← Book details Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 49

Sashe 17

Zuciyar Masoyi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

suna zaune
akarinka shigowa da kayayyakin tun daga bahun Hunan shinkafa taliya makaroni sabulai abun dai tamkar za'a bude shago"tsarabar su Abdullah kennan mlm dahiru yarasa inda zai saka bakinsa dan gaskiya ya yaba da Abdullah yaji ya kwanta masa a rai cikin lokacin daya "kyautar kudi kuwa Abdullah tamkar wanda yake da injin bugo su agida "mlm dahiru har kasa magana yayi sun sha fura sunci zabbi da aka soya musu anan sukayi la'asar sannan sukayi shirin tafiya Aisha dai tana daki tamkar ta fasa ihu da Kyar tayi sallah ko abinci kinci tayi ta sanya dan guntun hijab hular kanta ya sauko mata iya kafadarta ,farin takalmi tasa sai farin handbag data makale a hannunta ,a haka mlm dahiru yakarayi mata nasiha ta fito dan hasken ranar da ya nufi gabas zai fadi tana fitowa shi ya hasketa tasa hannu ta Kare fuskarta ,Dr sagir ya kallota ya girgiza kai yayin da yadan zunguri Abdullah ga madam nan fa. Abdullah ya kalleta tsab yayi murmushin a hankali yace ai aganinta duk mun matsa mata ne fa,suka sa. dariya ,lafiyayyun motoci tamkar na wasu shugaban kasa aka bude mata daya ta shiga ta gane direban da ya kawosu ne,ashe Abdullah ne ya turo shi,mlm dahiru na tsaye har sai daya ga tafiyar su tare da tsaraba man shanu nono fura kwan zabbi musamman dayake lokacin sane.salis da yaya Ali sune a motar gaba sai musa dake tuka su a dayar mota kuma shida Aisha a baya yayin da Dr sagir a gaban gurin me zaman banza Dr sagir ke ta kokarin janta da hira wani ta amsa wani tai shiru shi kuma Abdullah inda ka ganshi tamkar wanda akayiwa gafara jin sa yake kmr ya aure ta ne sun fito yawon ziyara yasa hannushi ya dauko jakarta dake kan cinyarta tana kallonshi batai magana ba har ya bude bbu komai a ciki sai kayan make up dinta yayi murmushin ya Ciro wani passport dinta na makaranta da uniform a jikinta har da dan kwalin perfect akanta ya zubawa hoton idanunshi sannan ya dago ya kalleta itama anyi sa'a ta dago da niyyar ta saci kallonsa ai kuwa suka hada Ido ,Ido cikin Ido suke kallon juna ya kashe mata idanunshi daya yayi murmushin ya zura hoton a aljihunsa , Aisha ta dauke kanta tacigaba da kallon hanya shida saura suka shigo birnni kebbi taso ace sai dare suka shigo , Amman ko sanda suka sauka daga mota Ido CA akansu musamman ita da Abdullah daman Kuma abunda bata so kennan gashi biye yake da ita jakar ta ma tana hannushi nan da nan tarinkajin tamkar ta nutse dan kunya yanayin ta ya sauya jikinta har rawa yake hatta Dr sagir sai da ya lura da yanayin da tashiga har kofar gida suka rakata suka Yi sallama da Dr sagir , Abdullah ya Mika mata jakarta ta juya zata karba ya lura hatta idanunta sun cika da kwalla ya rike jakar yana kallonta ya kira sunanta cikin sanyi murya Aisha..... are you alright .....?ta daga masa kai are you sure tasake daga masa kai sannan a hankali ya Miko mata jakarta tare da fadin I will come back letter ,ta amsa ta juya ta shige gida ya tsaya yana binta da kallo bbu halin yabita ya rarrasheta ya karaso inda Dr sagir yake yana ganinsa ya fashe masa da dariya yace kai friend be a man duk kabi ka susuce akan karamar yarinya "tension ne kawai ta samu na rashin sabo na gane irinsu duk kabi kawani rude Abdullah yayi murmushin karfin hali dan shi kadai yasan halin da ya tsinci kansa lokacin da suke tare Dr sagir ya bugi kafadarsa yace my friend a dage da addu'a .dan yarinyar taci ayi komai a kanta Abdullah ya mika masa hannu suka tafa yace thank you doctor ...

kamar yadda ya fada washegari karfe hudu da rabi suna Tare daga cikin soron gidansu ,simintin ciki a share yake tas Abdullah na zaune kan kujera har sanda tafito bai ji isowarta ba ,sai da ta taba kujera zata zauna sannan ya dago ya dubeta kallo daya tamasa tagane yau cikin serious dinsa yake sosai duba da yanayin fuskarsa ,byn ta gaisheshi ya zuba mata idanunshi yana kokarin sanya kwayar Idanunshi cikin nata kallo daya tamasa ta dauke kanta ya kira sunanta yace Aisha tun jiya byn rabuwarmu zuwa yau sau nawa kika tuna ni ?taji tambayar wani iri ta juyo ta kalleshi murmushi ya sakar mata yace ko sau daya ko na amsa miki ,ita ma dan murmushi tayi" yayi shiru na wani cikin lokacin tamkar mai nazarin ta inda zai fara yayi dan gyaran murya ya sake Kiran sunanta yace magana nike son muyi please ina son ki bani hadin kai, tai shiru batace komai ba ya zubawa yatsun kafafunta dana hannunta Ido yakanyi mamakin yadda suke kmr nashi yayi jin yana sake nazarinta sannan yace please Aisha ina son ki amince min inzo neman aurenki a gurin baba ina bukatar ki kinzama matata ta aure Kuma uwar ya'yana , maganar tashige ta ta dago Ido tana kallonsa shi dinma ita ya zubawa Ido sun jima a haka yayin da take kallon Abdullah wato yana son yazama wani sirri na rayuwarta kennan ,ita da kanta bata taba zama ta tuna wata rayuwar aure da sirrin dake ciki ta ba,sai ayanzu da Abdullah ya haskota da hakan shiyasa take masa kallon wanda zai iya sanni sirrinta kamar wacce ta farka daga mafarki da sauri ta dauke idanunta daga gareshi ,yayin da shi kuma kallon da ta dinga masa ya sake rudashi yanemi yafi haiyacinsa idanunta tamkar wanda ta fara bacci ta farka take masa kallon tsoro da maganar da yayi mata har sanda ta dauke Ido Amman shi ita yake kallo har yanzu yanajin yadda kaunarta ke sake tsumashi "shr bbu wanda yasake cewa komai ,ya kamo lip's dinshi na saka yana cizawa ahankali ya hade rai gudun Karta kawo masa wasa cikin lamarin ,yace nasan komai yana bukatar nazari ko na barki zuwa gobe sai in dawo naji abinda kika yanke .

kawai taji kalmar gobe ya fitowa daga bakinta yace Eh mana gobe Sunday shine Nike da time sosai da har zan fahimci maganar da zamuyi in ba haka ba sai zuwa rana irin ta yau Amman me kika gani ta sake kallonsa batare da tace komai ba yace banason nayi miki gaggawa idan kince indawo zuwa next week ne sai na bari ,ta daga masa kai cikin sanyi jiki yace to shikenan yana sake karewa mata kallo .

Anyi hakan asabar lahadi litinin aka kai aunty Maryam asibiti tun safe suke can gabanin magrib ta haifi diyarta mace washegarin talata aka sallemesu Inna bata dawo gida ba sai ranar laraba ita Kuma Aisha aranar larabar tashirya kayanta ta tafi gidan da yamma Abdullah yataso aiki tanan gida ya biyo yaga sanyin idanunshi Amman bai sameta ba sai usman ne yayi masa bayanin inda take a ranar duk yadda yaso ganinta hakan bai samu ba dan dama idan yashiga gida mami bata wani amincewa da fitar dare idan dai ba Dr sagir ne yazo suka fita ba,.

Amman washegari da wuri yabar office ya sameta can gidan aunty Maryam yadda Abdullah keji tamkar ya dauke ya gudu da ita yace Aisha ko nema na ba'ayi Kuma kinsa hanyoyin da zaki bi ki ganni ko kiji murya ta tadan saci kallonsa ta sunkuyar da kai tana tuna ranar da ta dawo daga ka'oje cikin jakarta ta tsinci complement card din shi guda uku aciki , address dinsa numbers dinsa da matsayinsa na aiki a jiki a tsakiyar wani littafinta ta zuba su bata kuma bi takansu ba yayi murmushinsa mai sake fidda tsantsar kyaun da Allah ya masa"meyasa magana take baki wahala ne ,ina aunty Maryam tana ciki baki daukomin bbyn taki nagani ba ta dauka da wasa yake sai da sake tabbatar mata Sannan ta Mike ta shige, zuwa jimawa ta dawo dauke da bby a hannunta ta Mika masa ya karba yana kallonta yace ina son bby mace Aisha tana birgeni da dadin wasa tajima a hannushi daga baya tasoma motse Aisha ta karbeta ta mayar da ita ta dawo da juice da snack da aunty tayi masa tun zuwansa ya zame daga kan kujera yace kai nagode wa aunty kamar tasan inajin yunwa. Aisha tamasa wani irin kallo kmr mai jin tausayisa ,yana kallonta ta sunkuyar da kai ya gane kallon da ta masa kawai yayi murmushin gefen baki anan sukayi sallah magariba har salis yace tama aunty Maryam barka zaizo gobe in Allah yaso ta amsa ta shige yabita da kallo, a kasan ransa ya furta har yanzu bata fara damuwa dani ba .
Chapter 17 · 0% Book details