← Book details A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 28

Sashe 5

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Dedicated To my Yar gatah°°°°🌹 Real Khady*
_Masha Allah for d completion of ur amazing and fabulous novel called *"Suhailat"* the most amazing and sweetest novel ever.​​ Congratulation one again_💋
_​My Love For you is deep and True baby....i Love You with all my and i always will Honey... I Love You so Much... I love you so Much...... I love you So much........._💓💓💓

*📄 PAGE 15____16*

Waje suka samu suna Shan Iska, nan suka fara Hira sosai tsokana tsokana, Soyayya soyayya gashinan dai dan hiransu bame tantance inda suka Dosa...

Xeexee ce tace Kasan meye Yau nayi frnd safiyya a school kai tanada kirki sosai walhi, tasan abun da takeyi. "ismail ne ya wani hada Rai yace frnd bayan Ni? Amma bana hanaki yin kawaba,

"xeey ce tace baka gantaba wlhi kaima da zakaso ace frnd dinkane, Taba baki yayi yace tab akai kasuwa, dan shi ganinshi yakeyi kamar frnd indai ta wuce Xee to Gaskiya se ahankali dan wani irin tsakuwa sukai Sosai,

"Tace Ya naga ka wani bata rai Frnd fa nace ba Saurayiba, kara bata rai yayi yace to ina ruwana da frnd nidai kisan frnds din da zaki dinga kulawa, dan da bakinki ma kina fada ki ba wata frnd da zaki after ni se gashi Ke kinyi, Nan dai suketa abunsu akarshe ma Fada Sukai kowa ya Tafi gida babu dadi a Ransu, gashi duka in suna tare basasan rabuwa amma Hakanan kowa yai xuciya ya tafi Gidansu...........
××××××××××

*AFTER 3 Months*

Hajiya halima ce kwance a daki yau ta tashi batajin dadi ko kadan dan ko Pallow ta kasa fitowa Takai kwana 2 a haka, yaudai abun yayi worst Ne. Alhajine ya Shugo dakinta yaga ko ina ba a gyareba Yasan ba lafiya ne tunda 2days da suka Wuce ba a dakinta yakeba, Rawar sanyi yaga tanayi ya taba jikinta yaji zafi dau, Subhanallah yace tare da fadin Halima meke damunki, Kasa magana tayi dan ba karamin Jin jiki takeyiba, Temaka mata yayi ya dagota Ya kira driver Da sauri ya bude mota aka Sata,

___Jin tadar motar ne Yasa Hajiya Sa'adatu Ta leko ta window dan ganin waye zai fita ko Alhajine ba Sallama, Kawai taga Alhaji na kokarin Sa hajiya halima A mota, Da sauri ta fito tana subhanallah, Meke faruwane, Alhaji yace asibiti zan kaita batada lafiyane zamuje a dubata meke damunta,

Hajiya sa'adatu a xuciyanta tace senaje jin kwakwaf dan haka tacewa Alhaji a jirata Taje ta dakko hijabinta su tafi tare, Yace to ki sauri, dakkowa tayi dan gulma a cikin motan Ta karashe sa hijib din driver kam yaja mota sai Wani babban *Ummiey_Xeey specialist Hospital* Nan aka fara gwadata akace admitting dinta zasui dan akwai wani Blood tests da zasui mata Alhaji yace badamuwa Ko nawane Ai mata, Hajiya halima kwata kwata batasan ma Inda Kanta yakeba,.... Koda su Xee suka dawo gida akace mamanmu batada lfiya Kuka Take tayi Dan har seda dad ya Dawo kenan zai kwasa wasu kaya yaganta ta takure se zabga kuka takeyi Abba kuma yana gefe shima yai tagumi

Dad ne ya karaso Inda suke yai hugging dinsu yace su kwantar da hankalinsu momman Su zata Sama lafiya

Nan ya temaka musu suka Shirya sannan driver ya jasu basu tsaya ko inaba se wani babban shag, nan yai musu siyayya suma na kayan dadi sannan yai wa mamansu siyayya itama then suka wuce specialist hospital
Suna zauna ne time din hajiya Halima ta Dan farfado ta samu taci wani abun tai wa kishiyarta godiya

Alhaji Abdullahi ne yace basu kawo texts din ba be gama rufe bakiba se ga WATA nurse ta Shugo dauke da murmushi ta gaisheshu Tace mika da Alhaji result din tana cewa Congrats

Dubawa yayi yaga matanshi Nada cikin WATA Biyu, Yace Wow..Masha Allah

Halima Ashe cikine dake baki fadamunba har tsahon WATA biyu

Tace haba dai Alhaji wani irin ciki yace gashinan dai ai ba karya zasui ba

Zee CE Dan murna ta kwalla ihu Tace wow Alhamdulillah,

Hajiya Sa'adatu kuwa tsit kake jinta Dan jikinta gaba daya mutuwa yayi

Gabantane yai wani mugun fadi Tace Halima ciki, Ikon Allah Alhaji yace eh wlhi ya mika mata result din ta gani wani bakin ciki taji ya mamaye mata Zuciya ohhhh Allah ta fada

Tofaaaa

*Muje zuwa kuyi hakuri ba yawa*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍

*the whole page is dedicated to you Miss_Xarah_Mansur❤ “Thank you for your love that you show me regularly. I love you Sweet Heart*❤

*📄PAGE 17___18*

Alhaji Abdullahi Murna Yakeyi Kamar wannan Karon Ne cikin Fari, Ita ko HajiyA Halima Tana fama da Kanta Hamdala Kawai takeyi a zuciyanta....

Sa'adatu ne fa nan abun duniya ya isheta, Kasa sukuni tayi amma Setaita wayincewa, Tace Dai bari Taje Gida Ta dawo Tayi mantuwan Ruwan Zafi a heater, Alhaji ne yai mata wani Kallo Irin taya zata fito akwai heater a gida ba ya hanasu ko ina zasu Su dinga kashe Komai ba, Tace yi hakuri Alhaji, Ta tashi da wani jikinta duk a sanyaye tai musu Sallama Ta kama hanyar Gida,

Tana cikin Napep ne ta kira aminiyarta Yalwa Tace su hadu a Gida Dan Allah Zata dau mataki, Tace namefa Hajiya, Sa'adatu Tace Sai kinzo Kawai Kawata, Me napep kam se satan kallonta yakeyi ta madubi amma ba halin magana,

********
___ Bayan Tafiyar sa'adatu Ne Alhaji ya kalle matarshi Halima da yaranshi Yaji wani Irin Nishadi kawai yakeji, Nan yaketa godiyawa Allah Daya bashi Yara, Duk tinaninshi daga Abba Bazata kara haihuwaba dan Se After 7years Take haihuwa wannan karon Kam Har Ya Shiga kusan 9 shuru, Ikon Allah kenan dama ko wace haihuwa da yanda take zuwa Maka.....

"halimace tace Alhaji ka kira kanwata Mariam Tijjani Ka sanar mata Da ina Asibiti, Yace ok Yauwa dama ina so indan Fita nan take ya kirata tace Tana ma hanya zata wani wajen ne Amma Gatanan Zuwa, Ba ai 10mins ba segata Ta Shugu, nan ta sama waje ta zauna Tai mata Sannu Sundan taba hira Kadan da yake mutuniyar Alhajine, Sannan Alhaji Ya fita zaije inda zaije,

"Su xee kam makalemai sukai Seda Ya fita shan ice cream Dasu, Nan dai Hajiya halima da kanwarta Suketa Hira dan zuwa yanzu Ta wartsake...

""Hajiya sa'adatune ta rasa meke mata dadi yanzu dai ta zama Juya Kenan ba Haihuwa se yawo takeyi a tsakar Gidan Tama kasa Zama Gaba Daya, knocking Taji Me gadi yaje ya bude Dama Tasan ba kowa bace se Aminiyarta YALWA....Rungume ta Hajiya sa'adatu tayi irin Taji dadin Zuwanta Dinnan, Daki Suka Shige, sa'adatu Ta zauna ta hada kai da gwiwa

Yalwace Tace Meke faruwane Ki natsu ki fadamun Yar uwa ko zan temaka Miki, Hajiya sa'adatu ta dago jajayen idanuwanta Tace yar uwa dole ki temakamUn, mamansu Xeexee Fa tana asibiti wai Cikin wata Biyu,

"Hajiya yalwa Ta wani zare ido tace Ci me?? Sa'adatu tace Yanda kikaji Ciki gareta Har na tsawon Wata biyu Anan Gidan...

Yalwa Tace Tabdijam Lallekam Bazaki Zaunaba, Yanzu Meye Shawara, Tsakaninta dake kafin tazo nan Gidan Shekara 10, yanzu Da auranta Kusan 17kenan Fa 27years Kenan kinanan Godan baki ajiye Komai Ba, gaskiya dolene musan matakin da zamu dauka da gaggawa Inba hakaba ai na shiga Uku Inji sa'adatu kenan,

"Yalwa ma Tace har tarama sai kin shiga tunda yanzu yana mutuwa yan uwanshi da yayanshi zasufiki gado, _subhanallah_

"Hajiya sa'adatu Tace tun muna england Nayi shawaran Zan amsa Xee amma yanzune Right time din daya kamata Na amsheta Inyaso......seta matso kusa da kunnanta Ta fada mata wani zance.... Tafawa sukayi Yalwa tace Aikinki nakyau yar uwa yanzu ki sakar musu komai ki nuna irin Bakyajin haushinsu inyaso..........

_Nasan readers kun kosa kuji me wa innan matan biyu suke Shiryawa Karku damu inanan daku, kuci gaba da biyoni zakuji komai Har End..love you All_

Nan suka wani kwashe da dariya, Sa'adatu tace kiyi hakuri ko ruwa ban kawo mikiba, Yalwa tace haba Ba komai Nan gaba idan komai ya kankama Ba ruwa Ma kadai zaki kawomun ba har wani abu me kala na roba....,

Sa'adatu tace sai yasa nake Sonki yanzu to Ki tashi muje mu gaisheta nan suka shirya Suna fitowa suka sama napep se *ummieyxeey specialist Hospital* Room din suka Shiga suka sametama tana bacci se sistern ta Mariam tijjani tana daddanna wayarta da alama Chat takeyi a group din taurarin Mata,

gaishesu Tayi Suka tambaya yame Jiki tace da Sauki Alhamdulilah, Sukace Allah kara sauki Tace ameen; taci gaba da chat dinta abunta.......

********

Bangeren Ismail Kuwa Yau wuni chur bega Beloved Xeexee Dinshi Ba ya kasa zama ko abinci ya Kasa chi da yaji Moto ya wuce seya leko gate ko su xeexee Ne, Yayi hakan Kusan 7 na karshene yace bazai koma Ko inaba Dan haka Yai Lamo A gado ya fara tinaninta chan ya hango wani cardboard Paper ya tashi ya dakko hade da wani dan table yazo ya zauna a bakin Gado ya ajiye Cardboard din Kan table dinnan Ya dakko pencil ya fara zana Xeexee (Drawing) Beyi Taking Time ba ya Gama Drawing ne Amma Tayi kyau sosai kyanta ya fito dan har wani smiling Yasa Drawing din yakeyi, Dauka yayi ya kwantar dashi a chest dinshi Kawai wani nishadi Yakeji Daya kalla Drawing din Se shima Yai murmushi Yace I love You my xeexeeeeeeeeee!!

Karar moto Yaji.......

*Kuci gaba da kasancewa Dani*

TEAM XEEXEE
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍

_Dedicated this page to you my beloved frnds..I love you so much_
Hummyluv
Armeenat
Ameemee
Fresh khady..

*📄PAGE 19___20*

Karar Moto yaji ya ayyana a ranshi Yace nasan ma basu bane ba Inda Zanje, Yaci gaba da Kallon Drawing din da Yayi,
Chapter 5 · 0% Book details