← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 87

Sashe 7

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Hanna* dan Allah mubar Wanda magana Dan fitowarta kamar rasa rayukanmu ne mu binneta kinji daga Mata Kai kawai tayi ammaa tasamu kanta da addu'ar Allah yasa kar suyi nasara akansa

To be continued

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

_Asmy_ _b_ _Aliyu_
Nagode da addu'arki ki gareni Allah yabar zumunci

Page 13

*

Haka kawai ta tsinci kanta da masa addu'ar kariya daga sharrin su

Haka amira tayita kwantar Mata da hankali Dan tasan Abu kadan ke dagawa kawar tata hankali gata dasa damuwa,,,,,,,, bata barta ba sanda taga tadan sake!!!!!! ,,,,,,,
Ni wallahi amira abinda yadaga mun hankali Sai kace abinda yake faruwa a film bantaba dauka yana faruwa a zahiri ba,,,,,,,,
Yanzu deh mubar wannan maganan barin duba mana abinda zamuci Fita tayi zuwa kitchen Dan dafa musu indomie Dan shi yafi komai sauki,,,,,,,,

================

Ina labarin najeeb ne??????

Yana katse wayan ya nufi falo a guje Dan fadawa mahaifinsu yaje nema masa aure,,,,,,,,,
Turus yayi tundaga bakin kofan falon zumudi yasa gabaki daya ya manta da babansu yayi tafiya,,,,,,

Murmushi yayi tareda sosa keyarsa yajuya Amma ya kudirta duk randa akace dad yadawo maganar da zaifara masa kenan,,,,

Haka yashare sukayi tacin soyayya awaya shida sweety dinsa duk da rashin ganinta yana damunsa Amma,,,,, yakudurta gobe saiya sata a idanunsa,,,,,,,,,

Babban abinda ke damunsa dukda a'ido tana nuna masa tana sansa Amma abaki bata taba furta masa ba
Ya alakanta Hakan da kunyan da take dashi

Duk bata kasance bafula tana ba,,,,,
amma tanada matukar kunya,,,,,,,,,,,,,, ita cikakkiyar bahaushiya ce Wanda kana kallonta zakaga cikar zatinta na hausawa,,,,,,,
Da asalin kyawu irinna hausawa ya bayyana ajikinta

================

Wayan da take gefen sane ta dauki ruri!!!!,,,,, Koda ba'a fada ba yasan wayan da ke kiransa,,,
Wani irin faduwar gaba ne yake damunsa kuma yarasa dalili,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Hakanne yasa kallon yanayinsa captain Ahmad yafita daga office din zaiba shi privacy,,,,,
Dan MG Idan yana cikin wani yanayi baya bukatar kowa kusa sanin halinsa ne yasa Idan suna tare dashi suka ganshi a wannan yanayi suke bashi waje shi kadai??????

Captain Ahmad yazo Fita ya umurceshi da ya ajiye masa phone dinsa guda biyu,,
Da Wanda mahaifinsa ke samunsa da kuma Wanda yake talakawa masu complain suke samun sa,,,,,,,,
Sai akayi rashin sa'a dake phones din iri daya ne ya'ajiye Wanda manyan mutane suke nemansa,,,,
Ringing din da wayarsa keyi ne ya tabbatar masa da ba phone din dayace a ajiye aka ajiye bah,,,,,

Tsaki yaja sanda wayan tayi rurin ta tagaji bai dauka ba,,,,,,,,,
Sai da aka sake kirane sannan cikin nutsuwa yadauki phone din tare da picking din call din
Dan kiran daga mr presdent na Nigeria ne,,,,,,
Gaisawa sukayi cikin mutun tawa sannan yake fada masa sunada meeting da zasuyi a Dubai a burj al_arab kuma suna gayyatarsa tareda bukatan matakan tsoro

Haka kawae ya tsinci kansa da rashin son zuwa wajen Amma zaije kodan kare lafiyar al'umma

================

Sai karfe uku sannan amira takira driver yakaisu taraka *_hanna_* gida
Suka fito sannan sukayiwa Ammin su amira sallama har kofar gida suka kaita,, sannan suka juya

Bayan shigar ta gida tayita kokari ta danne damuwarta, dan ko mama bata fahimta ba
Tun karfe tara najeeb yakira ta Dan hatta mance da abunda yafaru da rana hira sukasha sosai daga nan Sai kusan 10:30 sukayi sallama Dan anty hajja ta hanata wayan dare sosae.

Wayanta tasauka tahau bincike a iya bincikenta bata samu wata masaniya akan wannan mutumin da akeson kashewa ba,,, Haka bacci yadauketa da taradda din wayannan mutane

Baccine mai cike da mafarkai kala kala,,,,
Akarshe ne tayi mafarkin wannan mutumi wanda awancen lokacin tayi mafarki ya harbi najeeb,,,,
Ya gurfana agabanta yana kuka amma takasa jin abinda yake fada
Ahaka tafarka cikin tsoro Amma hankalinta baikai na wancen karan tashi ba waigawa gefe tayi taga anty hajja nata sharar bacci itada yaranta Mata biyu Aisha (mammii) mai sunan mama Sai halima Wanda taci sunan yayar babanta
Sauka tayi tanufi toilet tadauro al'wala salla taringa yi tana neman zabin Allah saikusan uku bacci yadauketa akan sallayan

Kiran sallan farko ne yatasheta tatashi takara dauro al'wala taga batar da sallah
Sannan tatashi anty Dan itama ta gabatar da nata sallan,,,,,,, koma wa tayi ta kwanta nan da nan wani bacci mai dadin gaske yayi awon gaba da ita

Kamar a afarki taringa jin muryarsa a cikin bacci komadda idanuwanta takarayi tarufe can kaman Wanda tatuno wani tayi saurin mikewa tayi cikin falo aguje tana ihu,,,,,

To be continued

_Ur's_
_Z33yyb3rw3r_

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

Page 14

*

Falo tayi da gudu, tana zuwa kuma tatsaya da mamaki dauke a fuskar ta,,,,,,,,,
Juyowa sukayi suka kalketa,,,,,,,,
Aikaman jira takeyi takarasa dagudu ta rungumeta,,,,
Cikin farinciki itama ta rungumeta,,,,,,,,
Muryar sane ta daki dodon kunnu wansu,,,
Oh ni tunda ba'a murnar ganina Sai in koma saurin saketa tayi ta riko hannunsa,,,,,,,
Yaya ba haka bane fah,,,, rausayar da kansa yayi!!!!!!!!
Toh meye Idan ba haka bah!!!!!!!
Kankantar da murya tayi,,,, yaya please OK ya wuce,,,,,,
Saurin sakinsa tayi tunowa da tayi bafah muharraminta bane,,,,,,!!!!!
Ankuma yafada acikin zuciyar sa,,,,,,,,,,,
Zama sukayi nan tadi ya barke tsakanin yan uwan da suka dade basuga juna bah,,,,,,,
Hira sukeyi sosai har ma ta manta tanada lecture's
Can wayan ta ta dauki ruri,,,,,,
Tana kallan mai kiran saida gabanta ya fadi,,,,,,
Alokacin ta tuno tanada lecture's
Saurin daukan wayan tayi,,,,,,,,,,,
Beb wai me kikeyi a gida ne tun 9 fa muka shiga lecture's kuma zuwa 12 zaiyi test ai batasan lokacin da taduro akan kujera ba,,,,,,
Daki tawuce tashiga wanka batafi 15minute ba tafuto,,,,,,
Shiryawa tayi cikin blue da red din atampha,,,,,
Bakaramin kyau tayi ba sannan ta dauko ribbom tayi parking kanta,,,, duk da gashin kanta bai cika tsayi ba Amma Idan tayi kitso yakankai kafadunta, cikan da kanta ke dashi ne yakan hana kallan tsayinsa sosai,,,,,,
Cikar da gashin ke dashi ne yasa da tayi parking yataso kamar Wanda tasa ribbom na acuci,,,,,,,,,,,,,
Dankwali tadaura sannan tadauko khimar dinta dogo sosai ta daura,,,
Sannan tafesa turare mai sanyin kamshi wanda saika matsa kusa da ita kafin kaji kamshin,,,,,,,,,
Takal minta ta dauko plat dake tanada Dan tsayi yasa tayi dass dass gwanin sha'awa,,,,,,,

Futowa tayi dauke da side back dinta mai tsadan ba jebbu ba,,,,,,,
Dan mama da yayunta na kokari wajen sayamata kayayyaki masu tsada,,,,,
Tsugunawa tayi tasauko phone dinta da tabari akan kujera,,,,,,
Juyawa tayi ta kalli kujeran da hameedah ke zaune,,,,, subhanallah wani irin kama naga sunayi da wannan yarinyar wanda bazasu wuce sa'anni ba Sai tsiran da bazaifi na months ba,,,,,

Tabbas suna kama saidai bambamcin da baza'a rasa ba,,,,,,,,,
6s muje koh,,,,,,
Muje inahh???? Skull mana kinsan ai tunda kinzo toh tare zamu,,,,,, Dan bawani uzurirrikan da zandauka,,,,,
Tashi tayi suka dugun zuma kitchen dan yiwa mama Sallama,,,,,, me nake gani badai wani wajen daku je ba,,,,
*_Hanna_* tayi saurin karfe zancen,,,,,,
Ehh mama school zamuje,,,!!!! Amma ai kyabarta tahuta yanxu fa isowarsu daga kano,,,,,
Ko ruwa batshaba balle wani abinci,,,,,
Zamuci a makaranta tafada tareda jan hannun hameedah,,!!!!!!

Saikusan 11 suka isa makarantar,,,,,
kiran amira tayi sukaje yanda take suka sameta,,,,,
Gaskiya Beb kuna kama da 6s dinki sosai,,,,
Harya wuce yanda kike fada,,,, saidai tafiki kyau tafada tareda kashe Mata idoh daya dukan wasa *hanna* takai Mata kinfiye sa idoh kekam kinji jiki,,,,,,
Kyaleta kawai dannasan tafada ne kawai kowa yace kinfini kyau
Dan idanuwanki yafi nawa girma kuma kinfini dogon hanci
Cewar hameedah!!!!!!!
Dariya sukasa kede kawai kin tsorata da wayan nan idanuwan tanne amma bawani kyawun da ta fiki,,,,,

Beb bamu karya bafa,,,, lallai bakida hankali kikabar bakuwa da yunwa harara ta galla Mata wacece bakuwar,,,,,,,
Ninaga alama in muka biyeki Sai munrasa test dinnan,,,,,
Uhm kawai amira tace sannan suka nufi hanyan _barhakkk_ dake gefen hostels na school din danyin breakfast,,,

Sanda sukeyi ordering kafin suka zaune tadi sukeyi wanda zaka rantse amira sundade da sanin juna da hameedah!!!!!!!!!! Dan duk su ukun bbu baya wajen surutu!!!!!!
Wayan *hanna* ce tadauki ruri jin kidan yasa tasan wa yake kira Dan ringing dinsa dabanne,,,,,
Daukan wayan tayi,,,, sannan tajuya gefe da gefe aikuwa caraff idanuwanta ya sauka akansu,,,,,,,,,,,
Saurin juyawa tayi sannan takara wayar a kunnenta,,,,
Hellow°°°°sweety
Na'am kina school ne????? Eh!!!!! Ina zuwa yanxu kijirani
Haka kawai ta tsinci kanta da faduwar gaba!!!!!! No plx karkazo,,,,, karnazo???? Dalili?????
Shiru tayi tafara kame kame '' ''''''''hmm dama nasani baki da wani abinda zakice nadade da fahimtar bakya sona nikadai nake hauka akanki,,,,,,,,
Tabbas kina shirin jefani wani hali Dan har ikika gujeni mutuwa zanyi plz karki barni nizan koya Miki yanda zaki soni Amma plx karki rabu dani yafada cikin sarkewar murya,,,,,,

Wani irin tausayinsa da sansa ne suka kara ninkuwa cikin zuciyar ta!!!!!
Mekaki fadi haka kasan Nima bazan iya rabuwa dakai ba
To meyasa bakyason muhadu????? Kijirani agidan anty Idan nafito a lecture's zanzo,,,,,,, OK bye luv u saurin katse wayan tayi dan bazata iya bashi amsa ba,,, tadaga wayan akunnenta tana murmushi,,,,,

Zuba Mata idoh sukayi kaman wanda tayi wani abun,,,,, meye hakan da'allah kun wani tsareni da idoh kaman tsoffin mayu,,,,, ko gizau basuyi ba sukaci gaba da kallanta hameedah harda karawa da tagumi,,,,,,,,
Amma cikin ranta wani dadi takeji na ganin yar uwarta tasamu masoyi,,,,,,,,,,,,,,,,,
Tsaki taja sannan taci gaba dacin abincinta,,,,,,,,

Waye shii?? Cewar hameedah najeeb tabata amsa atakaice yatsine fuska amira tayi "" ""sannan tace zaiyi yabari afusace da dago bangane me kike nufii ba cikin bacin rai!!!!!!!!!!

To be continued

Ur's
z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writting by
© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

This page is Dedicated to u___anty rash wish u success in your exams

Page 15

*

Ni na tabbata akwae wanda yarigashi kuma haka kawai zaizo yayiwa wani wucel aiba haka akeyiba
Cikin bacin rai *hanna* tace toh saiki mutu Amma aure kam na auri najeeb angama saikuje kuyita haukanku keda su
Tajuya gun waynnan mutanen ta maka musu harara,,,,,
Jan jakarta tayi tana shirin barin wajen
Saurin riketa hameedah tayi sannan takalli amira ku fahimtar dani mana har yanzu bawai nagane yanda kuka dosa bane
Chapter 7 · 0% Book details