← Book details A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 28

Sashe 11

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Xeey tace ke kika sani nikam bari na kwanta kafin Teacher ya shugo.....ta kwanta, Safiyya kam taji dadi tana ganin xeey ta fara gyagyadi ta dakko school bag dinta kamar tana Neman abu tai wayau ta saka mata memon da ismail Ya bata... Seda ta tabbatar ta saka sannan itama tadan kwanta haka dai suka karasa period din ba teacher daya shugo..

Har akai closing... Suka Koma gida, Nan ta tube kaya tasa kayan aikin dan dama ta saba kullun ta dawo ba hutu.. Haka dai ta kwana tanajin jikinta wani iri amma Batasan meye ba...

Washe gari ma haka taje school ko school bag din bata taba ba cos SS3 suke ba wani teaching ake zuwa yi masu ba......
****
_IsMail Kam Alhamdulillah ya isa kasar egypt lafiya An bashi daki suna zaune tare da wasu..... Su 3 ne a dakin dayan yana 300lvl me suna *musaddiq* se dayan yana 400 me suna umar shi kuma ismail yana 100lvl

kwansuu biyu suka shaku sosai dan halayansu tazo daya da *musaddik*dan har fadawa juna secret sukeyi dan su biyun jininsu ya hadu..Umar be Shiva Shiga tsabgarsuba

"Kullun ismail ya kira numbern xeey a kashe kome yasa oho yana tinanin ko fushi tai dashi dan be fada mata gaskiyar maganar Ba... Oho

*After two days*
Ranar friday da daddare Kamar ance xeey bude school bag dinki ta zazzage chan ta hango wani memo pink cikin Books dinta Tace meye wannan halama safiyyace ta manta Ta saka, tana dakkowa taji kamshin tilaren Ismail da sauri ta bude, zare idonta tayi takara kallon rubutan dake cikin memo din na first page an rubuta
*Xeeeetah* _I don't even know where to start cos i surely missed you_ zagaye da wasu flowers da stickers na love..

Kara bude 2nds page tayi taga.....
_My love, words however special ... could never even start, to tell you all the love I have for you within my heart_

_Loving you could take my life, but when I look into your eyes, I know you're worth that sacrafice_

_I miss you ... I need you ... More and more .... each day ... I love you ... more than words ... can ever say_

Haka take tayi har seda takai karshe taga duk abun love ne da missing...

Ruwa taga ni a jikin memo din ta taba Taga inda take ba ruwa, Taba fuskarta da zatai yaji ashe a jike yake hawaye ta ko ina........

*Ummiey Xeey*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​*
*UBA​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​```
*​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​*

*​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

*​​OCTOBER 2017​​*

```​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​```
*​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​*

*_WANNAN SHAFIN MASOYANE...ku warwasa JIRKIN SO ZAI TASHI_*
```AISHA UMMA, AISHA A MUHD, MY MEELAT, REAL KHADY, MISS_XARAH, HUMYLUV, BILKISU BK, and all Members of E.W.F♻```

*📄PAGE 39__40*

Taba fuskarta dazatai taji ashe a jike yake da hawaye ta ko ina dan haka ta tashi ta dakko handkichip ta share hawayenta, Lalobu wayar tayi ta kunna wata xuciya tace to ina zaki sama numbernshi? Ajiye wayar tayi chan sega text ya shuga, budewa tayi taga ansa i was calling your number tun shekaran jiya a kashe hope dai bani bane? Tana gama karanta Text din numbern ta duba taga ya fara da +201.... Smiling tayi Tace he's the One.. Dialing din numbern tayi taji a kashe... Dan haka tasa phone din a chaji, ta dakko memo din se re_reading takeyi tasashi a chest dinta har bacci ya kwasheta...

Washe gari nayi weekend ne da yake dad nanan sa'adatu ita ta tashi tai komai, xeey kam ba karamin dadi taji ba dan Zata sama enough time din da zasui chating da sweet special dinta..

__Aiko tun 8 suka fara chating farko kuka take tamai akan ya ze mata haka yadai bata hakuri yanzu ne suke da damar gina frndship dinsu ba tare da kowa yasa musu ido ba, dan Haka ta sake jiki ranar sunsha chating like no tomorrow....

"haka komai yake wakana kamar yanda kuka sani, xeey da ismal yanzu sun kusan 2months komai na tafiya normal tana kawo mai complain din Halin da suke ciki, sedai ya bata hakuri....

**********
akwai wata Rana da sa'adatu tana zaune duniya na mata dadi, xeey ta tafi hadda cos yanzu ba xuwa school takeyiba ta gama, Hajiya sa'adatu ta dauka waya ta kira kawarta akan tazo zasui wata shawara,

"hajiya yalwa haka ta kwaso jiki tazo dan su zanta da kawarta, su kadai ne a gidan amma saboda gulma seda suka kara shiga bed room suka dan tura kofar, Nan Yalwa ta bata sha'awaran akan Ta kashe Abba, dan idan ya girma ba karamin barazana zata fuskantaba dan tace mata idan Dadynsu nanan yai ta shigemai kamar xe fada mai wata magana dan Haka sa'adatu ta amince da wannan maganar

*Bayan Kwana biyu.....*
Sa'adatu wani Sabon Salo Ta fito musu dashi...makircin yau daban na gobe daban, Su xeey sunyi kuka har sun gaji ba matemaki se Allah... "sa'adatune Zaune kan kujera tayi tagumi duk abun duniya ya isheta, Ta Rasa yanda zatayi, kwasan sega Alhaji yaganta cikin halin damuwa Yake tambayarta meya faru, Tace Alhaji wani abu kawai Na tina Game Da Xeey, Kaga Ismail ta tafi kasar waje karatu, kuma ina me tabbatar maka bazasu Rasa magana da xeey ba, Karfa yaci gaba da hure mata kunne dan Haka Nake Kara rokanka akan maganar da mukayi kwanaki Akan mu chanza unguwa..kar ya dawo ya samemu anan Ina tausayin Xeey ne, Seta fashe da kukan munafurci...

"Alhaji Yace kai Amma hakane wannan shawaran nagode Nagode, kuma zanyi kokari na amshe wayanta Nan take Alhaji ya kira Xeey Ya amsa phone dinta ya babbabla sim din. Hankalin Xeey ya tashi sosai daki ta shige taci kuka sosai har tana kiran bro Abba Ta fadamai yace sist kiyi hakuri dan Allah komai Xe wuce Tace ok bro ba komai sukaci gaba da hiransu...

_Bangeren Ismail Kuma yayi kira har ya gaji tun yana boye damuwarsa har ya fada ma frnds dinshi fa ga halin da yake Ciki a takaice dai har basu labarin Yarinyar wato xeey yayi irin wahalan da suke sha wajen *MATAR UBA* suma sun matukar tausaya mai amma sukace may be wani abun ne yasa ta kashe wayanta suka dan kwantar mai da hankali but kana ganinshi kasan Yasha Missing LOLz dan har dan rama yayi

*AFTER TWO WEEKS*
Akwana a tashi ba wuya Yaune Alhaji Abdullahi Suke shirin Tashi su Koma sabuwar unguwa tun 5 aka tashi dama already an riga ankai wasu kayan chan wasu kuma sababbi aka siya, Gidan yayi kyau masha Allah, sa'adatu kam Dadi kamar ya kasheta dan Dadi dama abun da take So kenan Yanda zatai Abubuwa Son Ranta.. Yalwa kam Yanda kukasan gidan tane dan se wani rawan Kai takeyi.... Xeey kam Hankalinta a tashe dan Tasan ba karamin wuya zasu sha ba sedai muce Allah Ya tsare mu da irin wannan *MATAR UBA*

°°°WASHE GARI....
Sa'adatune Zaune tana cin abinci hankalinta kwance, Alhaji Abdullahi yayi tafi xuwa Abuja, Abbane Ya shugo ze dauka ruwan faro a fridge wani tsawa ta dakamai wai kar ya kuskura Yasha yaje ya eba na fanfo, wani kallo yai mata irin begane yaje ya eba na fanfo ba, Sa'adatune Tace Baka ji bane nace kaje ka eba da fanfo, Ran Abbane ya baci ya tunkarota yace haba Ke dama muguwace na gaji da irin abubuwan da kike mana, yana magana Yana nunata da dan yatsa, abincin da takeci Ya kabar, Nan Sa'adatu ta mareshi tace baka da kunyane,

"Abba ma daga hannu Yayi ya rama har su 2 je kake Tas Tas; xeey ce ta fito daga dakin dan ganin meke Faruwa, Ai tana zuwa taga abun ya fi karfinta gefe ta koma tana cewa Bro please leave her, kallon xeey yayi yace Tab wlhi sena koya mata hankali haba sist bakya ganin abubuwan da take mana ne dan kawai mahaifiyar mu bata da Rai..

"xeey tace uhm; Nan Abba ya chakumota ya janyo kafanta ta fadi a kasa Das, kuma yaje dakinta yai mata kacha kacha sannan Yazo yace wlhi idan bata fita harkanshi ba zata sani...Yai ficewarsa, Xeey kam daki ta shige taji dadin abun da yai mata amma tsoronta daya kar Ta fadawa dad dinsu...

"hajiya sa'adatune nanan shurum a kasa dan ta tsinke da Abba tsoronshi takeji Sosai... Waya ta dakko ta kira Aminiyarta....

UMMIEY_Xeey
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​*
*UBA​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​```
*​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​*

*​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

*​​OCTOBER 2017​​*

```​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​```
*​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​*

*Dedicated to UMMIEY XEEY, RUKSAD AND AMNOOR NOVELLA AND AISHAN UMMA NOVELS group*

*PAGE📄43__44*

"Xeey Tace
Au Hakane, mum bari naje na saka mai nima na saka nawa "sa'adatu Tace Yawwa Yar babanta Allah miki Albarka, Tace ameen amma tayi mamaki Sosai Sosai........

"xeey ce bayan ta gama sakawa Kowa Ta dakko abincinta Tai daki Ta zauna Taci, Ashe sa'adatu na bibiyanta tana ganin ta shige daki dan Haka sa'adatu Ta shige kitchen Din ta dakko abincin abba ta barbada mai magani Kamar Yaji sannan ta rufe ta bar kicin din, "ba Ddewa sega Abba ya dawo ya kwalla wa xeey kira yace Sweet Sist, Ita kam already tayi bacci ma, Yana shuguwa Da Hajiya taji motsinshi yana kiran xeey tace mai ai tayi bacci me kake bukata ne? Ya nuna Cikinshi Alamun yunwa yakeji,

"hajiya tai wani murmushi na mugunta shi abba duk be Sani ba, dan haka ta nuna mai kicin tace abincinka nachan kaje ka dauka, ya shiga da murna ya bude yaga abinci lafiyayye Kamshi ya bade ko Ina da sauri ya dakko ya bude frigde ya dakko ruwan faro sannan yazo ya zauna a pallow Ya fara cin abincin hankalinsa Kwance....
Chapter 11 · 0% Book details