← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 87

Sashe 84

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Plz cutie kibar kukannan haka kukanki ya isheni da jii bansan sake ganin hawayenki, hava-hava, murmushi tayi sannnan tace nadaina, yawwa cutie toh bashi abincii, bbu musu tafara shayarda yaron, har sanda ya koshi, haka sukayita zama wajen su kansu basusan lokacii yatafii ba dare yatsala sosai, kallonsa tayi sannan tace honey darefa yayi sosai, ah havadai yaushe kika futoma cewar marshall miqewa tayi tana cewa, nikam miqominshi mutafii, A'a dare yayi muwuce shashinmu kawai, nikam bazanjeba tabshi amsa, yanzuma dai nikam bansan da wani ido zan shiga ciki ba, dariya yayi sosai yace da idonki mana cutie, konawa kikeso nabaki aro?" aida zaifiikam danna gansu asoye tafad'a tana kokarin karbe yaron, riqeta yayi yana kokarin kissng dinta yana cewa barina gwada miki yadda suke asoye, samu tayi takar6e yaron, tana masa dariya, tashige shashin ummii, shafa sumar kansa yayi yanajin wani nishadi, ya dad'e kafin ya samu yatashi yanufii shshinsa."

Koda tashiga tasamu wasu daga cikinsu basuyi bacci ba, dan sunajiran kallon yaron kamar muna fuka ta miqashi awajen ummii bbu wanda yauna yasan tana sunne sunnenta ma, ganin hankalinsu yayi kan yaronne yasa tashige tayi kwanciyarta."

Washe garii da safe misalin karfe sha d'aya 11 kowa ya hallara a falon mai martaba, hadda momy wacce sassafe ta iso, mai martaba ya nuna farin cikinsa sosai naa ganin *hanna* kowa ya hallara kilishi da intisar ne kawai basanan, mai martaba ya aika akirasu, amma shiru jakadiyane, tashigo tadurkusa gaban mai martaba sannan tace, ranka shi dad'e, mai kulada shashin ta sanardani tun sassafe suka fice haryanzu basu dawo ba, daga nata kai kawai yayai tatashi tafice cikin ransa yanajin zafin yanda tafita batareda ta tambayeshi ba, amma bai nuna ba, ahaka akayi zama sosai aka nunawa marshall laipinsa, su inne kuwa sunsha godiya yayinda mai martaba buk'acesu akan su zauna sai bayan suna su tafii, basuyi musu ba, dan su kansu suna bukatar hakan."

Alokacinda affan yasamu labarin abunda marshall yayiwa intisar har cikin ransa bayai yaji dad'ii ba."
Ransa yabaci sosai kuma yasan umma(kilishine) tajawo mata, bai sake tsinkewaba da tausayinta ba saida yaga yadda intisar tarema lokacii d'aya tausayinta yakamashi, aikuwa dabad'an dan uwansa vane yayi mata wannan wulakancii da'anga yadda zasu kwashe, wasu kuma daga cikinr y'ay'an kilshi cewa sukai aidama namiji ba'ayimasa auran dole, Allah yasa hakanne yafii mata saukii agareta,

Kilishine gaban bokanta tana zaune dirshan daka ganta kasan magan ganun dayake fad'a mata ranta baiyi mata dad'i dasuba."

To be continued

Ur's
zaynab bawa

[25/10, 01:50] Zaynab M Bawa Fbk: *BIBIYATA AKEYI*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Writing by
*©zaynab bawa*
*(Z33iiyyb3rw3r)*

_Like my page on Facebook=zaynab BAWA novels_

_Join my group on Facebook= ZAYNAB BAWA NOVEL'S_

_Your fifth page, is here my *HAJJA CE* Allah yabarminke har abada, ke abun alfaharice ga al'umma."_
_Allah yaraya mana ihsan musha biki."_

====================

Tabbas ke k'awar arziki ce *ASMY B ALIYU* godiya da mai yawa ga dumbin soyyayarki gareni Allah yabar zumunci."

*
page 99

Bayan sunbar shashin mai martaba, kusan gabaki d'aya shashin ummii aka nufa, alokacin harsu yaya hindu duk sunzo, murna dai ranar acikin wannnan dangii ba'acewa komai, hanna ne zaune da su anty afeeya, dakuma sauran yayaunta, kallon anty afeeya tayi sannan tace nifa bqnga labba ba, dafqrko nadauka tana gidaki kuma naga haryanzu bata iso ba, murmushi anty tayi sannan tace labba kam tana nan tana tayqki kishi tama tattare kayanta gabaki daya takaoma wajen dangin ummii, tun jiya nake kiranta taki dauka tunani takeyi dan fad'a mata zancen and'aura aurenne ne, anty *hanna* labba tashiga tashin hankali, kowa yashiga tashin hankalin rashinki, yaya hindu ce ta kar6e maganar da cewa *hanna* ki gode Allah kina tare da masu k'aunarki dayawa, hakan yakasance abun dubawa dukda bazai kasance kowa yasoka ba arayuwa, idan kaga mai k'iinka saika tuna da dumbin masoyanka, mungode Allah daya dawo mana dake cikin koshin lpy, wannan kad'ai ya ishemu farinciki, kuka *hanna* tafara tana cewa kuyafeni en uwana, bason raina bane na 6ace nabarku cikin tashin hankali, nima nayi missing dinku sosai fiyeda yadda baki zai iyq furtwa, nayi missing dinku fiyeda yadda hankali zai d'auka, fiyeda tunanin yadda tunani zai dauka, inasonku sosai, inasonku tafad'a had'eda share hawayen fuskarta." kar6an wayar hameeda tayi sannan Tad'auki number din labba awayqr afeeya, dialing tayi, harta kusan katsewa ba'a daukaba,"
Labba dake kwance kan gado hankalinta duk yana gida amma batason komawa ne dan bataso takoma tajii and'aura quran yaya yareema ta intisar, intisar er uwartace bawai batason auran bane dan batason intisar ba, a'a saidan ganin rashin dacewar hakan, hakan yakasance butulci da'ace *hanna* tana nan yaya yareema zaiyi aure abun bazaiyi mata ciwo ba, kamar yadda ace batanan ta 6ace, yanzu wayanasan ma, kodan yaya yareeman akayi mata wannan abun ta6ace, yanzu rana d'aya ace *hanna* tadawo tasamu wannan labari wani irin hali zata shiga?"
D'an tsaki taja yayinda wayarta ta dameta da ringing kamar bazata d'aukaba harya kusan tsinkewa tak'arajan tsaki akaro nabiyu sannan tayi picking, shiru tayi batace komaiba, daga d'aya bangaren kuma *hanna* dataji and'auka, dasaurii ta ambacii *habibtiii* aikuwa labba ko bacci tatashi dashi bazata mance wannan murya ba, Batason lokacin da tafad'o daga kan gado ba, ita tayi gefe wayar tayi gefe, k'arar fad'uwar wayanne yacikawa *hanna* kunne yasa tayi saurin d'agawa daga kunnenta tana kallon wayar, sauri labba tayi ta nemo wayar, hango waya tayi agefe, daukan wayar tayi sa'arta d'aya wayar bata mutu ba, saurin karawa tayi akunnenta tana cewa, habibty habibty, dai-dai lokacin *hanna* tamayar da wayar akunnenta, na'am *hanna* ta amsa had'eda farfara ido kamar tana kallonta, jiki na 6ari labba tace sis ta gaske kece, gashi kuwa kinjin hanna tabata amsa atakaice, sannan tad'aura dacewa saura 4days suna yqronki, kiyi kizo idan ba haka ba baby yayi fushi dake, zqtayi magana *hanna* tayi saurin katse wayar ta kasheta gabaki d'aya, dariya afeeya tasaka sannnan tace aikuwa kin iya maganainta, yanzu zata fara shiri sannnan tatashi hankakli anem mata visa, aikuwa baku kyauta mataba, cewar yaya hindu yanzu haka zakusa hankalinta yatashi, dariya kawai *hanna* sukayi."

Palour suka koma waJen mama momy dakuma ummiii da inne da kakarsu, ita kuma hussentu tana taredasu *hanna* da yarinyar isshaq, sukuma Sadiq da isshaq suna masaukinsu, basu dad'e da zama afaon fa marshall yashigo d'aukeda sallama, mafii yawanci d'akinne suka amsa, sannan yakarasa shigowa kayan sodier's ne ajikinsa yayi masifar kyau, fuskarsa d'aukeda murmushi, da annurii, tsugunnawa yayi yagaida manyan dake wajen sannan yadubi mama yace," mama akwai wayanda zasuzo daga bauchii ne? Eh akwai tabashi amsa atakaice, sannan tadaura da cewa inaga kaman Aisha da rabi'atuh da ammansu zasuzo nikuma zankoma saboda su karima akwai hassana da husaaaina d'azu karima takirani sunata kuka, babuk'atqr komwarki marsall yafad'a sannan yad'aura da cewa inaso na aika soldier's yau za'a taho dasu, sannan masu zuwan su jira soldoer's su isa sannan su taho tare sabilida hatsarin dake cikin tafiyarsu su kad'aii," jirgi zasu tafii dan haka ba wani jimawa zasuyiba." d'aga kaii kawai mama tayi jikinta duk yabi yayi sanyi tasan lokacin rabata da yaran dasuka riga sukabi jinin jikinta yazo, ahanakali ta furta Allah yayi taimako yabaku sa'a abdallah kakula sosai kasan hatsari irin na way'annan mutanen." squran dake d'akinma addu'ar suka yi masa, juyawa yayi zai fita *Hanna* Wanda tun shigowarsa idanuwanta yake kansa sakamakon wani irin kyau da yayi, har zuwa lokacinda yayi gaisuwa idanuwanta yana kansa, alokacin da yafara magana kansu karima ne tunaninta yafara canjawa abubuwa dayawa sukayita dawo mata way'anda suka faru abaya." kukanda *hanna* tasakane yasashi juyowa tsayawa yayi kawai yana kallonta, maamakine yakamashi menene kuma nakukan?" ohow, yabawq kansa amsa, *hanna* akan gwuiwowinta, ta tsugunna agaban ummii tana kukaa tana cewa ummii dan Allah kihanashi zuwa wallhy akwai abunda zai faruu, marshall ne yace shhhhhhhhhhhh *hanna* bbu abunda zai faru, akwai tafad'a kayi shiru kawai kai baka sani ba, kabarsu da Allansu kawai plz karkje wani abuu yafaru dakai way'ananna mutane hatsabiban mutane ne."
Tsayawa kallonta yayi kawai dan baisan mai takeson cewa ba, sqka bayan hannunta tayi ta share hawayen fuskarta, taja majinar dake hancinta sannan tace ummiii sune way'anta suka sa aka harbeshi adubai gaban ummii ne yafadi daran tace hanna me kike shirin cewa ne??, hard'e hannayensa a k'irji marshall yayi, a iya saninsa yasan bai ta6a furtawa *hanna* cewa anharbeshi ba, sannan yasan bawai tasanda hakan bane, a hankali yafurta tayaaya akayi kikasan hakan *hanna*, nan da nan tashiga basu labarin abunra yafaru a highcourt lokacin zuwansu da amira wajan babanta, takara da cewa alokacin naso nasanar dakai toh idan zanyi hakan bansanka ba bqnkuma san a'ina zan sameka ba, amira ce ta hanani sanrada wani sabilida akwai hannun manyan mutane aciki bakasan wa zaka fad'awa ba dakuma mai hakan zai janyo Ba, labari taci gaba da basu, har izuwa lokacinda taji sanarwa a tv akan cewa an harbeshi bbu tabbacin yanada raii kokuma yamutu, dakuma mafarki da takeyi dashi, hanakalin ummiii yatashi sosai jin irin wannan labari, mama girgiza kai tayi sannan tace assha asssha *hanna* meyasq kika kasance mai zurfin ciki haka?" ni mahqifiyarki ace munkwana daki daya muntashi d'aki daya kikasa fad'amun wannan?" kuka kawai *hanna* takeyi takaea cewa komai, marshall wanda kukan *hanna* yafii d'aga masa hankali fiyeda maganganun da tafad'a masa yace shhhh *hanna* taso kizo nan, bbu musu tatashi tanufeshi, kama hannunta yayi suka fice waje sukabar mutanen ciiin wajen da zullumi, ummii idan tace bata shiga mummunan tashin hankali bama toh wannan ta yaudari kanta ne , tunowa da tayi irin tashin hankalin da tashiga lokacinda akasabarda ita cewa an harbeshi ahalin yanzu da sukasan cewa rayuwarsu tana cikin hadari dole zasu nemi yadda zasuyi kuga bayansa,"
Ayanzu kam bataga na zama ba dole dukansu sutashi da addu'a."
Lokacii d'aya suka miqe da mama kamar wanda ko wacce tasan abunda d'an uwanta yake sakwa acikin zuciya, alola sukayi sukai nafiloli sannan suka runga roqan Allah yarabasu da matsalolinsu sannan yarabu daga sharrin duk wani mai sharri."
Chapter 84 · 0% Book details