be continued

Ur's

Z33iiyyb3rw3r
[25/10, 01:48] Zaynab M Bawa Fbk: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

_Your secound page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al'umma."_

*Idan kuka kalli, late reponds Kuyi hak'uri massage suna yawa wallhy har taraddadin bud'e data nakeyi dan nasan abunda zan tarar, Allah nafiku k'aguwa na gama na huta." dan Allah idan kinyi magana banyi reponds ba amin uzurii." kunsan d'an adam ajizi ne, nima inasonku danna tabbatar masoyinka shike nemanka." ina sonku sosai."*

*Y'an group dina kad'an yarage ayankani yau." nadaiyi nahuta😒abarni nasha iska*

.

================

Page 96
*
Wani soldier ne yazo wajanda suke, fuskarsa ko annuri bbu, yace kufice awannan block d'in dan yallabai zaifuto yanzu, yana fad'i yana hucii, kukan *hanna* yatsananta, mitumin da tafii kowa kusancii dashi, shine wanda ake mata iyaka dashi."
Juyawa tayi kawai tana tafiya bawai dan tasan yanda take zuwa ba."
Suma Juyawa sukayi suka bita abaya."
Sanda tafice a hotel d'in tazube agate a k'asa tana rusa kuka, kamar wanda mahaifiyarta tarasu."
Duk rarrashinda yakamata sumata sunyii amma takiyin Shiru."
Inne tariqeta tana cewa habba bodd'i dan har yanzu *hanna* bawai ta fad'a musu sunanta bane, kitashi azaune ak'asa, kwananki biyu da haihuwa, hakan zai iya zama miki illah."
Kuka takara kecewa dashi tace, barni kawai nayi kuka, rayuwata gabaki d'aya bbu haske cikinta, da irin wannan rayuwar gwara na mutu ma."
Hussentu ne tamatso kusada ita tace, haba bodd'i wannan wace irin maganace?"
Kisan cewa kowani d'an adam da nasa jarabawar, kidubeni ki gani, aranarda aka d'aura aurena aranar mijina yarasu, sannan matar yaya i'shaq wajan haihuwa tarasu, mahaifinmu yau shekara, ishirin da biyu da b'acewarsa amma haryanzu bamu ta6a jin labarinsa ba." ki godewa Allah daya kasance kindawo cikin hankalinki, zaki iya fad'a mana k'asarku, kokuma garinku mu kaiki, idan kuma bazaki je ba, Wallhy zamu riqeki har iya k'arshen rayuwarmu."
Girgiza kai *hanna* tayi tace, mahaifana suna raye bansan wani hali suke ciki ba." shikansa wannan da nazo wajansa mij,,,,,,, ai bata k'arasawa ba motocin marshall suka fara futowa, kallo tabi motocin idanuwanta nazubda kwallah, kallon motarda marshall yake kawai takeyi."
Bak'in glass ne kawai, yarufe ko'ina, sanda motar ta6a cewa ganinta kafin ta kawarda ido, tak'ara fashewa da kuka, ba tafiyarsa bace tasakata, kuka A'a sai tunowa datayi dole yanzu su biyu ne awajansa."
Koda takoma ikonta yadawo kad'an awajansa, share hawaayenta tayi, tatashi tamiqe, tana tafiya wanda ita kanta batasan ina zataje ba."

Marshall wanda gabansa yayi wata mummunar fad'uwa a lokacin da akazo dabb gate d'in hotel d'in kuma haryanzu bawai gabansa yabar bugawa dasauri bane."
Wani tunanine yasa yace kai tsayarda motannan, afili kuma yace, nasan a mutum d'aya kacal nakeda wannan feellings d'in, buga goshinsa yayi yace kuma idanna ji, aiyakamata natsaya naduba. Shikad'ai yaci gabada magana kamar zaccauce," kallon d'an driver d'in yayi yace, kajuya zuwaga hotel d'in da muka baro." waya yayi yasanarda sauran motocin."
Juyawa sukayi, itakuwa *hanna* tana ta tafiya akan titin, hussentu nabinta abaya itada i'shaq, yayinda jaririn yake cikin mota shida diddi, dakuma inne, sadik najan motan ahankali yana binsu abaya."
Sunzo dabb da ita, *hanna* kuwa hankakinta baya jikinta balle taga dawowarsu, fad'uwar gabanda yajine yasashi cewa tsaida motan, hange yafaryi ta cikin glass ya hango wata yarinya tana tafiya tad'an wuce motocin da d'ayan tsallaken titin, jikinta tafiyarta sakk na *hanna* tsayawa tayi tariqe cikinta dake ciwo, dasauri hussentu da i'shaq suka k'araso wajanta, su inne dake mota ma suka fito suka nufeta, inne ce tafara magana, bodd'i kiyiwa giraman Allah kizo mutafii amota, jikinki bbu k'arfii."
Tsallaka titin marshall yayi yanufii wajan dan tabbatarwa idanuwansa cewa itace." tsayawa yayi akanta kawai hawaye yanabin idanuwansa, jikin *hanna* yabata ana tsaye akanta ana kallonta, gashi kamshin datafii so duk duniya ya mamaye wajan."
Hawaye tajii a idanuwanta wanda ita kanta batasan na mainene ba."
Bata d'agoba cikin muryar kuka tace, maiyasa kadawo?" kallonta sukayi duka suna tunanin kwakwalwarta, tak'ara samun matsala," Marshall bai iya Bata amsaba sai cewa kawai yayi, ya Allah idan mafarki nakeyi ka dawwamar mun da wannan mafarki har iya k'arshen rayuwata, sai alokacin suka d'aga ido suka dubeshi, kallon tsoro suka masa, wanda su atunaninsu balarabe ne, amma kuma ga hausa rad'al abakin sa."
*Hanna* na kuka tace nikam zanfii buk'atar mafarkinne amma kuma nafarka yanzu."
Honey please kafad'amun abunda kunnena yajii k'aryane, please kafad'amun bakayi aureba." Marshall yarasa mai zaice, ganin yayi Shiru yatabbatar mata da gaskene, wani kuka mai cin raii *hanna* keyi, tace mai yasa bazaka iya jiranaba?" alokacin su inne sun fahimci cewa mijinta ne, juyawa marshall yayi yadubii, soldier dinda wayarsa ke riqe ahannun sa yace, ban phone d'ina jiki yana 6ari yaciro yabashi."
Number d'in intisar yayi dialing tana d'auka yasaka a handsfree, itakuwa intisar farincikine yasaka tadauka dawuri, tattaro kawayenta tana cewa, bebs habibiy yakirani, ku matso kusa, itama tasaka a handsfree, duka k'awayenta suka matso danjin mai zaice, itakuma tayi hakanne, dan d'aga ajii, k'arya tayiwa k'awayenta akan aikine yahanshi halartan bikin, koda suka nuna cewa aibaya kiranta saita nuna musu, yana jejii ne Wajen aikii."
Shiyasa yanzu ta gayyataosu."
Da wata irin murya tayi sallama wanda yasa marshall murmushi, tace sannu da aikii, mijina, yawwa ya amsa, yagajiyar biki, sanda tayi wani farr tace, ai gajiya tanan, saika dawo zamu sauketa tare, maganar Sanda tayiwa marshall banbarakwai, yana godiya ga Allah dayabashi *hanna* mace mai kunya."
Chapter 79 · 0% Book details