← Book details Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 87

Sashe 1

Bibiyata Akeyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Compiled by Umar Dalha.

. BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
_Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)_

Page 1

Zaune take acikin wajan amma hankalinta baya jikinta domin kana kallanta kasan tana cikin matsananciyar damuwa wanda hakan yagaza boyuwa sanda yanuna akyakyawar fuskarta,

Tunani take acikin zuciyarta shin ko tajene tasamesu taji dalilin wannan *bibiya* da takura dasuke mata ne, atake wata zuciyar tayi saurin gargadarta domin batasan mugaye bane,

Amma aida mugaye ne dasun dade da cutar dake, wata zuciyar tace da ita. Mtswww taja wani dan siririn tsaki, ni wallahi tsoronsuma nakeji tafada cikin muryar kuka tareda kifa kanta ajikn table dinda yake gabanta.

Tosu wayannan mutanen suwaye?? mesuke nema awajanta??? Wani laifin tamusu dasuke *bibiyar*rayuwarta?? dataga dai bata dayadda datasamu amsar tambayoyinta kawai tamike tare da zarar jakarta tayi hanyan fita daga restuarant din dake cikin school din zuwa hall na lectures dinsu tana kallo daya yayiwa daya mZ33yyb3rw3ramu nuna masa ita yayi akan tatashi subita koda taga haka wuff tafice daga cikin wajan batareda datsaya biyan kudiba dan damuwa bata barta tayi ordering komaiba

Koda tafita tayi noticing ana binta amma hakan be daga mata hankalinta dan abunyafara binjiknta direct hall dinda zasuyi lectures tawuce tasamu har malamin sunshiga sa'arta daya bame tsanani bane yasa tayi saurin shiga tasamu gefen kawarta amira tazauna

Amira rada tamata akunne ke inata kiran phone dinki ina kika shiga kikabari phone anata kira banza ainaso kiyi missing attendance,

Gabaki daya wannan surutun da amira takeyi batasan atakure dakeba kawae tatashi tacanja wajen zama tace kici kanki

Ana tashi kuwa ko takan amira batayi ba tafice dama shine last lecture dinsu na ranan, kodatafita batayi mamakin ganinsu ba don tasan za'a rina (wae miji ya saki mata ubansa yaje zauranci)
Fita tayi tawuce gida koda tana keke napep ma haka taga suna binta sanda tazo dab shiga gida kafin suka juya,

Tana shiga gida tasauke wata nauyayyan ajiyan zuciyarta,
Da sallama tashiga tasamu babansu harya dawo tatsuguna aladabce tamasa sannu da hutawa ya amsa cikin sakin fuska sannan tatashi zata tafi harta fara tafiya naji yace, *hanna*

*Hanna*ni unknown nakara maimata sunan araina nace amma sunan yayi saurin juyowa tayi cikin ladabi da nitsuwa tace na'am baba yace idankin shiga ciki kyakiramin mamanki toh tace tareda juyawa

Tacigaba da tafiya cikin nutsuwa giftawa tajeyi taji wani zancen daya hargitsa mata Tunani yakara gigitata tare da tsundumata cikin damuwa kunnenta takara kawowa kofar dakin taji hajiyah lami wacce suke kira da Amma tanacewa,

Ai aikin malam nakarangi yanakyau kiduba tun yarinyannan naarama danasa yatura mata aljani wadda ze hanata aure aizancen danake miki haryau bbu wanda yataba sallama da sunan yazo wajanta ga yan uwanta komai ya kankama biki kawae muke jira itakuwa shiru kikeji kamar an aiki bawa garinsu tana gama fadin haka suka tafa tareda shekewa da wata shedaniyar dariya aibata jira sunkara wata maganar dazata daga mata hankaliba tawuce jiri na ebar ta harshirin yasadda ita yakeyi

Tana shiga dakin mamansu kawae tafada kangado tasaki wani marayan kuka me tsuma ran me sauraro

Temakonta daya mama bata dakin yasa tayi kukanta mai isarta daganan tatashi tawanke idonta daganan taadauro alola tayi la'asar tayita addu'o in neman tsari daga sharrin mutum da aljani

Mamane itada inna kaltu mai aikinsu Zaune akicin tana dafawa baba ruwan shayi ni inna kaltu kuwa kinga diyarki tadawo daga makaranta

Najita shiru haryanxu batazo tacemin tadawoba inna kaltu take aikwa bangantaba inaga bata dawoba, to halan cewar mama dauke da gajeruwar damuwa aranta

Yarone dan kimanin shekaru 12 yayi sallama mama waekije inji baba yana falo yana jiranki toh kace masa ganinan zuwa

Fita tayi daukeda farantin ruwan shayi ahannunta tanufi falo anan tatarar da baba yana karanta jarida sallamarta ce tasashi ajiyewa tareda zare gilashin dake idonsa amsa sallamar yayi sannan takaraso ciki tazauna tazuba ruwan shayin tamika masa yakarba yadan kurba sannan yayi gyaran murya mama tajuya ta fuskanceshi dan da'alama maganar dayakesonyi mai mahimmanci ne

Shin waini halima meyake damun diyarkine gabaki daya ina lura da ita kwanannan batasakewa batada walwala shin meke damunta?? Hmm wani gauron numfashi taja wallahi alhaji nima kwanakinannan haka nake kallonta narasa meke damunta nifa alhaji inaji yarinyar nan dagaske fadan mutanenne halan aljanine ya aureta

Kul karnasake jin wannan zance abakinki baba yayi saurin gargadarta ni inaji aji kina wani alkhairi ne yake BIBIYAR RAYUWARTA kace mahaifiyarta keyakamata kije kiji damuwarta

Bayan ta idarda sallah ne taki shingida tafara gyangyadi tagakamar inuwar mutum akanta agigice tafarka ta............

Shin wae wayake BIBIYAR rayuwar *hanna*??????????

Shin wae Su wayannnan mutane dasuke BIBIYAR yaruwarta ta suwayene???????

Shin dagaske Aljanin da aka turo mata ya sameta kuwa ko akwae wani boyayyen al'amari ne

Domin samun amsar wannan tambayoyi kubiyoni musamosu tare

Ur's
Z33yyb3rw3r

BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
_Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)_

Page 2
*
Gani tayi kamarda inuwar mutum akanta agigice tafarka lokaci daya kuma tasauke ajiyar zuciya ganin mama dake tsaye akanta,

Sunkuyar da kanta tayi sannan tace sannu dashigowa Mama batareda ta amsa taba tasamu waje tazauna sannan tace *hanna* ta dago takalleta cikin sanyin murya tace na'am mama,

Meyake damunki kifadamin dan banasan kallonki cikin damuwa murmushin yake ta kirkiro sannan tace bbu komaifa mama mekika Gani shiru mama tayi tazuba mata ido tana nazarin yanayinta ta kunsan uwa da danta koyaya dah yakai da boye damuwarsa takan gane yana cikin damuwa

*hanna* sunanta da mama takira ne yasata dago kanta daga sunkuyen da take sannan tace na'am mama tadaura da cewa nimahaifiyar kice kina tunani idan baki fadamun damuwarkiba akwae wanda yacancanta kifadawa bayanni

Murmushin yake takara kwakulowa sannan tace Allah mama bbu komai kainane yakemin ciwo kuma gashi samester yazo tsakiya karatu yafara zafi

To Allah yasauwake kisha magani saikihuta mama tafadi hakane bawae danta yarda cewa yartata bata da wata damuwa ba, kuma bawae dan tanada tabbacin datasha maganinba

Mama nafita tasauke ajiyan zuciya tareda jawo alqur'ani taci gaba da karantawa nantake taji kashi tamanin daga cikin dari na damuwarta ya gushe damuwarta ta batafi saura kalilanba

Rufe qur'anin tayi sannan tanade pray mate din cikin natsuwa tanufi kofar Fita daga dakin

================

katafaran masarautace mai girman gaske
Wanda ko bantsaya muku bayaniba kunsan yanayin girman masarautar kano dan tana daya daga cikin masarautu masu girman gaske
A wannan kasa tamu masarautace mai yawon jama'a

Da dumbin alkhaire atattare acikinta wanda kuma tasamu adali jajirtaccen sarki dattijon arziki mai farar aniya

*Sarki*Abdulaziz lamido

Wata mata nahango zaune akatafaren falon sarki wanda yasha kayan alatu dana more rayuwa matar dake zaune afalon kana kallonta koba'afada ba kasan itace matar sarki domin ko daga yanayin kayan dayake jikintama zainuna hakan balle azo zuwa yanayin fatar jikinta

Dukda dai bawata walwala atare da ita amma hakan baihana kyawun fatarta futowa kallo daya daka mata kagane damuwar dake tattare afuskarta

Ahankali tasa gefen gyalenta tamatso kwalla sannan tace mai martaba badai kanaso kagwadamin bani na haifeshiba shiyasa kaki amincewa da kudurina amma kasan yanda nake sansa araina koh yayan dana haifa bana sonsu haka

Kasan yadda nake jinsa araina kuwa tafada cikin muryar kuka inajin ciwo acewae shekara 35 amma haryanxu yagagara yin aure kuma munzuba masa idoh muna kallonsa

Nifa wannan yarinyar daya damu da ita atunanina aljanace ba mutum ba, mai martaba yakura mata ido kawae domin bayaso yatsaida ita saita dasa aya

Sannan taci gabada cewa tayaya xa'ace shekara tara kenan kullum zancensa mutum daya bamusanta bamutaba kallontaba

Mai martaba baza'aduba wannan zance ba idan da'abi shawarata atara malamai kawae suyita masa rokon Allah har adace wannan aljana tarabu dashi

Gyaran murya mai martaba yayi sannan yace bawae naki tatakiba amma yakamata mujira harsai shekatunda ya eba mana suncika kafin muyanke masa hukunci

Ainida ba se anjira ba dan wannan ba mutum bace ga yar uwarsa intisar aisai ahadasu

Kilishi Kilishi Kilishi mai martaba yakira sunanta tareda hadaerai sannan yace

Nafada miki alkawari na dauka zanbarshi yacika wannan lokacinda ya eba donhaka banasan sake jin tashin maganar nan

Toh tace amma bawae dan ranta yasoba sannan tatashi tawuce zuwa shashinta

Tana Fita fadawa sukafara kwasan gaisuwa amma ko kollonsu batayiba tawuce dayake Kilishi Allah yayita mace mai girman kai dakuma nuna isah

================

Zaman cikin gidanne yasoma gagararta domin sai habaice habaice kawae akeyi

Koda Mama taji abinda Su Amma sukeyi hakan baisa tatanka musu ba dan inda sabo tasaba kuma Allah yayita mace mai hakuri wanda gane fushinta abune mai wuya

Juyarda kanta tayi wajan inna kaltu sukacigaba da aikinsu domin yau itace mai girki domin bata taba bari mai aiki tayi ma mijinta abinci itata keyin kayanta

*Hanna* tashi tayi tayi da niyar shiga daki Hafsat da rabi'ah wanda suke yayu a wajanta ne suka tafa tareda shekewa da dariya Hafsat tace dama wasukam Ai saidai Zaman daki domin ba mashin shini suka kara tafawa yoh saima kunbata bakinkune kewar amma aixaman daki yanxu akaafarashi

Zuruf *hanna* tashige daki domin itama kanta abunyana damunta wani irin bakin jinine dani tafada tareda fashewa da matsanancin kuka

Amma yau tasamowa kanta amsar tambaya tada dade tana addabarta aranta, aljanine dagaske ya aureta tunda da kunnan ta taji bawani bane yajimata

Toh sukuma wayannnan masu *bibiyarata* suwaye shin ko suma aljanune??? ta tambayi kanta

Wannan tambayarne haryanxu takasa samun amsar ta kuma batasan wazata nema ya amsa mataba

Saidai takudirta aranta bawanda zaiji wannan zancen
Ai idan aljani yafi karfinta Toh itama akwae wanda zata kai karansu wajan sa

Tadauki alkawarin yin tsayiwar dare tahana idanta barci harsai Allah yamata sakayya da wayannan azzalumai masu BIBIYAR rayuwar ta.

Shin wae waye itah wannan hanna?????

Shikuma wannan wanda iyayansa suke tunanin aljana ta aureshi wayeshi????

To be continue

Ur's
Z33iiyyb3rw3r
BIBIYATA AKEYI

Bismillahirahmanirrahim

Writing by
Zaynab Bawa (z33iiyyb3rw3r)

Page 3
*
DUBAI

Wani tangameman gida nahango, wanda fadin girmansama tsayawa bata bakine, kyawunsa kuwa kokadan baya misaltuwa domin bansan dawani yare zanmuku bayanin da har zakugane kyau tsaruwar wannan gida ba, hatta tsaron gidan ma, sojojine masu tsaran gidan sunza gayeshi , tako wani sako da lungu gaba da baya,
Azatona tunda kasar larabawa ne nadauka sojajin larabawa zangani amma inah zancen yasha bam bam,

Sojojine kala kala wanda kowace kasa sanda suka bada gudumawa wajen kare lafiyar wannan bawa nasa, kowani soja yana sanyene da kakin kasarsu sojojine bila adadin wanda irga yawansuma bamai yiwuwa bane,
Chapter 1 · 0% Book details