← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 87

Sashe 25

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*
Juyawa tayi dan ganin wayake yimata manni ganin ya jalal yasata sakin murmushimurmushi ahankali tace," yaya ina kashiga?"
Bana ganinka, dan ta6e baki yayi, "
Banason hayaniyane yasani barin gidan,"
Sai kun gama bikinku zandawo, "
Harda saleem ko?"
*Hanna* tace eh yace mata atakaice,
Sanda yazo dai-dai kunnenta ya rad'a mata kinyi kyau d'an murmushi takarayi, yad'an kama ha6ansa🤔 ya kalleta kamar maisan gano wani abu a tattare da ita amma kinrame kad'an, mai yake damunki? "
Narai narai tayi da fuska alamun batasan tambayan,"
Ganin haka yasashi jan gyalenta ya nufii wata kujera da ita."
Alokacin ran MG inyayi dubu ya6acii har wani hucii yakeyi gashi idanuwansa sunyi jazirr. "
Jiyake kamar yaje ya shaqe jalal,"
Murmushin data masa yatsaya masa arayi gashi yawani ja mata gyalenta ita kuma tabishi. "
Runtse idanuwansa yayi kawai yana fitarda hucii mai tsafii."
Dakyar ya iya fita ya yiwa ango da amaryarsa liki, "
Yana tashi kallo yadawo kansa."
Daga nesa mutane keta d'aukansad'aukansa a photo dan wanda basubasu ta6a kallonsa bama yau sun kalleshi ba'a TV ba, balle masu pics wanda sunsan dasu samu kud'ii kowane mai photographer, burinsa ya d'aukeshi."
Dakyar yatsaya suka d'auki pics da couples d'in amma yahad'e girar sama data k'asa. "
Kusan 12 akagama diner, hanna tace ita dole gidan su zata wuce dakyar labba ta rarrasheta tayarda ta bisu shshin ummii suka nufa lokacin dare yayi sosai yasasu wucewa d'akin labba,"
Wanka suka fara yi sannan suka kwanta. "😴

Najeeb an sallameshi a asibiti jikinsa yad'anyi sauki saidai damuwace fall arayinsa danko abinci baya iyacii balle magana,"
Iya tambayoyin duniyarnan ammasa amma bbu amsa duk 'yan uwansa hankalinsu yatashi ganin halinda d'an uwansu yake. "
Koda yayansa yakira anty maman amal Bata fad'a masa tasan komai ba saidai tad'an canja muryarta bakaman yadda yasaba jiba sai yabar hakan a hidimar biki."

Washe gari da safe ko karyawa basuyiba *hanna* tasa labba dole sanda takaita gida. "
Ahaka tatashi takaita,"
Ummii na falo taga shigowar labba, "
Cikin gajiya tazube akan kujera,"
Ummii ne tace habibty daga ina haka da sassafennan? "
Wallhy ummii *hanna* ce tace saina kaita gida wai zataje tasha magani batajin dad'ii,"
Cikin nuna kulawa da damuwa ummii tace Allah yasauwake, "
Ameen ta amsa atakaice."

K'arfe uku suka fara shirin yin bud'ar kai wanda za'ayishi acikin fada. "
Saikusan 4pm kafin akagama shiryawa,"
Alokacin hanna tadade da isowa Bata wani dad'e awajenba da damu labba tatashi tarakata wajan moddibbo, "
Ba su d'auko lokaciba suka dawo dayake addu'oii kawai suka kar6o,"
Sannan suka juyo. "
Sunsamu angama kawai suka wuce gida hardasu amira," wanda gobe zasu koma, "
Labba ne tasamu ummii adaki akan sallaya ta idarda sallah."
Sannu ummii, "
Yawwa Sannu inakika shiga?"
Naraka *hanna* kun moddibbo ne, "
Murmushin tayi danko sunan *hanna* aka ambata takanji son yarinyar aranta."
Yanzu wajen mai martaba zanje naji zancen yanda suka tsaya akan zancen jiya sunje tambaya, toh tunjiya bamu samu dama munyi zancen canba shiysa yanzu zanje, "
Murmushin fuskar labba ne yafad'ad'a, Allah yasa andace amin tace."
Sannan tamike tayi shashin mai martaba afalo tasamu mai martaba. "
Cikin fara'a da girmamawa tagaidashi,"
Cikin tsolaya tace nabiyo sawu ne, dariya mai martaba yayi sannan yace ohh uwar yaro ba hakuri anaso aji yanda zance yakaya."Murmushin tayi sannan tace bakasan yanda yaronnan yake zuwa yazaunamin ba Koda bai furta ba amma nagane nufin shi. "
To ai muntsaida zance da iyayen yarinyar amma munaso yaran su dai-daita kansu yanda abun zaizo Cikin sauki."
To Allah yasanya alkairi aciki da amin ya amsa Suna Cikin zancen saiga MG yashigo da sallama amsawa sukayi sanna yasamu wajen yazauna gaidasu yayi suka amsa masa. "
Zama yayi nan mai martaba ya labarta masa yanda sukayi da mahaifan yarinyar."
Wani irin fad'uwa gabansa yayi danshi yana shakkar tunkararta baisan mai zaifaru ba. "
Murmushin ya kakalo sannan yamusu sallama da godiya yafita."
ya yanke shawarar jibi ya tunkareta dan yasan rana mai mahimmamci ne arayuwarta. "
Da safe su amira da mama suka fara shiri jitaayi duk garin bbu dad'ii daga ita har hameedan, dan da tafiyar da *hanna* za'ayi amma tafasa batason abinda zai had'ata da Najeeb kokadan kuma tasan har inde tatafi zasu iya had'uwa."
Babe yanzu jibi nefa birthday d'ina wednesday amma bazaki zauna ba? "
Srry Beb wallhy mom ce tatakura Nima banso komawaba,"
Badan ransu yasoba su kayi sallama su amira suka tafi, kuma duka bakin sun watse sai d'ai-d'aiku. "
Haka sukaji wani irii bbu amira arannan sunyi bacci sosai, wanda tunda akafara bikin basu sameshiba,"
Washegari sukaje sukayi odering duk wani abunda zasu buk'atq gobe. "

To be continued

Ur's
_Z33yb3rw3r_
[9/23, 10:28 PM] ‪+234 810 367 2210‬: *BIBIYATA AKEYI*
_
_Bismillahirahmanirrahim_

_
Writting by

© _zaynab_ _bawa_
( _z33yyb3rw3r_ )

My first novel

_This Page is sencirely dedicated to u my sweetest, cutest amazing, wonderfull, sweet heart *raheenat* u r such a damsel unique my dear, ILYSM my dear Allah yabar luv 😍 i heart u dear. "_(j'aime ```vraimene mon raheenat vous este un ami comme tout utre) jet'aime ```

Page 41

*
Sosai suke zurga-zurga dan ganin sun kammala komai kafin gobe, dan gobe da yamma sukesonyin celebrating na birthday d'in a gidan adda hindu,"
Umma takira wanda zasuyi decorating wajen, with pink and white flawer's cottons and balloons."
Sannan sunyi ordering 2 birthday cakes, pink colour mixing with white da kuma golden colour,"
Sai kuma cup cakes da sukayi ordering. "
Sosai suke tsara yanda komai zai kasance, sunje anwanke mata kai itada hameeda amma batasa relaxer ba,"
Sai sukaje shopping ananne suka sayo kayanda zasu sa. "
Abubuwa basu kammala ba sai karfe tara na dare 9pm sannan suka samu suka gama wasu abubuwan,
Sai alokacin tasamu dama takira labba ta shaida mata,
Fushi tayi bata kirata sunyi komai tareba ce mata tayi akan tayi hakuri taga ta gajii ne da hidiman biki yasa, sallama sukayi ta shaida mata gobe da safe data isoh. "
D'akin ummii ta nufa tasameta da murna ummii gobe fa birthday d'in *hanna* ,"
Cikin fara'a ummii tace To gobe saimu shiga kasuwa amata shopping na gift koh, "
Ummii muje yau mana gobe fa dasafe nakeson zuwa,"
Cikin Murmushin ta tak'ara cewa, yanzufa tara tawuce kibari gobe kinjii, "
Toh kawai ta amsa tafice Badan taso ba,"
Y'an tsirarun mutane aka fad'awa dan basaso suwuce fifteen 15 awajen, "a sunyi yawa sukai twenty 20."
Bacci suka kwanta dan sungaji likis, "
Kusan k'arfe goma taji wayanta na ringing Cikin magagin bacci taduba kawai taga numb d'in najeeb ne kasa picking tayi
Har yakatse,
Can kusan bayan 30 minute akasake kira kawai lokacinma har bacci yak'ara d'aukan, dan kiran farkonma bawai tagama fahimtar mai kiran bane, "
Tura wayan tayi k'asan pillow ba tareba ta duba ba, ahaka har aka d'auki tsawon awa biyu anayi ba'a kira sai bayan 30 minute batareda ta dubaba duka,"
Alokacin da 12 :00 taduba dai-dai lokacin massage yashigo wayan, "
Wanda bata damu ta dubaba,"
Kicin jin bacci tazare wayan tayi switching nata off. "

Najeeb na kwance ad'akinsa yaji yanason jin muryarta haka kawai wanda baisan dalili ba yayi - yayi ya daure ya kasa, shine dalilin d'aga waya ya kirata Koda ya kirata yaga ba'adauka ba yayi kusan 3 miss call ba'a picking yasashi, hakura yakashe wayan gabaki d'aya."

Gajiya ne yasasu makara har kusan k'arfe shida na asuba bbu wanda yatshi acikinsu,
*Hanna* ce ta d'an bud'e idanuwanta sannan ta mayar ta lumshe, batafi 1 minute da rufe ido ba, sai gata ruff akasa tafado, wanda hakan yasa hameeda mik'ewa zaune bbu shiri tunda taji k'arar faduwa, "
Waige-Waige hameeda tafarayi yayinda ita kuma *hanna* inahh hankalinta nakan neman wayanta da take yi, tunowa da tayi an turo mata massage bata duba ba yasata wannan fad'uwar tanada tabbacin bbu mai turo mata massage awannna lokacin kuma irin wannan rana inba shiba. "
Pillow tad'aga aikuwa saiga wayan tana bud'ewa taga massage ai Cikin ihu tace OMG itz dat numb again," massage tagani Kamar haka,"
*_HBD JAAN ITX TIME."_*
saurin komawa tayi tab'ude na wancan shekaran, " shima dai massage ne kamar haka."
*_HBD JAAN 1YEAR REMAINING. "_*
Tunanin tazaunayi mai hakan yake nufi da itx tym lokacin menene?"
Ita tasan dai shekaran ta biyar da wannan numb tafara mata massage tun ana 5yrs remain har yadawo itx time to lokacin mene ake irga mata. "
Iya kira tayi kira amma batsamu mai numb d'inba,"
Har campany na layin MTN taje dan tayi bincike anshaida mata cewa layin sai bayan shekara, shekara ake amfanii dashi kuma shi layin ba'a teracging kuma lokacin da aka fad'a mata ana bud'ewa shine lokacin birthday d'inta. "
Zama tayi abakin gado tayi tagumii kawai can kuwa sai maganar captain bala tafad'o mata,"
```Karki damu kin kusan sanin dalilin dayasa muke *bibiyarki* lokacin k'alilanne yarage wanda zai amsa miki tamabyoyinki yananan zuwa```
Tunani ne fall ranta kamar tayi tagumii kamar wanda aka tsikareta ta tashi aguje tayi hanyar waje, "
Hameeda da take kollonta tun lokacin da take neme neme itama tafita aguje tabita,"
Bata tsaya ba sanda tazo gate sannan ta tsaya alokacin Hameeda ta iso, *hanna* ina zaki futa? "
Sleeping wears nefa ajikinki."
Bata saurareta ba tabud'e kofar da yake jikin gate d'in, "
Tasakai ta fita, gashi lokacin garii bai wayeba, kodaga sallah ba'adawo ba." To her biggest suprise tana bud'e kofan tacii karo ta qatoton gift a ajiye akofan. "
D'auka kawai tayi ta tsaya duba gefe da gefe bataga kowaba, hakan yasa tajuya, zuwa ciki Hameeda ma tajuya tabita."

Suna shiga daki ta ajiye akan gado tayi toilet danyin alwala, tana Fitowa ta samu Hameeda na jiranta, tsareta tayi ta tambayan *hanna* waye ya ajiye wannan k'aton gift d'in awaje? "
Murmushi tayi Nima bansaniba abinda nasani kawai duk shekaranda zanyi birthday sai an ajiyemun gift da asubahi a kofar gidanda nake."
Tana fad'in haka tajuya tad'auki sallaya da khimar ta fara sallah. " MG baibar kofar gidanba sanda yaga tafito ta d'auki gift d'in tukunna yatada mota yawuce,"
Chapter 25 · 0% Book details