← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 87

Sashe 32

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*
Tun sassafe aka fara shirin zuwa nemo aure, "
Alokacin aka kira baba aka sanar dashi zuwan,
Aikuwa yaje yasamu Abba ya fad'a masa."
Abba ne yace amma yaya gani nayi kamar yayi wuri dasun bari nan da zuwa koda satii ne sai, "
Suzosu kaga yanzu bawani shiri mukayi ba."
Babane yace nima abinda nagani kenan, amma idan mukace wani abu zasuga kamar basan abun mukayi ba. "
Kuma ni maganganunda yarinyar nan ta fad'a ranar auren samha sai ina kallo kamar akwai wani abuu ak'asa,"
Kaga kuwa yakamata mu amince musu ayi wannan zancen da wuri kamar yanda suka bukata."
D'an gwauron numfashi Abba yaja sannan yace nima nayi tunanin hakan dan inaga akwai masu yiwa yarinyar nan ba dai-dai ba tunda dakanta tace aidama tasan bazasu barta ba, "
Acika mata burinta kamar yanda ta bukata abarta tazauna haka,"
Ai yaya kanajin wannan magana zakasan da wani abuu ak'asa, "
Kuma ta iya yiwuwa yanzu haka ita yarinyar tajii da kunnenta ne yasa ta fad'ar haka."
Dan ni gaskiya yaya bazan 6oyeba gidankanna bakowa nayarda dashi ba kawai abun yafi yanzu mudage da addu'a sannan kuma musa ayita mana saukar qur'ani, "
Kasan mutum kai baka damu dashi ba amma kai yadamu da rayuwarka."
Baba ne ya nisa sannan yace toh Allah yataimaka sai musan abinyi dan nasan zuwa jimawa zasu iso. "
Shiga Cikin gida sukayi,"
Suka samu mama da umma kud'in aikin da za'ayi na Cikin gida aka basu sannan su Abba suka wuce dan tanadarwa bak'i snacks da kuma drinks, "
Saleem ne ke fitowa daga dakiin su, Alokacin abokinsa yakirashi dan tun jiya sai samun kira yakeyi,"
Wa'yanda da ba frndz nasa bane, wanda then suna kallo mahaifinsa baida kud'in da zasuyi abota dashi yanzu haka sai kiransa sukeyi,"
Sunaso su jonehh. "
D'aukan wayan yayi cikin gadara."
Daga can Cikin wayan nayi ance palz yadai naji wani labari wai dagaske ne? "
D'an gyarawa yayi yafara koro Bayani yanayi yana wani gadara,"
Aikuwa duk abinda yake fad'a a kunnen Ammah datake zaune abakin kofa,"
Rikicewa tayi wai metake jine waishin dagaske *hanna* aure zatayi?" kuma dan gidan sarkin kano zata aura?"
kamar yanda tajii Saleem yadad'a, "
Afili tace kai ina haka bamai yiwuwa bane."
Shikuwa Saleem baimasan tanayi ba."
Can garin kano kuwa MG harya gajii da amsa call, dan governor's minister's ambasador's da president, "
Na k'asa she daban daban sai kiransa sukayi suna mai murna dan abu kamar wasa yabaza duniya sosai,"
Dayawa mutane ke sharing wannan video d'in. "
Aranar kuwa followe'r kamar zasu cinye, amira da hameeda."
Kai har takaiga radio's station, "
Tv chennel's,"
Bana k'asarnan zallah ba har na k'asa she da yawa."
Zance gabki d'aya ya karad'e duniya. "
Kowani tasha kika bud'e labaran kenan." MG daya gajine da recieving call, kawai sai ya yanke call saidai massag gashi har yanzu yan wshing basu barshi ya d'an samu tym yakira *hanna* ba. "
K'anin mai martaba ne zaune a falon mai martaba,"
Magana yake yi, yana cewa, "
Yaya aduba wannan lamari gaskiya baida ce ace ya auri yar gidan talaka ba."
Mahaifin yarinyar fa malamin makaranta ne,"
Kaduba matsayi da dukiya irinna yareema ga mulki, arasa wacce za'a aura masa sai yar gidan malamin makaranta yanzu yaya maiyaci yabawa iyalinsa har za'a gani ayi sha'awar aure? "
Ran mai martaba in yayi dubu yab'aci, dan irin maganganun da k'aninsa yake fad'i ya6ata masa rai,"
Amma dayake dattijo ne mai hakuri yasashi sharewa yabarshi yaci yacigaba da cewa ai wannan yakamata yayi tunda munada 'ya'ya mata sai qhad'ashi da d'aya aciki, "
Mai martaba ne ya nisa sannan yace,"
Mai dukiya dakuma talaka duk Allah ne yayisu, "
Kuma inaso kasani koda yar bukka yareema yakawo yace yanaso toh ita zan aura masa."
Balle mahaifin yarinyar yanada rufiin asirinsa duk abinda ake nema wajen aure to wannan yarinya da mahaifanta suna dashi addu'a yakamata muyi Allah yasanya alkhairii acikinsa. "
Duk da bahaka yasoba amma jikinsa yayi sanyi." Ammah bata tsaya ko inaba sai gidan kawar ta aminiyarta,"
Hajiya lamii tana zuwa tafara mata birgima tana cewa wallhy malam yacuceni duk kud'in da nake she ace baimin aiki mai kyauba, "
Shege dan iska halama boka ne," 😳nikuwa nace kajimin amman nan dama ke atunaniki wajan malami kike zuwa toka kin yaudarii kankii. "
Dan wannan ba malamii bane."
Hajiya lamii ne tayita rarrshinta sannan tace tayi hakuri su k'ara jarrava wani suganii,"
Cikin kuka Ammah tace mai nake dashi dazanje wajan wani kefa kina kallo na tattare duk kada rori na nasayar naba wannan macucin,"
Menake dashi dazan je wani waje,"
Cikin lallashi tace mata kiyi hakurii mutafii wani kauye abincika kinsan irinsu basusan zqfin kud'ii ba sai mu bincika."
Cikin d'an gamsuwa da maganar ta Ammah tayi shiru sannan tace to yanzu yaya zanyi tace kodaiyaya kisan yanda kikayi kika nemo kud'ii koda bbu yawa, "
Gaki da yara ai Had'a musu wuta zakiyi sai sun nemo miki."
Ahaka sukayi sallama Ammah tatafi bayan tagama kitsa mata makircii."

Can wajen su umma kuwa sunanan suna shiri iya dai-dai gwargwado sunyi k'okari sosai wajan tanadarwa da baki abun buk'ata. "
Alokacinne anty maman amal tace ashirya *hanna* dan tasan dangin sarauta yanzu haka da mata za'azo kuma zasu bukqcii ganinta,"
Chapter 32 · 0% Book details