← Book details A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sa'adatu tace Alright angama xeey kije ki daura kinjiko, Dukkansu sunyi mamakin Sauya musu da Tayi yan kwana biyun nan amma Suna tinanin ko *MATAR UBANNASU* ta chanza Haline, dan haka Xeey ta tashi taje Ta dauka komai tayi tagama sannan Ta sanar wa mummy dinsu Ta Gama, Tace Ok ki sama kowa a plate naga Abba benAn Kuma yana dawowa zaice zaici kinga kar kina Zaune Ya tadake,

"Xeey tace aww hakane Mum bari naje na saka Mai nima nasaka nawa..........

~Hmmmm Kuci gaba da kasancewa Dani...~

*Yours Ummiey Xeeeeeey*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​*
*UBA​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​```
*​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​*

*​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276

```​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​```
*​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​*

_WANNAN SHAFIN NAKUNE_ *♻YAN EXCLUSIVE*_INAJI DAKU HAR CIKIN RAINA..SONKU A JININA YAKE, HADIN KANMU NA BURGENI DOMIN DUK WANDA YAKE TARE DAKU HAKIKA YAYI DACE DA MUTANAN KIRKI_ *KEEP ON ROLLING THE BALL OF SOYAYYA*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*📄PAGE 45__46*

"Daren Xeey batai Bacci Ba, Kanta yana ta ciwo ga wani yunwa da takeji ga kayanta duk sunyi datti, Dakin har wari yakeyi _Allah Sarki_

_Safiya nayi Alhaji dakanshi Ya fincikota, Dama Ta gama harhada Kayanta, a ciki harda *MEMO* din da Ismail ya bata ita shikkenan Ta rabu da ismail se wani Ikon Allah,

"Alhaji kam fito da ita waje ya yayi ya kulle gate din tana Kuka tana Tino da dan uwanta Lalle Wata *MATAR UBA* tama sharri se kabar Garin yau gashi ita cikin gatan ta zatabar gidan Ubanta Allah Sarki...

"Haka take tafiya kafarta ma ba takalmi gashi abun takaici sa'adatu duk ta kwashe mata Kayanta Masu Kyau, Tana tafiya tana kuka, yara Suka fara tsokanar ta ga *MAHAUKACIYA* suna binta suna Tafi wasu mazan masu hankali su kora yara Wasu Kam Sedai su bita da ido... Tana tafiya har tabar ung batama san inda zata Ba, ga shi yunwa Takeji, Wani gefen Bola Taje na masu kudi ta zauna, Chan ta hango wani kankana, da lemo basui komai ba, a cikin leda, taje ta dakko ta fara sha, chan ko ga yara suka Kara mata chaa akai suna *mahaukaciya, mahaukaciya,* dan sanmun seta bige musu hannu....

"Bangeren Sa'adatu Kuwa suna zauna DQ Alhaji a pallor Tace bari nagwada Alhaji ko maganin zaiyi aiki sosai, Ta fasa kuka Tace alhaji Ka kora xeey ko, "Wani murtake fuska yayi yace me kike cewa waye kuma Xeey? bansantaba ai ni,

"seta tinsire da dariya Tace Aww, Wasane fa, Yace better shima ya wangale baki, Haka dai take tamai wayau tai ta amshe kudi wajensa, da kudin shi ake zuwa a karo Mai maganin da zai manta dasu kwata kwata.

__Haka dai kome ke tafiya kusan 1monts alhaji ya manta da komai Nashi, Yanzu sa'adatu ta All abun da takeso, se yanda tayi dashi
Shima, Alhaji baya ganin komai se matarsa a gabanshi, Dan yanzu ko office zaije dakyar ya zuwa dan wani sabon Makirce da dabara na soyayya da take nuna Mai....

Xeey Kam yanzu ta zama mahaukaciya na gaske, saboda tinani, Tashin hankali, Rashin bacci ga Zazzabi kullun cikinshi take ga matsanancin ciwon kai yasa Har *BRAIN* Dinta ya fara samun problem... Inta fara kallon abu harse ya bace, Haka yara zasu taro ko an mata magana batayi dan bata gane me Suka cewa Tadai zama mahaukaciya abun tausayi _Allah Sarki xeey_

"akwai Wata Rana da wata Budurwa yar matashiya da bata wuce age mate dinta ba 21 Haka tazo wucewa ta dawo daga School Na gaba da secondary, Kawai tai tuntube, dubawa da zatai taga ashe mutun ne a kudundune a wajen ga sanyi, Jikin fatima (Afrah) na rawa Ta kalleta tace mata sorry, Xeey kam kura mata ido tayi, Afrah ta tafi but se waige waige takeyi har ta isa gida hankalinta a tashe daki ta shiga taci Kuka sannan ta fito pallow, Har dare yayi but yanda afrah taga Xeey hankalinta har yanzu be kwantaba,

"Safiya nayi before Afrah ta taho school bayan ansa mata break fast dinta ta amsa ta shiga daki taci rabi tasa Rabi a leda da niyyar in zata school In har taga Xeey ta Bata, aiko haka akayi tana tafiya tazo daidai gun taganta a gefen bola afrah ta bude jakanta Ta dakko Mata Abincin da ta Rage Kwai ne da irish se bread, ta miko mata.. "xeey kam jikinta na rawa ta amsa batace tagode ba dan brain dinta nada problem, ido dai ta kura mata itama Afrah ta kura mata Ido tana mai tsananin tausayin yarinyar, Dan Allah Yayi Afrah da tausayi, Tana wajen xeey ta duba agogo taga zatai latti da sauri ta tashi Ta tafi school, Lectures akeyi amma hankalinta Gaba daya yana wajen Xeey...

__Xeey kam bayan tafiyar afrah ne Ta bude ledan taga abin dake ciki, Ci tafarayi kamar zata cinye yatsunta dan yunwa seda tagama ci tas sannan Ta sama wajen cikin bola ta mike tai kwanciyarta, Tana Cikin baccine taji kamar ana janye yar jakar Bako din kayanta ta bude ido ashe yarane ke so su dauke, Da gudu ta bisu tana zare musu ido gashi badamar magana,

*"Afrah* ko yanzu kusan 3months kullun tazo wucewa seta kawo Ma xeey abinci, Data lura yara ke kwacewa se afrah take zama har se ta gama ci komin dare sannan Ta tafi gida, Dan abincin da Afrah ke kawo Mata tanajin dadin ba karamin shakuwa sukai ba dukda bata magana, Idan taga Afrah har wani tsalle takeyi tana Murna.. Tasan cikinta xe cika,

__Akwai wata rana Afrah suna zaune da swt momma Sunan da suke kiran mahaifiyasu kenan, "Tace momma Please can i Ask a favour?
"Eh momma Tace you can,
"Afrah ta fara magana Tace wlhi Mum akwai wata yarinya Abun tausayi bata Magana ko ke kika ganta sekin tausaya mata shine please nake neman Alfarma Tazo gidan nan ta zauna, Afrah ta fashe da kuka,

"mum tace ki dena kuka afrah nasanki da tausayi kuma na aminci ki kira driver yazo yakaimu nasan ko Dad din kune ya dawo bazaiyi fada ba amma bari na sanar dashi... Nan Momma Tai dialing number babansu Ta sanar dashi Yace well it's Ok ba komai Allah Ya dafa mana, Kuma Allah yai mana jagora Tace ameen,

Nan suka Tashi suka nufa inda xeey Take dan dakkota Gidansu...

*UMMIEY XEEY*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR​​*
*UBA​​*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```​​​​​​STORY & WRITTEN BY​​​​​​```
*​​Ummiey_Xeey Abakson​💋​*

*​​♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​​​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*LIKES AND DROP YOUR COMMENTs*
FB..#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

```​​​​​​SADAUKARWA GA____​​​​​​```
*​​MARIAM TIJJANI ADAM​😍​* hak'ika ke yar halak ce domin kina daya daga cikin masu son ci gabana....kema ya Allah ya albarki rayuwarki da sister *Jeddah Adam Tijjani* MARUBUCIYAR *AL_MAJIRAH*...I LOVE YOU PLENTY❤❤

*PAGE 📄47__48*

Nan Suka Tashi suka nufa Inda Xeey take dan dakkota gidansu...
Tahowa suke a mota amma Afrah In banda Tinanin Xeey ba abun da takeyi, Mummy ce ta kalletace Tace sweet heart yaya dai, "Afrah Tace Uhm Momma ba komai shidai driver se driving Yake cikin hankali da Natsuwa har suka Iso daidai bolan Da Afrah Ta tuna mai,

"Parking din motar yayi 'yara suka chika a wajen Kamar Basu tab'a gani ba, Momma ce ta fara Fitowa, Xeey kam ganin mutun da tai a gabanta Yasa Ta dauke yar jakar bako dinta tana Shirin Guduwa.

"Muryar Afrah xeey Taji kamar ance ta waiga, Sukai Ido da Afrah Nan Xeey ta fara Murna Tasan Cikinta Ze Cika, "mummy kam kallon yarinyar tayi a zuciyanta tace Ikon Allah ai wannan daga GaninTa Gidan dadi ta fito ji gashin kanta kamar na fulani Ga Shi da tsaho Ikon Allah kenan, Allah yasa mu dace abun da Momma ta fada Kenan a Zuciyarta,

"Afrah Kuma Tunkarar Xeey tayi datai Tsaye tana kallonta kamo hannunta tayi tazo zata shigar da ita cikin Motar Hada ido da sukai da momma Yasa Xeey ta tokare tak'i shiga motar, Afrah na ta lallabata amma ina Xeey tak'i ta shiga,

"Mummy ce tace To ya zamuyi kenan Afrah, "Afrah tai murmushi har se da dimple dinta Ya fito Tace Nasan me zanyi momma just give me 500 naira, "mummy batai musuba Ta dakko ta bata, "Afrah tsallakawa titi tayi taje wani shago ta Siyo Hollandia, bata ddeba segata ta dawo, Mikawa Xeey tayi, aiko xeey na gani Tana shirin amsa Afrah ta Shige Cikin Mota tana ta ma Xeey Gashi, Ganin ta shigane Yasa Xeey ta bita har akai Sa'a Afrah nata yaudarar ta har ta shige Mota, Rufe Duka kofofin Driver yayi Sannan ya Seta Hanya, Ita Kam xeey ko a jikinta dan Ba hankali gareta bata san ma ina Za'a ba Dan ganin Afrah datai ne har akai sa'an yaudararta Yasa Ta bisu.

_Sunyi tafi bame nisa ba Suka Isa Gidan Su. Parking Space Driver ya Samu yayi sannan Afrah Ta rik'o ma Xeey hannu Suka Shiga, "momma kam se kallon ikon Allah take yanda Xeey ta Saba Da AFRAH...

"Suna Shiga xeey taga wata sabuwar duniya da ta ma manta dashi kallon ta tsaya yi kamar me hankali, chan kuma Ta fara yar dube dube cikin yar jakar bako Dinta, "Momma Na kan Kujera se kallon yarinyar Takeyi, ji take yarinyar ta shigan Mata Zuciya Tana Sonta..

"AFRAH kuma daga kitchen Ta fito dauke da wani plate shinkafa da taliya da miya se manyan Namomi Kake gani a Sama _Nasan wasu har sun hadiye miyau Lolx_ karasowa tayi ta ajiye plate din agaban Xeey, Xeey ko na gani tun kan ace mata taci ta fara Ci hannu bak'a hannu kwarya, Afrah kam na gabanta kamar yanda ta Saba in tanacin abinci har se ta gama sannan zata tashi,
Chapter 13 · 0% Book details