← Book details A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Riga da wando ya saka kasancewar Ismail bameson manyan kaya bane SOSAI, Riga blue se wandon jeans se p cap daya saka, kayan sun amsheshi, saboda farine yanada kyau masha Allah...Bike (Mashin) ya dauka sannan ya fita a harabar gidan, fita yayi amma besan inda zaije ba kawai se ya wuce wani park inda ake zuwa hutawa..

Yana shiga pack din waje ya samu ya zauna, ya kishinged e yana kallon sama tinanin xeey ya fara wai yanzu ta ina zasu fara neman tane!!
"Wasu yan manta ne zaune kana ganinsu kasan yayan manyane, Wata cikinsu naji tana magana tace Wow"" Ku kalla guy dinchan kuzo muje mu tayashi hira, se a time din dukansu suka maida kallo wa Ismail Har suna hada Baki sukace" *Wow he's damn cute...*

Kuci gaba da biyoni

Ummiey Xeey
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​​*

~Masu bina in turo maku daga Farko Ta PC, kuyi Hak'uri I can't amma zan bude group duk meso daga farko seta shiga~

*PAGE 75___76*

Se a time din dukansu suka maido kallonsu kan Ismail har suna hada Baki sukace" *Wow he's damn cute*.

"Ismail yayi nisa cikin tanini, kawai Sallamar yanmata su 3 Yaji, ya amsa da Wa'alaikumussalam tare da bin fuskar su daya bayan daya,
"Daya daga cikin sune tace ammmm! In bazaka damuba munaso mu tayaka hirane tun dazu muka ganka kayi shuru

Isma'il ne ya kalleta yace ohh yeah INA hutawane, daya daga cikinsu ta k'ara da cewa" uhm amma yanda kake dinnan ya kamata ace akwai abokin hira zakafi jin dadin zaman ae, dayar ta amsa da cewa" sisto baga muna nan ba ai se mu tayashi hiran koya? Shi dai binsu da ido yayi Dan yaga ko yace beso ba kyaleshi zasui ba, kawai yace alright _you're welcome_ dayan tace OK what's your name?
Ya fara magana ba tare da ya kalletaba yace *I'm Isma'il* sukace" wow what a nice name, yace" uhm, dayan tace" _well I'm siyama, daya tace I'm suhaila, dayan kuma tace I'm safiyya, Auta_ yace lol sunanku ya fara sa *S* siyama tace eh 3stars kenan, yace" to sannunku, nanfa Dan maganar da yayine suka wani gigice se zuba surutu sukeyi, shi kam in banda uhm da smiling ba abun da yakeyi,

Autace tace" bari naje nai mana ordan Abinci, shikam phone dinshi ya dakko ya shiga cikin gallery ya fara kallon pics din xeey tun suna school, wani murmushi yayi, suhaila ta taba, siyama tace kalleshi,

Isma'il ma yama manta da mutane a wajen, kallon pics yakeyi besan sanda yace Allah ya mallakamun keba, daidai lokacin da Auta tazo da abinci a hannu, tace" A cikinmu?

Ya kalleta irin bemasan me take cewaba, sukam siyama da Suhaila, kwashewa da dariya sukai, bayan sun gamane se surutu suke mai, auta tace" mtsww kai Ku tashe mu tafi wannan guy din batamu yake bafa,

Siyama ta kafeshi da ido ko zaice wani Abu tsit yayi ya bisu da kallo, suhaila tace" dagani beson magana please can I have your number?
Wani harare yai mata yace sorry bakui kama da Wanda zan basu number na ba, siyama taji haushi tai gaba abunta, auta kam dariya taiwa suhaila tace muje kawai Sist...

Bayan su yabi da kallo yace" ya salam wallahi wasu Matan basuiba, kalle shiga da sukai kuma sun shugo inda mutane ke yawan zuwa, Allah ka Shirya mana!!

Abincin kan table din da suka kawomai ne baiciba, ganin bakowane yace" Bari naci na banza ai ba aikensu nayiba, yaci ya koshi sosai, sannan still ya fada kogin tinanin xeey, nan danan yaji kanshi ya fara ciwo, kafin zazzabin yai zafi ya lallaba ya kai kanshi wani babban asibiti Dan dubashi.

Yana Shiga Aka nuna mai dakin da zaiga *DOCTOR*
Sallama yayi, doctor din ya amsa *(yayan Afrah)* ido hudun da suka hada tuni bro din Afrah ya m'ike yace Isma'il?
Isma'il ya amsa" da Musaddik

_Musaddiq yayan afrah ne da sukai school tare da Isma'il Wanda Isma'il ya dawo daga Egypt yana ta nemanshi...Ikon Allah yau Gashi sun hadu_

Tasowa Daga kujarar doctor yayan Afrah (musaddiq) yayi yazo, bashi hannu yayi suka gaisa hade sa rungume juna, Isma'il yace long time?

Musaddiq yace Alhamdulillah wallahi ba inda ban nemekaba I thought mafa baka dawo ba!

Ismail yace" wlhi nima nima na nema number ka na rasa, nan dai suketa hiran bayan rabuwa, gwanin sha'awa
Isma'il yace kayi aure ne? Musaddiq yace aa I'm still searching dai kaifa? Yace me too, sannan yace meke damunka? Isma'il yace wallahi ciwon kai nakeji ga zazzabi, nan Dr musaddik yama Isma'il allura sannan ya bashi magunguna, kuma yake sanar dashi anan yake aiki, Isma'il yace wow namaka Murna, Nima dai inanan INA nemane,
Musaddiq yace aiko ana Neman babban likiti irinka, I'll talk to them ansamu, Seka bani number ka, Isma'il yace wow ammafa Thanks wannan fitar nayi sa'a

Musaddik yace Lol Sosai ma kuwa, nan sukai exchanging number sannan Isma'il ya kama hanya se gida ciki da farin ciki,
Shima musaddiq yayi matukar farin cikin haduwa da amininshi na school..

Tun daga Bakin gate Mummy taji Ismail yana Kiranta mummy, Mummy, Mummy CE ta fito tana mamakin Isma'il kamar wani yaro yana kiranta, karasowa tayi tace" lafiya naga se kwalamun kira kake?

Isma'il yace" lol my Beloved mummy yau INA cikin farin ciki, mu shiga ciki, mummy girgiza kai tayi tace wannan yaron, zama sukai a pallow Sannan mummy tace'' wani farin ciki kake ko labarin Zainab ne??

Ummiey_Xeey
[1/3, 8:30 AM] UⓂmiey Xeey👄: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​​​*
*UBA​​​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​​​​​​​```
*​​​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​​​*

*​​​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​​*
_[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]_

*​​LIKES AND DROP YOUR COMMENTs​​*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​​​​```
*​​​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​​​*

_Dedicated this page you my dearest sisters_
```Ruqeey CE,
Nasbash
my Mareeya,```
*I love you plenty _# Ana Tare_*💕💕💕

*PAGE 77__78*

Wani farin ciki kake? Ko labarin Xeey dinne?

Isma'il yadan yi murmushin da bekai cikiba, Dan beson ma hiran xeey hankalinshi tashi yake, yace" no mummy INA wannan friend din nan nawa da nake ta nema banda contact dinshi? Mummy tace" Aww eh na tinashi, yace" yauwa yau muka hadu dashi wlhi naji dadi har yacemun anan Neman ma'aikicin Asibiti, Mummy tace Alhamdulillah, Allah yasa a dace Yace Ameen mummy nah,
Kallo ya farayi, mummy tace" gafa abincinkanan kan dining, Isma'il yace OK mummy zanci amma yanzu Alhamdulillah, Tace shikkenan, anjuma ma babanka zai dawo, Yace" Masha Allah, Allah ya dawo dashi lafiya..mum tace" Ameen

*********
Bangaren Sa'adatu ita yanzu hankalinta a tashe, yanzu kwata kwata Alhaji be mata magana, yana bata abinci da duk hakkinta na aure, amma shi kanshi yasan he's missing something, ko yaje office a tattare da damuwa yake, A gida ma haka, shidai kawai rayuwa yakeyi amma besan mekamai dadi ba, ko zaune yake ya tsundamu cikin tinani se ya fara tinanin Matarshi, sai kuma ya hargitse yaga kamar mafarki yakeyi, Hankalin Sa'adatu ba karamin tashi yakeba, kawai k'arshe ta take jira, yanzu dukda ta chanza wajen boka amma ba abun da take gani na ci gaba, Dan ba karamin addua ake yi mata ba ta ko INA amma duk bata saniba, yanzu bata da wani power duk tayi sanyi kamar tsohuwar munafuka!!

Bangaren Mariam Tijjani kuwa, addua ba rana ba dare, kullun setayishi, kuma rana dai dai ne bata mafarkin xeey, tana yawan fadawa mai gidanta, Yace" taci gaba da adduan, shima jikinshi yana fadamai Xeey na Raye, k'ara kwantar wa Mariam da hankali yake,

*Musaddiq* ne a office bayan sun gama aikin da zasui, around 4pm ne ya koma gida! Shima tare da farin ciki a tattare dashi, da shuguwarshi, Afrah ta kalleshi tace" oyoyo yau me aka samo mana naga se smiling ake ko anyi mana aunty ne? Xeey kam kallonta tayi tana mamakin Afrah!

*Bro musaddiq* yace see you, Afrah tai dariya, yace" Sister Xeey sannu, Halan se damunki da surutu takeyi ko?
Xeey tace aa bro your welcome tace" thanks sannan ya shiga ya gaishe da mummy, ya fito ya wuce part dinshi yai wanka yasa wani Wanda 3quater da yar karamar Riga yamai kyau sosai, bayan ya kintsane yazo yai joining din su mummy a tsakar gidan under wani bishiya dake cikin gidan nanfa suka fara hira SOSAI, Har yake sanar wa mummy yau ya hadu da wani frnd dinshi amma be fada sunansaba, yace mun Dade bamu hadu ba tun muna school yau Gashi mun hadu, Mummy tace to Alhamdulillah, Allah ya barku tare ya k'ara kareku da Sharrin mak'iya yace Ameen, basu suka bar wajen ba se gab da magrib, bro ya tafi sallah, su ma sukayo daki sukai alwala sukai salla basu suka mik'e kan sallayaba seda sukai sallan ishha'i Dan haka ka'idar su take, Idan sungana magrib basa tashi, addu'o'i suke Sosai Se sunyi Ishha'i sannan su tashi,

*After one week*
Haka rayuwa taci gaba da wakana ta ko wani bangare, *Isma'il* ne kwance a daki phone dinshi yaji yana ringing dubawa yayi yaga *Dr Musaddiq* yayan afrah, picking yayi hade da Sallama, dayan bangaren aka amsa, musaddiq yace my bro congrats, kasama aikin, but yanzu inbaka komai kazo da takardunka, Wani ihu Isma'il ya sak'i yace awwn I'm speechless, Bansan mezance makaba, thanks sedai mun hadu, musaddiq yace" OK frnd!

*Isma'il* ne ya fito pallow ya tarda mum n dad dinshi, nan yake basu labarin yanzu abokinshi ya kirashi wai yakai takardunsa, Farin ciki karara ya bayyana a fuskar su, Sukace Masha Allah, Allah ya temaka yace Ameen nagode maku, INA alfari daku, kuma da bazarku nake taka rawa! Daddy shafa mai kai yayi yace Isma'il Allah yasa albarka, Allah yasa a dace yace Ameen sannan ya fita
Yana fita car dinshi wannan karon ya dauka be zarce ko inaba se Asibitin, yana Shiga, kiran Dr musaddik yayi yace" gashinan ya shugo, ba' a wani bata lokaciba Sega Musaddiq ya fito yamai kwatancen inda yake yazo ya shiga dashi!
Chapter 20 · 0% Book details