← Book details A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

A Dalilin Matar Uba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aminiyartace tace haba Kawata ki kwantar da hankalinki abun da nakeso dake Shine, ta matso kusa da kunnan Kawarta ta shafa mata wani tsegumin da ni kaina banji me sukaceba, Tana cire bakinta wajen kunnanta naji Sun wani tafa suka hada baki sukace Mun kusan shiga Gari......!

Bayan sun gama yan Surutansu na kawaye ne Hajiya sa'adatu Ta kwaso kayan da tai tsaraba nan ta nuna mata, Hajiya yalwa tace kai amma kinyi daidai, tunda baki da da ko jika dole a gwangwaje yan uwanki da kaya, nan dai suketa firfito da kayan har suka gama Itama yalwan Ta sama rabonta sukai sallama sannan Ta tafi gida.....

"life goes on haka abubuwa suketa gudana; akwai wata rana da ya kasance Ranar Bakin Cikin Xeexee Suna Zaune a Class time Din Suna SS 1, Ismail ne ya kalla Xee yaga se Design takeyi a wani paper,
Ismail yace ki tashi i have something to Tell you,
Zee ce ta ajiye abun da takeyi ta fuskanceshi tace Ok bro i'm all ears,

Yace Soon to miss you my lil Sister,

"Tace Amm banganeba ina Zaka ba,

Yace Kinsan time yayi da zan zana waec dina so by next week zan bar zuwa school dinnan sedai mu dinga haduwa a gida....

Nan take xee ta fara kuka, wai ita dan me ze fada mata haka, Kuka takeyi ba sauki, Dakyar ya lallasheta tai shuru ana yin closing kam tun da tazo gida ta kwanta bata kara fitowaba, Kowa se tambayanta yakeyi what's Wrong setai banza da mutane, mummy kam bata damuba dan tasan ita da ismail ne duk yanda akayi, ranar Wuni tai a room dinta har Dad ya dawo ya sameta a kwance sannan ya tambayeta meke faruwa ta fadamai,

"Dad ne yai smiling yace Oh my baby lalle kun shaku da wannan yayan naki, in banda abunki ai ba Age mate dinki bane balle a ace zaku zauna Class daya,

"tace Dad wlhi i so much like ismail, guy din beda prblm and he knows what he's Doing, daddy dai ya bata hakuri akan Dole fa ta hakura tunda zaman mace da namiji ba zai taba Yuwuwa ba ko yan biyune dole sai daya yabar daya wata rana, Seda taji kalaman dad sannan Tai hakuri tace It's Ok,

ranar dai ba wani bacci tai ba se tinane tinane takeyi Na Ismail.....

*ONE WEEK LATER* Rana bata karya
Yaune Ismail ya dena Zuwa School.

Xeexee kam hankalinta a tashe yake koda taje school taga She's Alone ba abokin hiranta kwantawa tayi akan Desk Se tinanin her frnd takeyi,

Wata Safiyyace yar Class dinsu Tace Haba Sist, karki damu zan zama me share miki hawaye, Muma nan da kike ganin mu one day zamu rabu, no condition is Permanent....

"Xeey ce ta dago kai ta kyalletace Ta sake wani murmushi tace yes hakane sist, Ngd Yanzu na sama frnd kenan dama ni banson tarkacen kawayene sai yasa ban ciki bin Kowaba...
"Safiyya Tace yeah like me kenan naga rayuwarmu zatazo dayane sai Yasa Nazo mu kulla frndship...

"Xeexee tace well it's Ok Allah yasa mu dace Safiyya tace Ameen, "xeexeece ta ce to baki fadamun Ke wacece ba,

_Safiyya ta gyara zama Tace Uhm kamar yanda kika Sani sunana Safiyya, Muna Zaune a Ung Sarki, Mu ukune wajen Babanmu, nice yar auta, kuma inason kasancewa da mutun me gaskiya me rikon Amana bansan gulma...._

"Xeexee ce tai wani irin Ihun dadi Tace Wow, Lalle rayuwarmu zatazo Daya, Nidai sunanan xee, matan dad dina biyu, mamanmuce ta biyu kuma nida brother na Abba kawai ta haifa...

"Safiyya Tace Wow Nice family Allah yasa mu rike junanmu da Amana, Xee tace Ameeen

*Bangaren Ismail kuwa.* ...

_Lolz Ku tara a next page Love you All_

*Ummiey Xeey CE*
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍

This page is dedicated to my dear sweet Heart *Herlieymer Ameen* ```I love you so much, Allah ya kara daukaki da kungiyarku na``` *TWF* 💦💦

*📄 PAGE 13____14*

Bangaren Ismail Kuwa. Ranar Da ya dena zuwa School kamar mara lafiya dan missing Din Xeexee yakeyi, yana kwance a daki pillow ya dakko ya rungume, Naji yana wani surutai nasan be wuce Missing Din Xeexee, chan naga Ya sake pillow din Ya zauna a bakin gado, Kana Ganinshi Kasan Tinani yakeyi, Wani dan Memo naga ya dakko yayi rubutu,

"tashi yayi ya nufa side Din Dad dinshi ya Ajiye wani write Up din da yayi, Dawowa daki yayi amma Jikinshi Be bashiba dan gabanshi wani Fadi yakeyi Kome ya

"rubuta Ohon mai.... Around 10Am ne Dad din Ismail ya Tashi after yayi wanka ya shirya zai fito daga Room dinshi kenan Yaga wani dan memo a Side Bed dinshi ya dauka ya fara karantawa kamar Haka....
_Dear Dad Please ina rokon Wata Alfarmane Nasan Zaka iyamun, Nasan nayi karami amma Dan Allah Dad Kai Mun Aure yanzu, A auramun Xeey Inasonta inyaso sai inci gaba da karatuna_

Dad Ne Ya kara kura ido Yace WHAT? Ismail ne da wannan rubutun! Pallow ya Nufa ya zauna Akan Kujera sega Mahaifiyar Ismail tazo itama ta zauna, Dad din ismail ne ya mika mata write up din da yayi itama ta karanta gabantane yai wani mugun Fadi tace Aure, He's Just 21years Fa Subhanallah,

"Baban ismail ne yai wani murmushi yace ki barni Dashi Jeki kiramun Shi, "Hajiyace ta tashi ta nufa room dinshi knocking biyu ya bude tana kallonshi Maida kanta gefe tayi Tace Alhaji na kiranka,

"Gabanshine yadan Fadi but wata zuciyan nacewa Yo ai ba karya kayiba kaje kawai kaji, Tafiya kadan segashi a Pallow, Waje ya sama ya Zauna a Kasa ya gaishe da Dad dinshi

"Alhajine Yace Naga Sakonka Amma abun da nakeso dakai Shine ka Daga Kai ka kalleni ka fadamun Da bakinka aure kakeso,

Ismail ya kasa daga kai ya kalla dad dinshi balle ya furta WATA magana ,

"Alhaji yace badakai nake maganaba Nace Ka daga Kai ka kalleni Nan ma shuru seda Yace ya kalleshi sau Uku amma Duk ismail ya Kasa...

Dad ne yai murmushi Yace To baka Isa aureba tunda ka kasa daga kai ka kalleni, Haba Ismail saurin me kkeyi kaifa dayane a gidan nan, Karatu nakeso kayi sosai wanda kasa zasui alfahari dakai Amma Kanaso Ka kawo maganar Aure? Nan Ismail yaji duk wani kunya ta isheshi shima Me yasa yai rubutun Oho..

"Yace I'm Sorry Dad, "DAD yace Sorry for urself inma zaka cire wani maganar aure ma To ka Cire dan By Monday computer school zaka Fara zuwa a *DIALOQUE* idan ka kammala By next year Kuma Kasan waje zakaje Kai karatun doctor ko wani abun. Aure time ne zakayishi ko bakaso.

"Ismail To Kawai yace dan dad ya rusa mai plan but ba yanda zaiyi hakanan ya hakura, "hajiya kam tunda suka fara magana Ko A batace ba dan abun yaron nata ya girmama... Alhajine yace ya tashi ya Tafi dan haka ya mike sumi sumi jiki ba kwari ya nufa daki,

"yana Zuwa fadawa gado yayi Ya fara Imagining yanda rayuwarsa zata kasance ba tare da Xeey Ba...Pillow ya dakko ya fara chusa kansa a ciki yana i love you my xee, my hrt beat... Wata Xuciyan kuma Tana Cewa ka manta da zancen Dad kenan na ba yanzo ze maka aureba

Wani bakin ciki yaji A tare dashi Kawai Yace Nama Hakura da xee nasan baza a bani itaba da wannan tinanin bacci yai gaba dashi...

"Alhaji kam Bayan tashin ismail Hajiya ya kalla yace kinga yaronki ko, yanaso Ki tsufa da wuri wai aure ni dariyama ya bani wallahi.

"Hajiya tace hmm Nasan be wuce zeey zaice yana So dan ita kadai ne Suke Tare, Ni na rasa gane kanshima aure at this early age of him, Alhaji yace kema kya Gani, Allah dai ya tsare mana Zuri'an Mu gaba daya tace Ameen, nan ta kawo mai breakfast, yaci yasha sannan ya tafi office itama ta tashi tai gyare gyaren Ta...
°°°°°°°°°°

Around 2Pm ne Xee sundawo daga school kenan ana droping dinsu a bakin Gate ko gida bata shigaba Gidan su ismail ta shiga, Ta sameshi yana wanke Singlet dinshi da wasu kayanshi, Beji tafiyantaba dan yayi nisa a tinani kawai hannu yagani a cikin bukitin da yake wanki, Yaji tsoro dago kai yayi dan ganin waye, Kawai sukai ido hudu da xee wani murmushi ta sakar mai shima ya maida mata,
tace weldone bari na tayaka,
yace no Karki bata kayanki da ruwa,
"ki barshi yanzuma zan Gaba bazanyi taking time ba kije ki zauna kafin Na Gamaa

Tace tab Bari dai naje gida na cire uniform na dawo yau akwai labari yace Ok sist, Tana tafiya ya bi bayanta da kallo Yace Damn...this girl is Pretty, Seda yaga ta fita a gidan sannan ya duka yaci gaba da Wankinshi shap shap ya gama yai wanka ya shirya,

"xee kuwa tana shiga gida tai wa mum dinta Sannu da gida ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta dakko kayan da ta sama sawa Gida da wando tasa, Ta dakko abincinta taci tacewa mummy Bari taje gidan Su Frnd ismail, Da mummy kamar zatace kartaje amma seta barta tace to sai kin dawo karki dade tace Ok Mum.....

Tai ficewarta Zata shiga gidan Su ismail kenan segashinan sun hadu a bakin Kofa, tace laaa da fita zakai ko inzo bansamekaba, Yace aa dama wajenki zani najiki shurune tace tom Ganinan....Yace yanzu ina zamu gidanku ko gidan mu, Tace Noo mu Zauna a waje kawai mui hira nan suka sama Waje Suka zauna a kasan wata bishiya suna shan Iska.......

Ummiey Xeey Ce
[11/7, 6:55 AM] Ummiey Xeey Abakson💋: *_ ∆°°••~❣_💞••💙💓❤💛
*A DALILIN MATAR*
*UBA*
*_ ∆°°••~~❣_💞••💙💓❤💛

```STORY & WRITTEN BY```
*Ummiey_Xeey Abakson*💋

*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM​*
[ɦօʍɛ օʄ քɛaċɛ, ɦօռօʊʀ aռɖ sʊքɛʀ աʀɨtɛʀ's]

*OCTOBER 2017*
_SHORT STORY_

```SADAUKARWA GA____```
*MARIAM TIJJANI ADAM*😍
Chapter 4 · 0% Book details