← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 49

Sashe 8

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

a daidai wannan lokacin ita Kuma Aisha na can tun magariba ta shige daki ta kulle kanta tace bata jin dadi tai kwanciyarta don ma kada bakonta na jiya ya dawo yau ace sai ta fita ,kmr yadda yace zai dawo tanajin usman a kofar dakinta zaune kan Yar tsugunne inna yana cin tuwo yana sanya hirarsa da ita Amman bata kula shi ba ,yace zan danyi kokari in dinga kwaikwayon su inna wajen azumi Lada,yaya Umar dake wanke kayansa a bakin fanfo yace matsa can ka bawa mutane guri kai din da kullun safiya zaka tashi kmr ka kwana baka Ci ba shine zaka wani iya azumi na dole ma yaakayi aka cika ,.

Usman yayi dariya yace "ai tashi ne yaya sai inji kmr an kai min farmaki cikin dare , Amman ina son yin tun yaushe nike fada ,su yaya Aisha bana jin an taba kwatanta fadar zaayi .

Yusif yashigo ya Mika masa kudin maganin soro na duka gidan ya karfa ya wanke hannushi
ya fita .

Washegari da yamma ne Aisha na tsakar gida tana tankade garin tuwo usman ya aro dutsen guga kennan zai fara aka dauke wuta da Kyar ya hada na gawayi ya gama hurawa zai fara suka dawo da wutar NEPA , usman yace wlh baza ayi da wutar NEPA ba dana gawayi zanyi tunda ba dole bane yi dana NEPA.

AISHA ko mai zatayi in ba dariya ba Abba dan makarantar su usman ya shigo usman wai kaje ana kiranka usman yace injiwa Abba yace wasu ne a waje su biyu Maza usman yatashi yafita jimawa kadan ya dawo wannan Karon a natse yake magana Amman acikin Yar murya yace yaya Aisha baki kikayi a waje ina ga balaraben nan ne da yazo shekaranjiya da daddare .
Aisha kallonsa kawai take duk da bata nuna komai ba a fuskarta ba Amman sai ta tsinci kanta da faduwar gaba cigaba tayi da abunda take zuciyarta na dukawa da sauri da sauri usman yashiga gyada kai dan Allah yaya Aisha kije wallahi suna da kwarjini da kima bazan iya komawa ince ba zaki zo ba .

Bata kulasa ba haka bata bar abunda takeyi ba , saboda a ranta bata da niyar zuwa Amman tarasa meyasa zuciyarta ke harbawa , usman yace innarmu zan gayawa zata saki kifita yanzu ,ta ja tsaki har ya nufa dakin inna kome ya tuna sai Kuma ya fasa ya juya ya sake kallonta ya girgiza kai ya fita .yayin da tabishi da kallo ,har ya dawo ya cigaba da gugarsa bai sake ce mata uffan ba .

Gabannin magariba wasu guraran ma an soma kiran sallah yaya Ali ya idar da alwala ya fita , Aisha na kicin dinsu tana sauri ta kwashe abinci itama tayi alwala sai ga yaya Ali ya dawo Niki Niki da kaya ya zube yasake fita yashigo da wasu kwali guda uku ya kalli Aisha yace gashi nan wai Kuma ana miki sannu da shan ruwa ,ya fice abun sa cikin mamaki ta bishi da kallo to yaya Ali ne bbu fuskar, da ta dakatar dashi ta tambaye shi bata taba komai ba har sanda inna ta sanya aka kwashe kayan daga gurin mamaki bai gama sakin ta ba har zuwa byn sallah ishai ta fito wanka kennan mlm abu yashigo daga waje yace taje tayi bako .

Cikin tsoron ya mamaye ranta kmr ta daura hannu akanta ta kurma ihu haka takeji haka ta shirya cikin sanyi jikin ta fita.

Sanye yake cikin kananan kaya masu duhu colour din da suka sake fidda kyaunsa a fili ga jar fatar sai sheki take , tun fitowarta ya zuba mata idanunshi daman Kuma kofar gidan yake kallo har ta karaso garesa ta tsaya bai dauke idanunshi daga kanta ba yanajin yadda zuciyarsa ke tsalle kmr zata fasa kirjinsa ta fita lumshe sexin eyes din shi yayi sannan ya bude su fas akanta ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da yatsun hannuta shima dai shr yayi yana sake kallonta San ransa,shiru yabskunci wajen na wani lokacin can dai cikin tsoro tace ina.....wu...ni yayi murmushin karfin hali ya bude baki ya amsa mata ,sannan yace Aisha kinyi kokari yin azumi yau ga rana banda kince indawo yanzu da zan barki kin huta ya sake kallonta tamkar wanda yake son ya dauke mata gajir azumin da tayi sannan yace wani abu ne a zuciyarta yakasa hakuri dole sai yazo yaga yadda kika Sha ruwa usman yace akwance kike da fatan ba wani abu ke damunki ba ,sannan yayi shiru ,kiris yarage Aisha tasa kuka shikenan dama tasan akwai shirin da usman yazo ya kulla mata tun dazu jikinta ke bata ,bata iya cewa komai ba illa har yanzu kanta nakasa taki yarda su hada ido dashi Abdullah ya zuba mata idanunshi ,da gani zatayi tsadar magana ,ya furta haka cikin ransa yakira sunanta cikin sanyi Aisha I you ok , ahankali ta daga masa kai ya koma lip's din shi na kasa yasoma cizawa ahankali........

MMN SUDAIS CE
[3/12, 3:01 PM] Kaunace Sila: 💗💗💗💗💗
ZUCIYAR MASOYI
💖💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO

Page 6

Tsaye take turus sai hawayen dake bin fuskarta bata san har yanzu yanan ba kawai sai taji badadi ko kadan ba nufinta tayi haka agaban shi ba ,bugu da Kari Abdullah ya girmewa babnan yayanta yusif dan sai taji tamkar tayi raini ga babba.
Chapter 8 · 0% Book details